'Akwai kuskure a rahoton bincike kan rikicin Filato'

Plateau

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Masana harkokin tsaro a Najeriya sun fara bayyana ra'ayinsu kan rahoton kwamitin da gwamantin jihar Filato ta kafa don binciken hare-haren da suka addabi jihar a shekarun da suka gabata.

Tun a watan Mayun 2025 gwamnatin jihar Filato ta kafa kwamitin domin ya zakulo abubuwan da ke janyo rikici a jihar da tantance irin ɓarnar da aka tafka da kuma waɗanda lamarin ya shafa.

A cikin rahoton da ya gabatarwa Gwamna Caleb Muftwang bayan shafe watanni aƙalla huɗu yana aiki, kwamitin ya ce rikicin da aka yi fama da shi a jihar cikin shekaru 20 ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutane dubu 12 tare da raba ɗaruruwa da muhallansu.

Haka nan kuma Kwamitin ya ce ya gano wasu bayanai masu tada hankali da suka sanya hare-haren ke ci gaba da faruwa, inda a cikin shekara huɗu da ta gabata aka kai hari kan al'umma yankuna 420, da ke jihar:

Dr Kabiru Adamu, shi ne shugaban kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan harkokin tsaro a Najeirya, kuma ya shaidawa BBC cewa duk da kwamitin ya riga ya miƙa rahotonsa ga gwamnan jihar Filato, akwai kuskuren da ya tafka wanda ya saɓa tanadin fitar da bayanan tsaro.

Ya ce a bisa rahoton kwamitin ana son nuna cewa rikicin jihar Filato yana gaba da na sauran wurare, lamarin da ya saɓa alƙalumman da kamfaninsa ya tattara game da rikicin.

''Alƙalumman da mu muke da shi, sai ka je wajen na biyar ko na shida kafin ka ga jihar Plateau da Benue.

''Ban da masaniya a kan irin dabarun da suka yi amfani da su, duk da yake da na duba sai na ga babu ɗaya daga cikin su da ya ke da irin wannan ilimin na tattara bayanai da tantance su.'' in ji Dr Kabiru Adamu.

Masanin tsaron ya ce rahoton ya bashi mamaki ƙwarai da gaske saboda yawan mace-macen da aka nuna da kuma garuruwan da aka ce abin ya shafa.

Haka nan kuma masanin tsaro ya ce kuskure ne babba a samu rahoto irin wannan yana ɗauke da bayanan da ke nuna cewa wata ƙabila ce ke da hannu a rikici.

Ya ce ''Kalmar fulanin nan, jam'i ne ga jama'a. Duk wani masanin bincike irin wannan na ilimi ya san cewa ba ka amfani da kalmomin wanda za su iya tunzura jama'a da, misali su kalli wata ƙabila da cewa su suke abu kaza.''

Shi dai kwamitin da gwamnatin jihar Filaton ta naɗa domin zaƙulo bayanai game da rikicin jihar ya riga ya miƙa rahotonsa ga gwamnan jihar, Caleb Muftwang kuma a wata hira da BBC a ranar Alhamis, sakataren kwamitin, Timoty Baba Harlong ya ce sun zagaya ƙananan hukumomi 17 na jihar, inda suka gana da al'ummomi da jin bayanan su kafin kammala rahoton aikin nasu.

Sai dai Dr Kabiru Adamu ya ce ''na so a ce kwamitin ya ziyarci wani gari, ana ce mashi Tilden Fulani a jihar Bauchi... yawancin su ƴan gudun hijira ne da aka kora, aka ƙwace masu dukiya daga jihar Filato.''

Masanin tsaron ya ce duk da dai kwamitin ya bayar da shawarwari kuma ciki harda na amfani da dabaru na daban ba ƙarfin bindiga kaɗai ba, akwai buƙatar a tuntuɓi irin waɗannan al'umma da aka yi wa ɓarna domin samun sasanci da yafiya a tsakani.

Da ya ke tsokaci, gwamna Caleb Muftwang ya sha alwashin miƙa rahoton ga shugaban ƙasar Bola Tinubu domin ɗaukar mataki.