Sababbin hare-haren Boko Haram na tayar da hankali a jihar Borno

BoKo Haram

Asalin hoton, Getty

Lokacin karatu: Minti 3

Karuwar hare-haren kungiyar Boko Haram a Borno a baya-bayan nan na sanya damuwa da fargaba ga al'ummar jihar.

Danmajalisar dattawan da ke wakiltar kudancin jihar ta Borno ne ya nuna damuwar a yayin hira da BBC, a kan yadda kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren a yankinsa.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce maharan sun kashe manoma a yankin Gwoza, lamarin da ya jefa al'ummar yankin cikin zaman dar-dar tare da tsoron zuwa gona.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da rundunar sojin kasar ta kara daukar kwararan matakai na dakile ayyukan kungiyar.

Sanatan ya ce: ''Hankalinmu ya fara dawowa jiki kuma mutane suna zuwa gona su noma abin da za su ci sai kuma aka fara samun sababbin hare-hare wadanda ba mu saba da su ba. Sun kashe mana mutum biyar a ranar Asabar.''

''To a ra ar Lahadi ma sun je Musa, wani gari wanda daman kwanan nan ne ma suka koma Musa din can Askira Uba, shi ne damuwarmu, muna gani wannan abubuwa ne da muke ganin kamar an samu sauki ta wajen musamman kudancin Borno. Ga shi kuma ya sake tasowa,'' in ji shi.

Da aka tambaye shi ko babu jami'an tsaro ne a yanzkin da har aka samu komawar hare-hare sai ya ce akwai su amma ba su da yawa.

''Kamar a wajenmu akwai jami'an tsaro, inda jami'an za su ajiye dakaru daga safe suna sintiri, manoma kuma suna aiki a gonakinsu to amma akan samu matsala don ba su da yawa, saboda sojojin ba za su iya gaba daya ba.'' Ya ce.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ya ce jami'an tsaron ba su da yawan da za su iya zuwa da bayar da tsaro a dukkanin inda manoma suke zuwa aiki ba.

Ndume ya kara da cewa, '''akwai kuma wadansu manoman da suke ketare iyaka. Idan an ce kar su je fiye da kilomiya 3 ko 4 ko 5 daga hanya don sojoji su samu su yi sintiri suna ganin abin da yake tafiya to a irin wadannan lokuta da yawa daga ciki suke tsallaka wannan iyaka su kuma Boko Haram ta wajen ne kamar hanyarsu take.''

Ya ce ta nan suke kaiwa suna komawa to shi ne inda ake samun matsalar.

Dangane da girman wannan matsala ta sake bullowar barazanar kungiyar ta Boko Haram a yanzu sai Sanatan ya ce: ''Barazanar Boko haram dai ta yi sauki tsakani da Allah ana samun nasara, amma har yanzu gaskiyar magana ita ce sojojinmu ba su da isassun kayan yaki da za su tunkari wannan matsala da ke gabanmu.''

Ya kara da cewa,'' idan yanzu da a ce muna da jiragen sama masu saukar ungulu na yaki a Maiduguri a zaune dindindin kamar guda biyar wadanda suke zaune a nan kodayaushe to za su iya aiki a Borno da Yobe har ma cikin Adamawa da sauransu.

In an ce an samu irin wadannan jirage na yaki a Zamfara ko Sokoto za su iya biyan bukata a yankin arewa maso yamma.

''Amma gaskiyar magana ita ce ya kamata gwamnati ta bayar da fifiko a kan tsaro da walwalar jama'a wanda wannan shi ne dalilin gwamnati.'' In ji Sanatan.