Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ya sa gwamnatin Najeriya ke son ta fara ɗaure masu biyan kudin fansa
- Marubuci, Daga Nduka Orjinmo
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Bayan biyan kudaden fansa sau uku domin ceton 'yan uwansa, wani dan kasuwa a Najeriya Lawal Ado ya ce dokar daure masu biyan kudin fansa ba abu ba ne mai kyau.
Wani kuduri mai cike da rudani kan kama masu biyan kudin fansa a Najeriya shi ne mataki na baya-bayan nan da kasar ta dauka domin daƙile ayyukan masu fansa da mutane.
Kudurin na son a rika daure mutanen da suka biya kudin fansa shekara 15.
Malam Ado ya ce 'yarsa na tafiya tare da rakiyar 'yan sanda kan titin Buruku a cikin jihar Kaduna, lokacin da wani gungun masu garkuwa da mutane suka sace su a watan Disambar 2021.
An tsare su har na tsawon sati 15 kuma an sake ta ne bayan ya biya fansar naira miliyan 10 daidai da fan 19,000.
Bayan shekaru kadan, an kara sace matarsa a gidansu da ke Kaduna, an kuma sake ta ne bayan ya biya fansar naira 700,000.
An kama mahaifiyarsa lokacin da take kan hanyarta ta zuwa kauyensu a jihar Kaduna - ya biya naira 300,000 sannan aka sake ta.
Malam Ado ya ce lokacin da wadannan 'yan bindigar suka kama ta na kusa da kai da kake kauna, ba ka da wani zabi da ya wuce ka biya kudaden da suke bukata.
Ya ce 'yan majalisa na goyon bayan dokar ne saboda "ba a taba kama wani makusancinsu ba".
'Yan majalisar na cewa biyan kudin fansan na kara wa masu garkuwa da mutanen karfi. Abin da yake karawa sanya masu wannan aiki kama mutane kan me uwa da wabi kuma suke neman kudi domin sakinsu daga naira miliyan daya har zuwa 100.
Tun 2011, masu garkuwar sun karbi kudi da ya kai akalla dala miliyan 18, yayin da suka karbi rabin abin da suka suka amsa a baya a tsakanin 2016 da 2020, in ji kamfanin hada bayanan sirri na SBM da ke Legas.
Wani masani a hukumar binciken bayanan sirri ta tarayya Eguaoje Funmilayo, ya ce iyalai da yawa ba su son shigar da 'yan sanda cikin harkokinsu, sun fi son biyan kudin fansa, abin da 'yan sanda kullum suke hana wa.
Cikin wata nasara da ba a fiye samu ba, a farkon wannan watan 'yan sanda sun ce sun kama wasu mutane da ake zargi da kitsa sace daliban wata makaranta da iyayensu suka biya naira miliyan 200 kan asake su.
Senata Ezenwa Onyewuchi - shi ne ya gabatar da wannan ƙuduri da ya samu karbuwa a majalisar dattijai yanzu - yace garkuwa da mutane na kara zama "abin da yake kawo kudi cikin gaggawa a Najeriya".
Babu wani waje da aikin masu garkuwa da mutane bai je ba, amma sun fi ƙarfi a yankin arewacin Najeriya. Filayen jirgin sama da na kasa barikin sojoji da wuraren addini duka na cikin wuraren da ake hara cikin shekaru masu yawa.
Iyalan wadanda ake sace 'yan uwansa yawanci na sayar da kadarorinsu ko kuma su karbi bashin banki ko dangi su tattara kudi domin kubutar da 'yan uwansu.
Wadanda suka gaza biyan kudin kashe su ake yi, an kuma ta samun rahoton wadanda aka kashe ta hanyaar cire sassan jikinsu kuma su sayar.
Usaman Mbaekwe, wanda ya kwashe kwana biyar a daji a kudancin Najeriya lokacin da aka kama su a mota, ya ce jami'an tsaro ba su yi wani yunkurin kubutar da su ba. An sake shi ne bayan matarsa ta samo naira miliyan daya ta biya kudin fansa.
A duniya, manyan kasashe kamar su Amurka da Burtaniya sun hana biyan kudin fansa, suna cewa ita kadai ce hanyar da za a iya dakile wannan ta'ada.
Amma a kasashe irinsu Faransa da Jamus da Sifaniya da Italiya an sha samun rahoton cewa sun biya miliyoyin daloli domin a saki mutanensu da aka kama a Afrika da wasu sassan duniya.
Ko gwamnatin Najeriya ta taɓa biyan manyan kudade ga masu garkuwa da mutane a baya - ciki har da mayakan Boko Haram da suka saki 'yan makarantar mata ta Chibok wadanda aka sace a 2014, da gwamnatin Katsina ta biya kudi aka sami yan makarantar da aka sace a 2020.
A baya-bayan nan kuwa, mummunan harin da aka kai wa fasinjojin jirgin kasar da yake tafiya Kaduna daga Abuja a watan Maris.
Akalla mutum takwas aka kashe, a yanzu kuma ana maganar cewa akwai mutum 60 ne a hannu.
Masu garkuwar ba su nemi kudi ba amma sun gindaya wa gwamnati wasu sharuɗɗa.
"Biyan kudaden fansa ba matsala ba ne a nan, amma sace mutanen ne matsala," in ji Imran Rufa'i wanda aka kama dan uwansa a jirgin kasa.
Ita ma Zara Aliyu wadda aka dauke dan uwanta ta amince da hakan.
Ta ce "Za a iya amfani da irin wadannan dokoki ne kawai idan akwai cikakken tsaro," in ji Zara.
Har yanzu ba a dai sani ba ko Shugaba Buhari na goyon bayan wannan kuduri, amma dai ya nuna rashin goyon bayansa ga biyan kudin fansa a bara.