Abin da ya sa mata suka fi maza saurin kamuwa da ciwon sanyin al'aura

Mace riƙe da ciki
Bayanan hoto, Cutar sanyi na iya yin mummunar illa ga lafiyar mata
    • Marubuci, Rebecca Thorn
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health
  • Lokacin karatu: Minti 6

Kin taɓa jin fitsari ya matse ki, kika yi gaggawar zuwa banɗaki amma fitsarin ya ƙi fitowa? Ko kina jin ƙaiƙayi da zafi yayin de kike fitsari?

Waɗannan na iya zama manyan alamomin ciwon sanyi na mafitsara (UTI), wadda ke da matuƙar zafi da ciwo a lokacin da ta kama mutum.

A duk duniya, an ƙiyasta cewa sama da mutane miliyan 400 ke kamuwa da ciwon sanyin mafitsara wato UTI a kowace shekara.

Duk da cewa wannan cuta tana iya kama maza da yara, mata ne suka fi kamuwa da ita – kusan rabin mata a duniya za su yi fama da cutar sanyi a wani lokaci na rayuwarsu.

Tun da wannan na ɗaya daga cikin mafi yawan cututtuka a duniya, har yanzu ana tambayar yadda za a tabbatar da samun ingantaccen magani, musamman a wannan zamani da ake fuskantar ƙalubale na bijirewar magungunan kashe ƙwayoyin cuta (antimicrobial resistance).

Ta dalilin haka ne BBC ta nemi ra'ayin masana don fahimtar abin da ya kamata mu sani da kuma matakan da za a ɗauka don kare kai daga kamuwa da ita.

Me ke janyo ciwon sanyin mafitsara?

Sanyin mafitsara cuta ce da ke kama hanyar mafitsara ko kuma a wasu lokutan idan ta yi tsanani har ma takan kama ƙoda.

Sau da yawa kwayoyin cuta ne ke haddasa ta, musamman idan suka shiga hanyar mafitsara.

Yawanci irin waɗannan ƙwayoyin cuta – kamar E.coli – na fitowa ne daga wajen ƙarshen uwar hanji.

Mata da 'yanmata sun fi saurin kamuwa da cutar sanyi saboda yanayin hanyar fitsarinsu idan aka kwatanta da ta maza, hakan yana sauƙaƙa wa ƙwayoyin cuta su shiga cikin mafitsara.

Haka kuma, matan da suka shiga lokacin da al'adarsu ta yanke sun fi shiga haɗarin kamuwa da irin waɗannan cutuka, saboda raguwar sinadarin oestrogen a jikinsu wanda ke taimakawa wajen kiyaye daidaiton ƙwayoyin cuta a gaban mace, don haka raguwarsa kan iya sa mace ta fi zama cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Mene ne alamomin cutar?

Alamomin ciwon sanyin mafitsara (UTI) na iya bambanta tsakanin mutane, amma wasu daga cikin mafi yawan alamomin da Hukumar Lafiya ta Birtaniya (NHS) ta bayyana sun haɗa da:

  • Jin zafi ko ƙaiƙayi wajen yin fitsari (dysuria)
  • Saurin matsuwa ko yawan yin fitsari fiye da yadda aka saba
  • Fitsari mai hazo ko duhu
  • Jini a cikin fitsari
  • Ciwo a mara ko ciwon baya a ƙarƙashin haƙarƙari
  • Zazzaɓi, jin zafi ko sanyi, da kuma jiri
  • Jin gajiya ko rauni

Ga tsofaffi, UTI na iya haifar da sauyin yanayi ko halin mutum, kamar rashin natsuwa ko rikicewa.

A cikin yara, fitsari a gado da amai na iya nuna alamar UTI.

Ciwon sanyin mafitsara na iya warkewa da kansa?

A woman holds her abdomen while holding a blue and green pill in front her. There are packets of pills behind her, along with a glass of water and an alarm clock on a side table.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Maganin kashe ƙwayoyin cuta ne hanyar da aka fi amfani da ita wajen maganin cutar mafitsara
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ga wasu mata, ba sa buƙatar magani, jikinsu kan magance cutar sanyin mafitsara da kansa. Amma wasu suna buƙatar maganin antibiotics," in ji Dr Rajvinder Khasriya, ƙwararre a sashen kula da lafiyar mafitsara a asibitn Whittington da ke London.

Ba a fahimci dalilin da ya sa wasu mata ke warkewa da kansu ba yayin da wasu kuma ba haka ba ne.

A yayin da ake samun ƙaruwar bijirewar magungunan kashe ƙwayoyin cuta, wannan muhimmin bincike ne.

Cutukan sanyi na mafitsara na ɗaya daga cikin cututtuka da ake yawan ba da maganin antibiotics a kansu.

Dr Katherine Keenan ta gudanar da bincike kan waɗanda suka kamu da cutukan mafitsara da ke bijire wa magunguna a yankin gabashin nahiyar Afirka, ciki har da Tanzania da Kenya da Uganda, inda rabin masu zuwa asibiti ke da irin waɗannan cutuka.

Kunyar magana da tsangwama na hana mata neman kulawar a lokacin da suke fama da cutar. "Suna ɓoye kansu saboda suna tsammanin alamominsu na iya bayyana ko suna tunanin cuta ce ta jima'i ko daga abokin tarayya," in ji Dr Keenan.

Bincike na Global Burden of Disease ya nuna cewa fiye da kashi 50 na masu ɗauke da cutar sanyin mafitsara na fuskantar wasu lalurori, kamar tsananin damuwa.

Shin cuta ce da ake ɗauka?

Duk da cewa sanyi cuta ce da mutum ke iya ɗauka daga wani, amma ba cuta ba ce da ke saurin yaɗuwa ba, kuma ba cuta ce da ake ɗauka ta hanyar jima'i ba.

Sai dai, yin jima'i na iya ƙara haɗarin kamuwa da cutar sanyi saboda za a iya tura cuta daga wurin dubura zuwa kafar mafitsara a lokacin jima'i.

Hukumar Lafiya ta NHS tana bayar da shawarar a yi fitsari nan da nan bayan jima'i don wanke duk wata ƙwayar cuta da ka iya shiga cikin mafitsara.

A lokacin da cutar ke yawan dawowa, likitoci na iya ba da maganin antibiotic da za a sha nan take bayan jima'i.

Ta yaya ake gano cutar sanyin mafitsara?

A woman holds a pot of urine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Likitoci za su iya buƙatar wadda ke da alamomin cutar ta kawo samfurin fitsarinta domin gwaji

Hanya mafi sahihanci wajen gano cutar sanyin mafitsara ita ce gwajin fitsari.

Ana ɗaukar samfurin fitsarin mai cutar a ka shi zuwa dakin bincike, inda za a gwada domin gano ƙwayar cuta a kan farantin gwaji.

Bisa sakamakon ne likita zai iya tantance wane magani ya fi dacewa don magance cutar.

Sai dai, wasu ƙwararru suna gargadi cewa gwajin fitsari don gano cutukan sanyi tsohuwar hanya ce, kuma likitoci ya kamata su yi la'akari da alamomin wanda ya kamu da cutar da tarihin lafiyarsa.

An ƙirƙiri gwajin fitsari a shekarun 1950 tare da gudunmawar wani masani mai suna Edward Kass, bisa bayanan da ya samo daga mata masu ciki da ke fama da cutar ƙoda.

Idan ka na tunanin kana da cutar sanyin mafitsara, ya kamata ka nemi shawara daga ƙwararren likita.

Ta yaya za a kiyaye dawowar cutar?

...

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu bincike sun nuna cewa lemun cranberry yana taimakawa wajen hana ko magance cutar UTI yayin da wasu suka nuna babu wani amfani.

An kiyasta cewa kashi 25 na mata da suka taɓa samun cutar sanyi za su iya sake samun ta: aƙalla sau biyu a cikin wata shida, ko sau uku a shekara.

Domin kare kai daga cutar sanyin al'aura, hukumar lafiya ta Birtaniya ta bayar da shawara kamar haka:

  • Mutum ya goge wurin ban ɗaki kafin yin bayan gida
  • Tsaftace jikin al'aura da kuma goge duk wani danshi
  • Shan ruwa mai yawa don yin fitsari akai-akai
  • Wanke fatar kusa da farji kafin da kuma bayan saduwa
  • Yin fitsari nan da nan bayan saduwa
  • Sauya ƙunzugu da zarar ya cika ko ya ɗauki datti
  • Sanya ɗan kamfai na auduga

Cibiyar nazari kan lafiya ta NICE da ke Ingila tana ba da shawarar amfani da ƙananan magungunan antibiotic don rigakafi kan yawan dawowar cutar sanyi.

Haka nan akwai zaɓin amfani da sanadaran estrogen na al'aura ko maganin methenamine hippurate, wanda ke aiki a matsayin maganin kashe kwayoyin cuta da ke cikin fitsari.

Mece ce cutar sanyi mai tsanani?

Baya ga cutar sanyi da ke yawan dawowa akai-akai, ana samun cutar mai tsanani inda mutum ke jin alamun cutar kullum.

Bincike ya nuna cewa wasu ƙwayoyin cuta na iya shiga cikin bangon mafitsara ko manne wa bangon mafitsara inda magunguna ba sa isa wurin.

Har yanzu masana na bincike domin gano dalili da kuma yadda mutum ke samun cutar sanyi mai tsanani.

Dr. Khasriya ta ce, "Akwai bayanai da yawa da ba a sani ba saboda bincike kan cutukan sanyi da lafiyar mata ba su wadatar ba."