Gaske ne Boko Haram ta kai hare-hare sau 333 a shekarar nan?

Asalin hoton, Boko Haram
Alƙaluman wata ƙungiyar ACLED mai sanya ido kan tsaro da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito sun nuna cewa ya zuwa yanzu Boko Haram ta kai hari sau 333, a yankin arewa maso gabashin Najeriya a wannan shekarar ta 2025.
To sai dai kuma kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited ya ce bisa alƙaluman da ya tattara, ƙungiyar Boko Haram ta kai hare-hare har sau 199 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Satumbar 2025.
Shugaban kamfanin Dakta Kabiru Adamu ya ce da dama masu nazarin ayyukan Boko Haram ba sa banbance tsakanin ƙungiyar da sauran ƙungiyoyi masu riƙe da makamai.
"Wani abu mai muhimmanci da masu bincike ba sa banbantawa shi ne akwai ƙungiyoyin da ba na Boko Haram ba da ke kai hari sai a kira su da Boko Haram. Misali akwai ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai amma ba sa iƙrarin jihadi, idan suka kai hari sai a yi kuɗin goro a ce Boko Haram," in ji Kabiru Adamu, Beacon Security and Intelligence Limited.
Ga wuraren da Boko haram ta kai hare-haren:
- Adamawa 21
- Borno 165
- Yobe 13
Sabuwar fasahar hare-haren Boko Haram
Wani abu da masana tsaro ke nuna damuwa a kai shi ne yadda ƙungiyar ke amfani da fasahar zamani wajen kai hare-hare, kamar amfani da jirage marasa matuƙa masu ɗauke da makamai ko kuma wajen tattara bayanai.
Kuma wataƙila sabunta fasahar kungiyar ne ya sa hare-haren nata suka yawaita saɓanin a baya lokacin da a koyaushe sai dai su kai samame.
Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin samar da tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce ko a watan Disamban 2024, mayaƙan sun kai wa sojoji hare-hare har sau hudu ta hanyar sanya bama-bamai jikin jiragen marasa matuƙi.
Dakta Kabir ya bayyana cewa ba yanzu waɗannan ƙungiyoyi suka fara amfani da jirgi maras matuƙi ba.
"A 2019 mun ga lokuta inda waɗannan ƙungiyoyi suke amfani da jirage maras matuƙa amma kawai domin leƙen asiri, suna dasa bama-bamai a waɗannan jirage."
Yadda Boko Haram ta kai samame sansanonin soji
A ranar Alhamis ɗin nan ne rundunar sojin Najeriya ta ce masu iƙirarin jihadi sun ƙaddamar da hare-hare lokaci ɗaya kan sansanoninta huɗu da ke arewa maso gabashin ƙasar, sai dai ta samu nasarar murƙushe su. Sai dai kuma a ɓangare aya
"A dukkanin hare-haren dakarun sun tsaya tsakin-daka, suka yi artabu cikin karsashi, suka murƙushe harin, inda suka yi wa ƴan ta'adda mummunar ɓarna"
A lokacin wannan artabu, a cewar rundunar "martanin sojojin ya kai ga halaka ƴan ta'adda 50.
Haka nan dakarun sun ƙwato bindigar AK-47 guda 38, da bindigar labarbar bakwai, da bindigar tarwatsa tankokin yaƙi guda biyar, da bindigar GPMG biyu da tarin gurneti da dubban harsasai.
Bugu da ƙari dakarun Najeriya sun ce suna ci gaba da neman sama da mutum 70 cikin waɗannan ƴan bindiga da aka raunata.
Ƙarfin Boko Haram
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Barrister Bulama Bukarti masanin harkar tsaro a ƙasashen Afirka da yankin Sahel ya ce duk da cewa an ci ƙarfin Boko Haram nesa ba kusa ba to amma har yanzu akwai sauran rina a kaba.
Ya ce dalilin da ya sa a baya ba a cika jin cewa sun kai hari ba shi ne tun bayan mutuwar Abubakar Shekau, shugabannin ƙungiyar na yanzu ba sa kai hare-haren kisa kamar irin na baya. Sannan kuma akan samu yanayin da ake ɓoye batun hare-haren da ƙungiyar ke kaiwa.
"Ƙunigyar tana nan da makamai da mayaƙa. Sannan Boko Haram da sojojin Najeriya kowa ya kama wani sashe ba a kai wa juna hari. To idan ka ga an yi irin wannan zama to kowanne ɓangare na neman dama ne kan abokin hamayyarsa.
Har yanzu Boko Haram na cikin dazuka da ƙauyukan tafkin Tchadi da arewacin jihar Yobe. Kuma a gaskiya sojojin Najeriya ba su fiya kai musu hari ba. Za ma a iya cewa kamar an sallama musu dazukan da ƙauyukan. Suna nan sun ja tunga kuma lallai sai an kai musu hari har inda suke idan ana so a gama da su,"kamar yadda Bulata Bukarti ya shaida wa BBC a kwanakin baya.
Hanyoyi biyar na kawo ƙarshen Boko Haram
Dakta Kabiru Adamu da Dr Bulama Bukarti sun amince da wasu hanyoyi da suka ce su ne idan aka bi su to za a ga bayan ƙungiyar Boko Haram.
- Dole a kai musu (Boko Haram na ɓoye a dazuka da kauyuka) yaƙi har maɓoyarsu.
- Daƙile yunƙurin ƙungiyar na ɗaukar sabbin mambobi.
- Daƙile hanyoyin samun kuɗaɗensu na gudanarwa.
- Daƙile hanyoyin samun makamai da hanyoyin sufuri.
- Bin dokokin daƙile hanyoyin ta'addanci a tsarin kundin Najeriya.











