Yadda za ka gano idan kana da kansar hanji

Mace.

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Philippa Roxby
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Health Reporter, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 5

Dame Deborah James, wadda ta rasu a sakamakon kamuwa da cutar daji ta hanji tana da shekara 40, ta bayar da shawara ga kowa, da mutum ya riƙa duba kashinsa a matsayin wata hanya ta fadakarwa a kan wannan nau'in cutar kansa.

Amma mece ce wannan kansa, kuma ta yaya za a iya gane ta?

Ta yaya zan gane alamun cutar?

Akwai muhimman abubuwa uku da za ka duba:

  • Ka ga jini a kashinka ba tare da wani dalili ba - zai iya kasancewa mai haske-haske ko kuma mai duhu.
  • Sauyin yadda kake kashi - kamar yawan zuwa bahaya ko kashinka ya zama da tauri ko ruwa-ruwa.
  • kasan cikinka ya riƙa ciwo ko kuma kumburin ciki, ka riƙa jin cikin bam-bam.

Za a iya samun wasu ƙarin alamun:

  • Ramewa
  • ka yi kashi ka ji kamar da saura a cikinka
  • Jin gajiya ko juwa ko hajijiya fiye da yadda ya kamata

Ganin waɗannan alamomi ba wai lalle hakan na nufin kana da cutar daji ta hanji ba ne.

Amma shawara ita ce ka je ka ga likita, idan har ka ga alamar ta wuce mako uku ko fi, ko kuma idan ba ka jin daɗi.

Hakan na nufin za a iya saurin gano matsalar a magance ta.

Ita cutar daji gano ta da wuri kan sa a iya magance ta da wurwuri.

Jini.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ka duba jini a kashinka ko kuma a duburarka

Wani lokaci cutar daji na iya hana mutum bahaya, wanda hakan na iya toshe dubura.

Wannan na iya sa ciwon ciki mai tsanani da rashin yin kamshi da kuma rashin lafiya.

Idan ka samu kanka a wannan yanayi to ba shakka kana buƙatar ka garzaya zuwa asibiti da gaggawa.

Ta yaya zan iya duba kashina?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ka sa ido sosai ka ga yadda kashinka yake kuma kar fa ka ji kunyar yin magana a kai.

Ka duba sosai ka ga ko akwai jini a cikin kashinka ko kuma daga can kasan kashin.

Jini mai haske ka iya kasancewa daga wata jijiya ce da ta kumbura a duburarka wato basir kenan, haka kuma zai iya kasancewa cutar dajin ce ta janyo.

Idan jinin yana da duhu a kashinka, to hakan zai iya kasancewa daga hanjinka ko kuma tumbinka yake, shi ma kuma zai iya kasancewa abin damuwa.

Za kuma ka iya samun sauyi a yanayin bahayarka, kamar kashin ya kasance ruwa-ruwa ko kuma zuwa banɗaki fiye da ƙima.

Ko kuma ka ji kamar da sauran kashi a cikinka bayan ka je bandaki.

Haka kuma rashin zuwa banɗaki yadda ya kamata.

Ƙungiyar likitocin cutar kansar hanji ta Birtaniya na bayar da shawar a riƙa rubuta jerin bayanan alamun da mutum ya gani kafin ya je ganin likita, saboda kada ka manta da wani abin.

Likitoci sun saba ganin mutane da alamun matsaloli daban-daban na hanji, saboda haka ka gaya wa likita duk wani sauyi da ka gani ko kuma jinin da ka gani domin a gano abin da ya haifar da hakan.

Hanji.

Asalin hoton, Getty Images

Me ke janyo cutar kansa ta hanji?

Ba wanda zai iya cewa takamaimai ga abin da ke janyo cutar, to amma akwai abubuwan da ake ganin za su iya janyo ta:

  • Yawan shekarunka - yayin da kake shekaru kana shiga yanayin da za ka iya kamuwa da cutar daji - yawancin masu wannan cuta ta kansa ta hanji manya ne 'yan sama da shekara 50
  • Cin abinci da jan nama mai yawa da kuma abincin gwan-gwani (na kamfani wanda ake sayar wa a kanti)
  • Shan taba kan iya kara hadarin kamuwa da cutar daji
  • Shan giya da yawa
  • Teɓa da yawa
  • Idan kana da matsalar da hanjinka ke hayayyafar wasu 'yan kananan kumburi ko kuraje, da ka iya zama daji

Ko ana gadon cutar dajin ta hanji?

Yawanci ba a gadon cutar, to amma idan akwai wani a danginku da aka taɓa samu da ita kafin ya kai shekara 50 to yana da kyau ka gaya wa likita.

Akwai yanayi na gado kamar matsalar kuraje ko kumburi a hanji, wanda hakan ka iya haddasa cutar. To amma likitoci za su iya magance wannan idan sun san da ita.

Kansar hanji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Hanjin mutumin da ke fama da cutar kansar hanji

Yadda za ka kare kanka daga hadarin cutar?

Masana kimiyya sun ce za a iya kare kusan rabin haɗarin kamuwa da cutar idan mutum yana bin hanyoyin rayuwa na lafiya.

Wannan na nufin yawan motsa jiki da cin ƴaƴan itace da ganyayyaki da rage cin maiko da shan ruwa kusan kofi shida zuwa takwas a duk rana.

Bayan waɗannan akwai kuma buƙatar zuwa ganin likita a duk lokacin da ka ga wata alama, da kuma amfani da damar yin gwajin cutar daji a duk lokacin da aka samu damar.

Za a iya min gwaji?

Ana yin gwaji don gano alamun cutar daji ta hanji tun ba ta yi girma ba.

Akwai kayan gwaji na gida, wanda ke gano awata lamar jini a kashinka. Gwajin da za ka iya yi a gida ka aika asibiti.

Sai dai ba kowa ba ne yake samun wannan abin gwaji, sai wadanda ke rukunin shekarun da ake ganin za su iya samun cutar.

Ana yin gwajin a faɗin Birtaniya.

  • A Ingila a hankali ana rage yawan shekarun da mutum ya cancanta a yi masa gwajin daga 60 zuwa 50 zuwa sama.

Ba a samun dacewa ɗari bisa ɗari a bincike, wanda kuma zai iya kai wa ga yin maganin da zai iya cutarwa ko kuma wanda bai kamata ba, idan ana gwajin mutane da yawa masu lafiya.

Saboda haka idan kai matashi ne kuma kana da alamun cutar, yana da kyau ka san alamun kuma ka ziyarci likitanka idan har ka damu - kada ka sayi kayan gwajin ka je ka yi da kanka, saboda sakamakon ka iya ba ka wani abu mai rikitarwa.

Waɗanne hanyoyin magani ake da su yanzu?

Ana maganin cutar daji ta hanji musamman ma idan ana gano ta da wuri.

A duk matakin da aka gano mutum na ɗauke da cutar za a iya gaya masa abin da za a iya yi a kai.

Wannan ka iya kasancewa tiyata ko gashi ko kuma amfani da magunguna domin kashe kwayoyin cutar, ya dai danganta ga yanayin cutar a jikin mutum.

Waɗanne matakai ake da su na girman cutar?

  • Mataki na 1 - cutar karama ce kuma ba ta yaɗu ba
  • Mataki na 2 - cutar ta yi girma, amma har yanzu ba ta fara yaɗuwa ba
  • Mataki na 3 - ta fara yaɗuwa a jikin wasu jijiyoyin da ke kusa da ita
  • Mataki na 4 - cutar ta yaɗu har ta kama wani ɓangare na ciki ta haihu