Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ran 'yan Najeriya da dama ya ɓaci kan dokar hana biyan kuɗin fansa
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 3
Baya ga raha da kakaci da tattaunawar ilimi tsakanin 'yan Najeriya a shafukan zumunta, akwai kuma ɓacin rai kan ƙudirin dokar da ta haramta biyan kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane a ƙasar da Majalisar Dattawa ta amince da ita.
Wannan ba abin mamaki ba ne saboda maganar biyan kuɗin fansa ga 'yan fashin da ke kamawa da kashe mutane ɗaiɗaikun 'yan Najeriyar ta shafa kai-tsaye, kuma duk da ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi akasarin waɗanda ake sacewa sai an biya kuɗin ake sako su.
Hukumomi sun yi amanna cewa biyan kuɗin fansar na rura wutar sace mutane a Najeriya, kamar yadda su ma 'yan Majalisar Dattawan suka yi imani da hakan.
Sai dai kuma ƙudirin dokar, wanda gyaran fuska ne ga dokar yaƙi da ta'addanci, ya tanadi hukuncin kisa ko ɗaurin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane.
Ƙudirin, ya ƙunshi ɗaurin rai-da-rai ga masu satar mutanen da kotu ta kama da laifi, kuma matukar satar ta kai ga mutuwar mutum, masu laifin za su fuskanci hukuncin kisa.
'Da akwai tsaro babu wanda zai tara kuɗin fansa'
Kusan kullum, 'yan Najeriya musamman mazauna yankin arewa maso yamma, na cikin fargabar sacewa ko kisa daga 'yan fashin daji da ke kai hare-hare a kullum.
Wani rahoto kan sha'anin tsaro da kamfanin Beacon Consulting ya fitar ya ce hare-haren 'yan bindiga sun kashe mutum 1,500 cikin watan Maris kaɗai a Najeriya.
Rahoton ya ce alkaluman da aka samu na da nasaba da yadda mahara suka fara amfani da bama-bamai wadanda ake sarrafawa a gida da ake kira IED.
Mutum fiye da 8,000 ne suka yi tsokaci kan labarin dokar da BBC Hausa ta wallafa a Facebook, wasu fiye da 200 kuma suka bayyana ra'ayoyinsu a Twitter. Akasarinsu na ɓacin rai ne da kuma tambayar abin da gwamnati ke yi don daƙile satar 'yan uwansu.
"Da a ce sun samar da tsaro a ƙasar babu wanda zai so ya tara kuɗi don ya biya fansa," a cewar ma'abociyar Twitter Surayya Ahmad.
Shi ma wani mai suna Auwal Gambo Ahmad a shafin BBC Hausa na Facebook ya nanata ra'ayin Zainab. yana mai cewa "da kun yi abin da ya dace ai da ba haka ba".
Ita ma Ramatu ra'ayinta kenan.
Wani ma'abocin shafin BBC Hausa a Twitter mai suna Yusuf Buhari, addu'a ya yi wa shugabannin Najeriya cewa "Allah ya ba su hankali".
A toshe layukan mutanen da 'yan fashin suka sace - Majalisar Wakilai
Mako biyu da suka gabata ma Majalisar Wakilan Najeriya ta buƙaci hukumomi su dinga toshe layukan waya na mutanen da 'yan bindiga suka sace saboda kada su nemi kuɗin fansa.
Majalisar ta ce ta hanyar toshe layukan waɗanda aka sacen, 'yan fashin daji za su rasa hanyar cinikin kuɗin-fansa da dangin mutumin da suka sace.
Ɗan Majalisar Wakilai Abdullahi Balarabe Salame na cikin wadanda suka gabatar da wannan bukata a zauren Majalisar, kuma ya faɗa wa BBC cewa ya kamata a samu hanyar dakatar da 'yan bindiga daga karɓar kuɗin fansa.
"Mutanen nan dai mun ga duk manufarsu ita ce kudi sannan don kudin da suke samu shi yasa suke kashe mutane, shi ya sa suke daukar mutane.
"Ya kamata mu samu wata hanya wadda za ta hanasu samun wannan kudi, idan sun dauki mutum ba za su sami kudi ba."
Ƙarin labaran da za ku so: