Yara sun rayu bayan sun yi kwana 9 a kogon dutse a Thailand

Asalin hoton, Facebook/ekatol
An gano wadansu yara 'yan wasan kwallon kafa 12 da kocinsu bayan sun kawashe kwana tara a cikin wani kogon dutse mai cike da ruwa a kasar Thailand.
Wadansu masu aikin ceto 'yan kasar Birtaniya ne suka gano su bayan kwashe fiye da mako guda ana nemansu a wani da ke birnin Chiang Rai da ke arewacin kasar.
Iyalan yaran sun bayyana farin cikinsu bayan samun labarin gano yaran. Sai dai ba a kai ga fidda su daga cikin kogon mai zurfin kimanin mita 400.
Gwamnan yankin ya ce za a ci gaba da zuko ruwan da ke cikin kogon yayin da aka tura da likitoci don duba lafiyarsu.
Yaran wadanda shekarunsu suka kama daga 11 zuwa 16 sun je kogon ne a ranar 23 ga watan Yuni don yawon bude ido.
Masu aikin ceto suna kokarin kai musu abinci don su samu kuzari, kafin a ci gaba da yunkurin ceto.
Fiye ma'aikata fiye da 1000 ne suke aikin ceto wadanda suka fito daga kasashen China da Myanmar da Laos da, Australia da Amurka da kuma Birtaniya.







