Yadda al'ummar Filato ke kai samame kan sansanonin ƴan fashin daji

'Yan bindiga

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 3

Da alama wasu 'yan Najeriya sun zaburo domin magance wa kansu matsalar ƴan bindiga da ta addabi yankunansu.

Al'ummar wasu garuruwa a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato sun yi haɗin gwiwa da sojoji inda suke kai wa ƴan bindiga hari har maɓoyarsu, a maimakon su jira ƴan bindigar su kawo masu hari sannan su kare kansu.

A irin wannan hari da suke kai wa ne suka samu nasarar halaka ƴan bindiga da dama a baya bayan nan, ko da yake wasu daga cikin ƴan sa kan suma sun samu raunuka.

Karamar hukumar Wase dai na daga cikin yankunan da ke fama da matsalar 'yan bindiga abin ya zaburar da wasu mutanen yankin wato 'yan sa kai suka hada kai da jami'na tsaro inda suka bi 'yan bindigar har maboyarsu da ke dajin dutsen Zaki wato yankin da 'yan bindigar suka kankance.

Daya daga cikin masu jagorantar wannan hadin gwiwa Abdullahi Usaini, ya shaida wa BBc cewa a samamen da suka kai wa 'yan bindigar a baya bayannan sun yi nasarar kashe 'yan bindiga akalla 100.

Ya ce," 'Yan bindigar suna barazana a Dogon ruwa sannan sun kori mutane a Dutsen Zaki da dai wurare da dama da ke yankin Wase to hakan ne ya sa muka dauki mataki inda al'ummar gari suka bayar da shawara cewaidan za a tafi a hada da jami'na tsaro a haka muka tafi tare kuma ko da muka yi artabu da su na yi kare jini biri jini, yanzu haka duk mun fatattakesu daga maboyarsu da ke karamar hukumar Wase."

" A yayin artabun daga bangarenmu mun rasa mutum hudu sai wasu 17 da suka samu rauni wanda yanzu suna asibiti ana yi musu magani, sannan daga bangaren 'yan bindigar kuwa ina kyautata zaton mun kashe ya kai mutum 100." In ji shi.

To sai dai kuma Abdullahi ya bayyana fargabar cewa 'yan bindigar da suka fatattaka za su iya dawowa yankin.

Ya ce," Kalubalenmu shi ne akwai maboyarsu a karamar hukumar Kana, sannan um al'ummar Wase ba zamu iya shiga yankin Kana um yi aiki ba wanda hakan zaiiya ba wa 'yan bindigar dama su sake dawowa yankinmu tun da muna makwabtaka."

" To amma yanzu muna jiran sarkin Wase da shugaban karamar hukumarmu su yi abin da ya dace don ganin ko za a samu hadin kai daga mazauna Kana don maganin wadannan bata gari." In ji shi.

Dama dai masana tsaro a Najeriya sun jima suna bayar da shawarar cewa ya kamata al'ummar yankunan da ke fama da matsalar tsaro su tashi tsaye domin taimakawa kansu musamman ta fuskar bayar da bayanan sirri na inda mutanen suke da samun hadin kai a tsakaninsu da jami'an tsaro.

Al'ummar karamar hukumar ta Wase dai sun ce dama 'yan bindigar sun jima suna cutar da su musamman wajen hana su yin noma da satar mutane domin karbar fansa har ma da satar dabbobi.