Bayanan da ya kamata ku sani kan sabon tsarin fasfo a Najeriya

..

Asalin hoton, Nigerian Immigration Service

Lokacin karatu: Minti 2

Fasfo da mallakarsa a Najeriya ya zama wani abu da kullum yake fuskantar sauye-sauye da ke ɗaukar hankalin ƴan ƙasar.

Daga sauya fasalinsa zuwa yawan warƙoƙinsa da farashinsa da ma yadda za a karɓe shi da kuma abu na baya-bayan nan wanda shi ne wurin da mutum zai je ya yi rijistarsa da karɓarsa.

A ranar Alhamis ne ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Tunji-Ojo ya kai wata ziyarar gani da ido domin duba katafariyar cibiyar yin fasfo ɗin ta Najeriya.

Cibiyar samar da fasfo

..

Asalin hoton, Tunji-Ojo/X

A baya dai duk mai son yin fasfo zai iya zuwa ofishin hukumar shigi da fice ta Najeriya da ke jihohi domin ɗaukar hoto da ma karɓar fasfo ɗin. Haka ma ƴan Najeriya da ke ƙasashen waje, sukan je ofishin jakadanci domin yin fasfo din a wurin jami'an na shige da fice.

To sai dai a yanzu al'amura sun sauya inda ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya ce samar da fasfo zai koma a Abuja amma kuma mutum zai iya bayar da bayanai a sauran cibiyoyin.

Ministan ya ce sakamakon gina wannan cibiyar ta samar da fasfo, hukumar hana shigi da fice za ta rinƙa samar da fasfo 4,500 zuwa 5,000 a ƙasa da sa'a biyar.

A baya ana samar da fasfo 250 zuwa 300 ne kacal a ranar in ji ministan.

Rijista ko bayar da bayanai daga gida

A baya idan mutum zai bayar da bayanan da za a yi amfani da su a fasfo dole sai ya ɗaya daga cikin ofisoshin hukumar da ke faɗin Najeriya.

To sai dai tun a shekarar 2024 ne al'amura suka sauya cewa mutum zai iya zuba bayanansa da kansa daga gida ta hanyar intanet, kafin kuma daga bisani a kira shi domin ɗaukar hoto da yatsu.

Farashin fasfo

..

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 1 ga watan Satumba 2025 ne hukumar ta shigi da fice ta sanar da fara amfani da sabon farashin fasfo a ƙasar.

  • Fasfo mai shafi 64: Shi wannan fasfo mai shafi 64 yana da tsawon shekara 10 da aka ɗeba masa kafin ya daina aiki kuma farashinsa shi ne naira 200,000.
  • Fasfo mai shafi 32: Wannan nan ne ƙaramin fasfo mai shafi 32 wanda kuma yake da tsawon shekaru 5 da aka ɗeba masa kafin ya daina aiki kuma farashinsa ya kama naira 100,000.

Lokacin jira

Ministan harkokin cikin gidan na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo ya ce idan aka fara amfani da wannan katafariyar cibiyar yin fasfo, za a rinƙa samun fasfo ɗin a tsawon mako guda bayan kammala ɗaukar bayanan mutum.

A baya dai mutanen kan kwashe mako shida kafin su samu fasfo ɗin nasu kamar yadda ministan harkokin cikin gidan na Najeriya ya sanar.