Musulmin China na tsaka-mai-wuya a Thailand

Hoton wasu 'yan Uhygur

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Adem Karadag a gaba sai Yusufu Mieraili daga baya, lokacin da suke shiga kotun sojoji a Bangkok a 2016

Mutuwar wani Musulmi ɗan shekara 49 ɗan ƙabilar Uyghur ta China da ke neman mafaka a Thailand ta sanya ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam neman mafita ga halin da wasu Musumin 50 ke ciki, waɗanda ake tsare da su a Thailand kimanin shekaru tara.

Aziz Abdullah ya mutu ne kwatsam a wata cibiyar da ake tsare ‘yan cirani a Bangkok inda ake tsare da shi.

Yana cikin Musulmi 350 ‘yan asalin Uyghur da suka nemi mafaka bayan sun tsere daga Xinjang a yammacin China a 2013, amma aka tsare su a Thailand.

An riƙa zargin China da aikata laifukan cin zarafi ga Musulman Uyghur da kuma wasu ƙabilun marasa rinjaye da ke Xinjiang.

ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam sun ce China ta tsare sama da mutum miliyan ɗaya a wata cibiyar tsare mutane mai kama da sansani a ‘yan shekarun baya.

Sai dai Beijing wadda ta kira waɗannan cibiyoyi “wajen ilimantarwa”, ta musanta duka waɗannan zarge-zarge.

Aziz Abdullah dai manomi ne a wani yanki a kudu maso yammacin Xinjiang.A 2013 kuma ya gudu Thailand da matarsa da ke da ciki da ɗan uwansa da kuma 'ya'yansa bakwai.

Masu fafutukar da ke waya da wasu da ake tsare da su a cibiyar da ake tsare ‘yan cirani sun ce, ya kai mako uku yana fama da rashin lafiya, kuma hukumomin Thailand sun ƙi amincewa su kai shi asibiti domin a yi masa maganai har sai da ya faɗi.

“Ya daɗe yana tari da kuma aman jini – ba ya iya cin abinci,” in ji Polat Sayim, daraktan cibiyar kula da ‘yan ciranin Uhyghur ta duniya da ke zaune a Australia.

“Wani likitan cibiyar da ake tsare da su ya duba shi sannan ya ce rashin lafiyar tasa ta ƙarya ce, babu abin da ke damun shi.”

Amma bayan ya faɗi sai aka kai shi asibiti, sannan kuma ya ce ga garinku nan ba da jimawa ba. Shaidar mutuwar da asibitin suka bayar ta nuna ya samu matsalar huhu ne, kuma ita ce ta yi sanadin mutuwarshi.

.

Asalin hoton, CCTV

Bayanan hoto, Thailand ta yanke shawarar mayar da mutanen Uyghur 109 zuwa china a 2015, duk da kiraye-kirayen da MDD ta yi.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu fafutuka sun ce ya fito tare da mutanensa ne da niyyar su je Malaysia, daga baya kuma su tsallaka Turkiyya, amma sai aka kama su a kudancin Thailand.

A wannan lokacin, mafi yawan Musulman Uyghur na cewa su ‘yan Turkiyya ne domin kar a mayar da su China, saboda ita Turkiyyar tana ba su shaidar zama ‘yan ƙasa.

A watan Yulin 2015, Thailand ta kyale mutum 173 daga cikinsu tsallakawa Turkiyya, kuma ciki har da mata da ‘ya’yan Aziz.

Amma, China ta ƙalubalanci hakan, inda ta zargi Turkiyya da shiga harkokin ƙasashe masu ‘yanci, tana kuma bai wa ‘yan cirani takardun zama ‘yan ƙasa ba bisa ƙa’ida ba.

A ranar 8 ga watan Yulin 2015, hukumomin Thailand sun bai wa ofishin jakadancin China damar zuwa cibiyar domin tantance masu neman mafaka.

Kuma roƙon da gwamnatoci da kuma hukumar ‘yan cirani bai samu karɓuwa ba, wanda ta nemi kada a mayar da mutanen Uyghur gida.

Thailand ta mayar da aƙalla mazaje 109 China a jirgin sama sanye da ankwa a hannuwa da ƙafafunsu.

Sun haɗa da ɗan uwan Aziz Abdullah.

Wannan mataki na yi wa ‘yan Uyghur da ke zaune a Turkiyya haka bai yi daɗi ba, abin da ya kai da suka riƙa jifan ofishin jakadancin Thailand da ke Istanbul.

Kafafen yaɗa labaran China sun bayyana su a matsayin mambobin gungun mutanen da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, wasu kuma an riƙa zarginsu da harkokin ta’addanci.

Babu dai wani labari game da makomar mutanen tun bayan mayar da su China.

Sai dai gwamnatin Thailand ta yi ta yunƙurin kare matakin da ta ɗauka, inda ta ce China ce ta nemi a mayar mata da duka ‘yan ƙabilar Uyghur da ke zaune a ƙasar, kuma wannan shi ne dalilin mayar da su.

Mako shida baya, an samu wata fashewar bam a wani wurin bauta da ke tsakiyar Bangkok da mutanen China ke yawan zuwa, an samu mutuwar aƙalla mutum 20, wasu da dama kuma sun jikkata.

Amma gwamnatin Thailand ta ce wani mataki ne na adawa da ƙungiyar mutanen da ke fasaƙauri ke yi da su, sai dai hujjojin da aka samu bayan faruwar abin sun nuna masu fafutuka ne daga ƙabilar Uyghur suka kai harin.

An kama wasu mutum biyu ‘yan ƙanbilar Uyghur kuma an tuhume su da kai wannan hari, ko da yake ɗaya daga cikinsu da ya ce ba hannunsa ciki yana cikin waɗanda suka nemi mafaka, kuma an kama shi ne lokacin da ‘yan sandan Thailand suka kai sumame wani gida da suke zargin cewa ana haɗa bam a cikinsa.

An yi ta ɗage sauraren shari’arsu, cikin sama da shekara takwas tun bayan kama su; alamu na nuna cewa hukumomin Thailand ba gaggawa suke ba wajen yi musu shari’a, har yanzu dai ana tsare da su.

Hoton iyalan

Asalin hoton, COURTESY ABDULLAH FAMILY

Bayanan hoto, Aziz Abdullah (a dama) da ɗan uwansa da 'ya'yansu kafin su tsere zuwa Thailand

Yanayin da suke ciki ba shi da kyau, in ji masu fafutukar da ke neman taimaka musu, babu ko ɗaya daga cikin waɗanda ake tsare da su da suke ganin juna kowa wurinsa daban.

“Abin ya yi muni, sama da na sauran fursunoni da ake tsare da su a ƙasar,” in ji Chalida Tacharoensuk daga gidauniyar People's Empowerment wadda ke fafutukar ganin an kyautata wa Musulman na China 'yan Uyghur.

“Inda ake tsare da su a cike yake da mutane. Ga shi ba sa samun isasshen abinci, wanda kuma ake ba su ba mai tsafta ba ne. Ba su da zaɓi kan cewa sai sun samu abincin halal a matsayinsu na Musulmai. Kayan shan da ake ba su duk ba masu tsafta ba ne – kuma dole su sha ruwan famfo. Babu abin da ya shafi kiwon lafiya a tsarinsu. Idan ba su da lafiya sai dai su sha maganin rage raɗaɗi ko kuma maganin da bai kai ya kawo ba.

Phil Robertson na kungiyar Human Rights Watch ya ce: “ Wannan mutuwar ba ta taɓa zuwa kan hukumomin Thailand ba, da tuni sun ɗauki mataki”.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mutum 20 ne suka mutu a harin da aka kai wurin bauta na Erawan

Gwamnatin Thailand ta yi alƙawarin aiki tare da Majalisar Ɗinkin Duniya domin kyautata yanayin da gwamman ‘yan gudun hijirar da suke neman mafaka a cikin ƙasar, sai dai har yanzu babu wani cigaba ga halin da suke ciki.

Masu fafutuka sun yi amannar cewa da ‘yan ƙabilar Uyghur za su samu dama a sake su da sun tafi wata ƙasar domin neman inda za su zauna su yi rayuwa mai kyau.

A ƙarshe dai an bai wa ‘yan uwa da ke Thailand gawar Aziz Abdullah, kuma tuni aka binne shi a wata maƙabarta da ke Bangkok.