Tsutsar da ke cinye tsokar jikin mutane ta ɓulla a Amurka

Wasu tsutsosti kimanin 12 kenan da aka jibge a wurin bincike

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An tabbatar da ɓullar annobar tsutsar screwworm a nahiyar Amurka ta Tsakiya da Mexico
Lokacin karatu: Minti 3

Ma'aikatar Lafiya ta Amurka ta bayar da rahoton ɓullar cutar New World karon farko a jikin mutum a ƙasar.

Cutar da ke cin tsokar naman mutum, an same ta ne a jikin wani maras lafiya da ya koma Amurka daga El Salvador, ƙasar da cutar ta yi wa katutu a nahiyar Amurka ta Tsakiya.

An tabbatar da ɓullar cutar ne a ranar 4 ga watan Agusta, kuma babu hujjar cewa mutumin ya yaɗa wa wasu cutar, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Amma mece ce ita wannan cuta ta New World screwworm, kuma ta yaya take kama mutanen da dabbobi?

'Ƙwaro mai kiɗimarwa'

Wani ma'aikacin hukumar aikin gona ta ƙasar Honduras yana aikin cire tsutsar screwworm a wata gonar dabbobi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Tsutsar screwworm za ta iya shan jinin dabbobin gida da na daji, da tsuntsaye a wasu lokutan, ko kuma mutane 'yan ƙalilan

The New World screwworm (NWS) tsutsa ce da ke ɗimauta wanda ta kama, a cewar hukumar kula da dabbobi ta ''Animal and Plant Health Inspection Service'' (Aphis) - mai aiki a ƙarƙashin ma'aikatar aikin gona ta Amurka.

Balagaggiyar tsutsar ta kai girman ƙuda irin na gida (ko kuma ta ɗan fi shi). Suna da ido ruwan ɗorawa, da shuɗin idanu ko koren jiki, da kuma zane-zane mai duhu a gadon bayansu.

Tsutsar ta screwworm na cizon dabbobi na gida da daji, da tsuntsaye, da kuma mutane a wasu lokuta marasa yawa.

Aphis ta ce idan tsutsar ta gatsa tsokar dabba mai rai, takan haddasa matsala mai haɗarin gaske.

Tuni aka ayyana NWS a matsayin ƙaramar annoba a ƙasashen Cuba da Haiti da Dominican Republic, da wasu ƙasashe a nahiyar Amurka ta Kudu.

Ta yaya NWS ke kama dabbobi?

Sunan screwworm na nufin ɗabi'ar tsotsotsi na kurɗawa cikin rauni ko ciwo, inda suke kukkurɗawa kamar yadda ake ɗaura noti a jikin katako.

Macen tsutsar kan saka ƙwanta a cikin jini mai ɗumi da ke tsakiyar raunin a jikin dabbobi.

Da zarar ƙwayayen sun ƙyanƙyashe, sai ƙananan tsutsotsin su kafa bakinsu a cikin tsokar dabbar, waɗanda za su iya kashe mai tsokar idan ba a ɗauki mataki ba.

Screwworm za su iya haifar da babbar matsala a shanu da dabbobin daji, amma ba su fiya shafar mutane ba.

Wani maras lafiya da ya kamu a shekarar da ta gabata bayan gajeriyar ziyara a Dominican Republic ya bayyana wa hukumar CDC abin da ya ji.

"Bayan 'yan awanni, sai fuskata ta fara kumbura. Laɓɓana suka kumbura. Da kyar nake iya magana. Na dinga jin kamar an kunna wa fuskata wuta. Sai na fara zubar da jini ta hanci. Ko zuwa banɗaki ba na iya yi ba tare da hancina na zubar da jini ba," in ji shi.

Ta yaya ake kula da masu cizon NWS?

Mutane musamman masu fama da buɗaɗɗen rauni, sun fi shiga haɗarin kamuwa da cutar idan suka je ƙasashen da ake fama da ita.

Hanya ɗaya da ake iya kula da mai ɗauke da cizon tsutsar ita ce ta hanyar cire ɗaruruwan ƙwayayenta daga tsokar da suka kutsa, da kuma wanke raunin da suka shiga a nutse.

Ana iya warkewa sarai idan an cire tsotsotsin da wuri.

Annobar da aka yi a baya

Wani makiyayi yake kula da shanu a Ciudad Juarez da ke ƙasar Mexico

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu kiwon shanu na farabar yaɗuwar cutar

A cewar ma'aikatar noma ta Amurka, a shekarar 1933 ne tsutsar ta yi hijira daga kudu maso yamma zuwa kudu maso gabashin ƙasar ta hanyar shiga jikin wasu dabbobi.

Zuwa 1934, gidajen gona suka fara bayar da rahoton ɓullarta a jihohin Mississippi da Alabama da North Carolina da South Carolina da Georgia da kuma Florida.

An yi nasarar korar tsutar daga Amurka a shekarun 1960 lokacin da masu bincike suka fara fitar da jinsin maza na tsutar waɗanda aka fiɗiye kuma suka haɗu da mata domin saka ƙwayayen da ba za su rayu ba.

Wannan annobar ta yanzu ta fara ne a ƙasar Panama a 2023, kuma tsutsar ta ci gaba da yaɗuwa zuwa arewaci daga tsakiyar Amurka da Mexico tun daga lokacin.