Yaƙin Cambodia da Thailand ya tsananta

Sojoji a motocin yaƙi

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

An shiga kwana na uku a artabun kan iyaka da ake yi tsakanin sojojin kasar Thailand da kuma na makwabciyarta Kambodiya.

Yaƙin ya janyo asarar sama da mutum talatin da kuma dubbai da suka bar muhallinsu, tun bayan da rikicin kan iyakar ya barke kwatsam ranar Alhamis.

Rahotanni na cewa sojojin ruwa na Thailand sun danna dakarun Kambodiya baya a can kuryar kudu ta iyakar kasashen biyu, iyakar da ta mika har zuwa teku.

Wannan kenan ya sa fadan tsakanin makwabtan junan ya fadada zuwa wani sabon yankin daban.

Yunkurin diflomasiyya na farko-farko da aka yi don dakatar da rikicin, ya kasa samun wata nasara ta a-zo-a-gani.

A lokacin wani taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, Kambodiya ta ce a shirye take idan za a dakatar da bude wuta nan take kuma ba tare da wani sharadi ba.

To amma Thailand ta ce a'a ba ta ga alamun hakan ba, ganin cewa dakarun Kambodiya sun kai hari wannan sabon yanki na kudu da a da rikicin bai fadada zuwa can ba.

Tun kafin sannan ma mai rikon mukamin Firaministan Thailand din, Phumtham Wechayachai ya ce, ta yiwu a samu Kambodiya da aikata laifin yaki – saboda mutuwar fararen hula a hare-haren da ta kai wa kasarsa.

Haka kuma Thailand, cikin karamci ta ki amincewa da yunkurin da Firaministan Malaysia, Anwar Ibrahim ya yi na kawo karshen rikicin – saboda bacin ran da take ciki kan mutuwar fararen hula 13 a sanadiyyar wani makamin roka da Kambodiya ta kai mata hari da shi ranar Alhamis.

Thailand na ta ruwan makaman roka zuwa yankin Kambodiya kusan ba kakkautawa daga inda ta jibge makaman atilari a wajen babbar iyakar kasashen biyu.

Thaksin Shinawatra, wanda jam'iyyarsa ke jagorantar gwamnatin hadaka a kasar ta Thailand, ya ce akwai bukatar a koya wa shugaban Kambodiya, Hun Sen darasi.

Barkewar rikicin kwatsam a watan da ya gabata tsakanin tsofaffin abokan junan biyu, ta sa dangantaka ta yi tsami – wadda daman tuni take tangal-tangal saboda rikicin kan iyaka da ake ta samu a tsakanin kasashen biyu.