Ƙasashen da ake magana da harshen Hausa

Ginin al'ada a ƙasar Hausa

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Hausa ta zamo ɗaya daga cikin manyan harsunan duniya da ake amfani da su a mu'amullar yau da kullum da kuma yaɗa saƙonni a kafafen yaɗa labarai da kuma shafukan sada zumunta.

Masana sun tabbatar da cewa harshen na ƙara bunƙasa, kama daga yadda mutane da dama a sassa daban-daban ke amfani da shi wajen magana da juna da kuma ta fannin rubutu da wallafe-wallafe na littafai da jaridu da ƙasidu da ma a shafukan sada zumunta.

Farfesa Aliyu Muhammad Bunza na jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto a Najeriya yana daga cikin masana da suka yi fice wajen nazarin harshen Hausa kuma yana ganin cewa harshen ya zarce yadda ake masa kallo.

Ya ce ''A ƙidayar da aka yi a duniya, cikin harsuna 7,500 Hausa ita ce ta 11 da yawa. Sai dai mu ɗalubai ba mu ƙaryata malamanmu ba don binciken mu ya nuna Hausa ita ce ta 7 a duniya''.

Masanin ya yi bayanin cewa daga binciken da malaman harshen Hausa magabata suka yi, babu wata ƙasa a yankin Afirika ta Yamma da Hausawa ba su da yawa ''ko a ce Ƙabilun asalin ƙasar da kaɗan suka rinjayi Hausawa''.

''Don haka Afirika ta Yamma ana ganin Hausawa sun fi yawa ƙwarai''. in ji Farfesa Bunza.

Ya ƙara da cewa a tsakanin sauran ƙasashen ƙasashen Afirika, babu ƙasar da Hausawa ba su ziyarce ta ba, ko suna ziyartar ta har yanzu. ''kuma wannan ziyara idan muka bi al'adar Hausawa ta zarce shekara ɗari. Ka ga kenan dogon tarihi ne,''

Farfesa Bunza ya jaddada cewa ''in ka dubi bayyanar addinin annabi Isah da ya gabaci musulumci, da hannun Hausa a ciki. To za ka ga cewa Hausawa suna da alaƙa da sauran ƙasashen duniya fiye da 700 ko 600.''

Wasu daga cikin ƙasashen da Hausawa ke da yawa su ne:

Najeriya

Najeriya ita ce kasar da ta fi yawan al’umma masu amfani da harshen Hausa, musamman arewacin kasar inda nan ne cibiyar harshen.

A ƙarshen shekara ta 2016, wani taro da aka gudanar a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya bayyana cewa yawan masu amfani da harshen Hausa a Najeriya ya kai miliyan 120.

An gudanar da taron ne a sashen harsunan Afirka da al’adu na jami’ar, inda a karshe aka fitar da takardar sanarwa.

Sanarwar ta ce yawan masu amfani da harshe wani sharadi ne na ayyana shi a matsayin harshen hukuma.

“Sannan ana rarraba masu amfani da harshe zuwa gida biyu, wadanda ke amfani da harshe a matsayin harshen uwa da kuma wadanda suka tsince shi daga bay.

A Najeriya akwai mutum mikiyan 70 masu amfani da harshen a matsayin harshen uwa sannan sai wasu mutanen kimanin miliyan 40 zuwa 50 wadanda suke amfani da harshen ba a matsayin harshen uwa ba,” in ji sanarwar.

Jamhuriyar Nijar

Kusan rabin al'ummar Jamhuriyar Nijar na magana ne da harshen Hausa, abin da ya sanya a shekara ta 2025 ƙasar ta ayyana Hausa a matsayin harshen ƙasa.

Duk da cewa akwai harsuna 11 da hukuma ta ayyana a kasar a matsayin na hukuma, to amma Hausa ne ke da mafi yawan masu amfani da shi, inda kimanin kashi 47 cikin dari na al’ummar kasar miliyan 27 ke magana da shi.

Ghana

Baya ga harshen Akan (Twi), Hausa ne harshe na biyu da aka fi magana da shi a ƙasar Ghana.

Ƙiyasi, wanda ba na hukuma ba na nuna cewa akwai sama da mutum miliyan biyar da ke amfani da harshen Hausa a Ghana.

Akwai Hausawa a dukkanin shiyyoyi 16 na ƙasar, inda suke zaune a unguwanni da ake kira Zango, inda a Accra babban birnin ƙasar akwai manyan Zangonni sama da 10.

Saudiyya

Ana kiyasin cewa akwai Hausawa sama da mikiyan daya da ke rayuwa a kasar Saudiyya, wadanda akasarinsu tsatson mutane ne da suka yi kaura tare da samun wurin zama a kasar, musamman wadanda suka je kasar da nufin aikin Hajji.

Yawancin irin wadannan mutane ana yi musu lakabi da Hausawi ko Hawsawi, inda suke zama a yankuna daban-daban na kasar.

Wasu bayanai na cewa yawancin Hausawan da suke zama a Saudiyya, sun cikin Musulman da suka tashi daga yankin yammacin Afirka zuwa yankin Larabawa a ƙarni na 19 domin guje wa turawan mulkin mallaka.

Ina ne asalin Hausawa?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dangane da wajen da za a kira asalin Hausa kuwa, Farfesa Bunza ya ce ''Ba mu cewa komai sai abin da su malamanmu suka faɗa domin ba mu fi su ilimin ba.''

Ya ƙara da cewa ''sun tabbatar mana Hausawa ƴan asalin ƙasar Hausa ne, nan aka haife su, nan ƙasar su ta kafu, duk wanda ya zo cikin ta an hausantar da shi,''

Masanin harshen Hausa ya kuma kafa misalan da ke goyon bayan bayanin nasa inda ya ce ''Gwarzon Bahaushe da aka sani ya buwaya ga kare kai da yaƙi, ba a kai Bagobiri ba. Gobirawa sun ce daga wata ƙasa suka ito can gaban Egypt. In ka dubi managarta a Hausawa, ka sami Kabawa ka gama. Kabawa sun aminta cewa su ƴan ƙasar Hausa ne, amma sun tabbatar cewa su daga ƙasar Larabawa suka fito.''

''Idan aka bi haka, sai a ce a godewa manyan malamanmu cewa asalin ƙasar Hausa ba ta bata rasa alaƙa da Katsina da Zamfara, duk inda ta yaɗu kuma yaduwa ta yi.''

Wannan na tabbatar da cewa asalin Hausawa ƴan Najeriya ne.

Farfesa Bunza ya ce ko zance da ake yi cewa Bayajidda ne ya kawo Hausa zance ne maras tushe, domin ko a yadda tarihin ya nuna a lokacin da ya zo ƙasar Hausa ya tarar da Saurauniya Daurama a matsayin sarauniya ta 10 a masarautar ƙasar Daura.

''Cewa shi ne tushen su, lamarin ƙanzon kurege ne.'' in ji Farfesa Bunza.