Matar da aka haifa 'babu mahaifa' ta haihu

- Marubuci, Fergus Walsh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Medical editor
- Lokacin karatu: Minti 4
An haifi wata 'ƴar baiwa' wadda ta zamo jaririya ta farko da aka haifa a Birtaniya bayan an bai wa mahaifiyarta gudumawar mahaifa.
Mahaifiyar jaririyar mai suna Grace Davidson, mai shekara 36, tun farko an haife ta ne ba tare da mahaifar da za ta iya renon ciki ba, inda a shekarar ta 2023 ƴar'uwarta ta ba ta gudumawar mahaifa - lamarin da ya zamo karo na farko a Birtaniya da aka yi dashen mahaifa cikin nasara.
Shekara biyu bayan wannan dashe, Grace ta haifi ɗiyarta ta farko a watan Fabarairun da ya gabata. Ita da mijinta Angus, mai shekara 37 sun sanya wa jaririyar suna Amy, wato sunan yayar Grace, wadda ita ce ta bai wa ƴar'uwar tata mahaifar.
Grace wadda ke riƙe da jaririyarta Amy, mai nauyin kilo biyu, ta ce ba za ta iya bayyana irin farin cikin da take ji ba da ta zama uwa a karon farko.
Grace da mijinta Angus, waɗanda ƴan asalin Scotland ne amma suke zama a birnin Landan, na sa ran samun haihuwa ta biyu nan ba da jimawa ba da mahaifar da aka ba su gudumawa.
A farko ma'auratan ba su so su fito fili su bayyana kansu ba, amma bayan haihuwar jaririyarsu Amy, sun yanke hukuncin tattaunawa da BBC kan abin da suka kira "ƴar baiwa".
Likitocin da suka yi wa Grace aikin dashen mahaifar sun ce sun ƙara yin irin wannan dashe sau uku ta hanyar amfani da mahaifar mutanen da suka mutu, tun bayan aikin da suka yi wa Grace.
Sun ce suna sa ran yin dashen maihaifa 15 a matakin gwaji.

Asalin hoton, WTUK
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An haifi Grace ne da wata lalura da ba a cika samu ba, wadda ake kira Mayer-Rokitansky-Küster-Hauser (MRKH) syndrome, inda mace kan zo babu mahaifa kwata-kwata ko kuma ko da akwai mahaifar ba cikakkiya ba, sai dai sukan zo da ƙwayaƙwayan haihuwa.
A karon farko da BBC ta tattauna da ita a shekarar 2018, Grace na sa ran mahaifiyarta za ta ba ta mahaifarta domin ta samu damar haihuwa - sai dai daga baya an gano cewa mahaifar mahaifiyar tata ba ta yi daidai da jikin Grace ba.
A shekarar 2019, BBC ta sake tattaunawa da Grace da mijinta Angus, lokacin da ake auna ƴar'uwar Grace, wato Amy Purdie, domin gano ko mahaifarta za ta yi wa Grace.
Amy da mijinta sun riga sun haifi yara biyu, kuma ba su da buƙatar ƙara haihuwa.
An zaunar da ƴan'uwan biyu aka yi masu bayanio dalla-dalla gabanin tiyatar dashen mahaifar.
Grace ta ce an yi mata tayin amfani da tsarin amfani da mai dakon juna-biyu ko kuma ta karɓi riƙon yara, amma a cewarta ɗaukar jinjirin da ta rena a cikinta "abu ne mai matuƙar muhimmanci".
"Na kasance ina son zama uwa," in ji ta, "amma sai na riƙa dannewa a raina saboda halin da nake ciki."
Haihuwa ta farko da aka samu bayan yin dashen mahaifa a duniya ta faru ne a ƙasar Sweden a shekarar 2014. Tun daga wancan lokacin an yi dashen mahaifa kimanin sau 135 a fiye da ƙasashe 10, ciki har da Amurka da China da Faransa da Jamus da Indiya da kuma Turkiyya. Kuma an haifi jarirai kimanin 65 bayan dashen.
Kimanin likitoci 3o ne suka yi aiki a kan Grace lokacin dashen mahaifar da aka yi mata a watan Fabarairun 2023, inda suka kwashe sa'o'i 17 suna aikin cire mahaifar daga jikin Amy tare da mayar da ita a cikin Grace.

Asalin hoton, WTUK
An haifi jaririya Amy ne ta hanyar tiyata a asibitin Queen Charlotte's da ke yammacin birnin Landan a ranar 27 ga watan Fabarairu.
Grace da Angus sun ce suna sa ran samun ɗa na biyu - da zarar masana lafiya suka ce masu za ta iya sake ɗaukan ciki.
Za a cire mahaifar da zaran Grace ta haihu sau biyu. Hakan zai bai wa Grace damar daina shan maganin da take yi a kullu-yaumin, wanda ke hana jikinta botsare wa mahaifar da aka dasa mata.
Shan waɗannan magunguna a kowace rana na iya ƙara mata haɗarin kamuwa da cutar kansa, musamman idan za ta kwashe shekaru masu yawa tana sha - amma likita Isabel Quiroga ya ce haɗarin kamuwa da kansar zai kau idan ta daina shan magungunan.











