Yadda ƙungiyar IS ta mayar da hankalinta kan Afirka

Hoton mayaƙan IS daga reshenta na Sahel inda take iƙirarin kai hari Nijar a watan Yuni

Asalin hoton, ISLAMIC STATE

Bayanan hoto, Wani hoton mayaƙan IS daga reshenta na Sahel inda take iƙirarin kai hari Nijar a watan Yuni
Lokacin karatu: Minti 5

Sakamakon koma-baya da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS ta gamu da shi aka fatattake ta da kusan a ce an kusa mantawa da ita a sassan duniya ga dukkan alamu ƙungiyar ta mayar da hankalinta tare da karkata ga ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara.

A baya ISIS ta shahara a yankin Gabas ta Tsakiya da Afghanistan.

A yanzu ƙungiyar na gudanar da ayyukanta da yaɗa farfagandar nuna cewa har yanzu ita barazana ce ga duniya.

Yayin da aka cika shekara 11 da ƙaddamar da Daular Islama da ƙungiyar ta yi - ranar 29 ga watan Yuni, a yanzu kusan kashi 90 cikin ɗari na hare-haren da ƙungiyar ke iƙirarin kaiwa a duniya a Afirka take yi, wanda hakan ya ƙaru daga kashi 70 cikin ɗari a shekarar da ta wuce.

Ƙungiyar na amfanin da hare-haren da take iƙirarin kai wa daga reshenta na Najeriya da yankin Tafkin Chadi (ISWAP), da reshen yankin Sahel da Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo (ISCAP), da kuma na Mozambique da Somalia, wajen yaɗa farfagandarta.

A wata shida na farkon wannan shekara an samu ɓullar wata ƙungiyar ta masu iƙirarin jihadi a Najeriya.

Sannan kwatsam an ga ƙaruwar ayyukan reshen ƙungiyar na Somalia abin da a baya ya lafa.

Hakazalika ba tsammani an ga yadda ta yi kutse a gandun dajin Mozambique, da kuma yadda take kai hare-hare munana kodayake jifa-jifa a yankin Sahel.

Sai dai ƙungiyar IS ta kuma gamu da cikas a nahiyar ta Afirka, inda aka ga raguwar ayyukanta da kuma yawan mutanen da hare-harenta ke shafa a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, tare da kuma da gaza ɗorewar ayyukanta a wasu yankunan kamr Sahel da Mozambique, duk da bugun ƙirji da takan yi a wasu lokuta na tayar da zaune tsaye.

Afirka ta zama dandalin farfagandar IS

Hare-haren reshen IS na Afirka shi ne kashi 90 cikin ɗari na ayyukanta a duniya
Bayanan hoto, Hare-haren reshen IS na Afirka shi ne kashi 90 cikin ɗari na ayyukanta a duniya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Miyagun hare-haren da rassan ƙungiyar ke tunƙaho da kaiwa kusan kodayaushe a yanzu su ke mamaye jaridar mako-mako ta ƙungiyar, al-Naba.

Hotunan bidiyon farfaganda guda uku na baya-bayan nan dukkaninsu sun fito ne daga rassanta na Afirka - biyu daga Najeria.

Saɓanin haka kuma rassan ƙungiyar waɗanda ba na Afirka ba kusan a ce babu wasu ayyuka da ake ganin sun yi da za su ɗauki hankali, kama daga bayanai da ɗaukan mayaƙa ko kuma fitar da hotunan bidiyo.

Daga bugun jaridar ƙungiyar al-Naba guda 25 da ta fitar a wannan shekarar, dukkanin labaran da suka kasance a shafin farko in banda ɗaya duka na Afirka ne.

Reshen ƙungiyar na Najeriya - ISWAP shi ne kan gaba da labari 16, sai kuma reshenta na Somalia da guda bakwai sai kuma guda ɗaya daga Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo ISCAP, abin da ke nuna raguwar ayyukan ƙungiyar daga wannan reshe.

A babban sharhin jaridar ta al-Naba ta watan Mayu - wadda yanzu ita ce babbar kafar yaɗa farfaganda ta ƙungiyar zuwa ga mabiyanta da kuma masu yaƙi da ita - a yanzu IS ta sake fitowa tana alfahari da nahiyar Afirka a matsayin babbar cibiyarta ta ƙaddamar da abin da ta kira jihadi.

Ta yaba wa mayaƙanta na nahiyar Afirka, yayin da ta yi gum a kan mayaƙanta na ƙasashen Larabawa Musulmi, waɗanda kusan take ɗora wa alhakin dakushewarta a yankin, inda take nuna cewa ba su dakishi da jajircewar da ake buƙata wajen jihadi, kuma masu miƙa wuya ne ga gwamnatocin ƙasashensu.

A bara lokacin da ƙungiyar ta cika shekara goma da kafa Daularta ta Musulunci, shugabancin ƙungiyar ta bayyana cewa rassanta na Afirka ne suke samun ƙwararrun mayaƙa, tare da kiran ci gaba da samo mayaƙan - kodayake sai a baya-bayan nan aka fara ganin alamun waɗannan sababbin mayaƙa daga kafofin IS ɗin.

Ana ganin jaridar ta al-Naba ta mayar da hankalinta ne a kan Afirka saboda a watan Afirilu an yi raɗe-raɗin cewa magoya bayan IS da ba sa jin daɗin jaridar na shirin kafa wata sabuwa da za ta kasance kishiya a gareta, saboda a wajensu jaridar na kawar da kanta daga yankin Gabas ta Tsakiya.

To sai dai kuma fa ba za a iya cewa komai na tafiya daidai ba a harkar farfagandar ta IS a Afirka.

A lokacin watan Ramadan da kuma lokacin Sallah Ƙarama da kuma Babbar Sallah, duka a waɗannan lokuta uku ba a ga irin abubuwan yaɗa labarai na farfaganda na ƙungiyar ba da take tunƙaho da su, sosai.

Mayakan ƙasashen waje

Babban abin ɗaukar hankali na ayyukan IS a Afirka ya bayyana ne a ƙarshe-ƙarshen watan Disamba, lokacin da ƙungiyar ta bayyana samun wasu mayaƙa na ƙasashen wajen a rassanta na Najeriya (ISWAP) da Somalia.

A wannan watan IS ta saki wani hoton bidiyo na farfaganda da ke nuna hannun masu bai wa mayaƙan ƙungiyar horo da kuma mayaƙa duka 'yan yankin Gabas ta Tsakiya.

Wani hoton bidiyo da ke nuna 'yan ƙasar waje masu bai wa mayaƙan IS horo a Najeriya

Asalin hoton, ISWAP

Bayanan hoto, Wani hoton bidiyo da ke nuna 'yan ƙasar waje masu bai wa mayaƙan IS horo a Najeriya (ISWAP)

Ƙungiyar ta ma nuna yadda take da tasirin mayaƙan waje sosai a reshenta na Somalia, inda ta nuna wani hoto na mayaƙa 13 da tace daga ƙasashe bakwai suke

(Saudi Arabia, Libya, Yemen, Tunisia, Morocco, Ethiopia, da Tanzania) - inda ta yi iƙirarin cewa yawancinsu sun ƙaddamar da harin ƙunar-baƙin-wake a lokacin da aka kai wa jami'an tsaron yankin Puntland, ranar 31 ga watan Disamba.

Sababbin hare-hare a Najeriya

Reshen ƙungiyar IS a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma yankin Tafkin Chadi wato ISWAP, ya kasance mafi tasiri a tsakanin dukkanin rassan ƙungiyar na duniya a yawan hare-hare da kuma tasirin harin.

Labarai da hotunan farfaganda na hare-haren da ISWAP ɗin ta riƙa kai wa sansanoni da barikin soji masu tsaro sosai a arewa maso gabas kusan a ce su ne gaba a farfagandar ƙungiyar a duniya.

A watannin nan ƙungiyar ta yi iƙirarin kai irin waɗannan hare-hare sansanonin soji inda ta ke cewa ta hallaka sojoji da dama tare da yin awon-gaba da makamai da za ta yi amfani da su nan gaba, kuma a lokaci da dama sai ma ta lalata sansanin kafin ta fice.

A ɓangaren fitar da saƙonni ƙungiyar ta wallafa sharhi biyu na jaridarta ta al-Naba, inda ta ayyana wannan ƙuduri nata na hari a matsayin nasara da kuma gazawar waɗannan sansanonin soji na Najeriya da ake tunƙaho da su.

Hotunan waɗannan hare-hare sun riƙa mamaye shafin farko na jaridar ƙungiyar a shekarar nan.

Haka kuma ISWAP ta bayar da rahoton ƙaruwar hare-harenta a kan fararen hula a wannan shekara, inda ta kai wani mummunan hari ranar 28 ga watan Afirilu, inda a lokacin ta ce ta kashe farar hula sama da 20 a kusa da garin Chibok.

Bayan wannan IS ta yi iƙirarin ƙona coci-coci da gidajen Kiristoci a wasu jerin hare-hare a shekaran nan, inda yawanci take fitar da hotuna da ke tabbatar da iƙirarinta.

Yayin da aka san cewa kai hari a kan Kiristoci abu ne da ƙungiyar IS ta yi fice da shi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Mozambique, to amma ba a san haka ba a Najeriya inda galibi ƙungiyar ke kai hari kan barikin da sansanonin soji.

Ba a san dalilin yawan kai hare-haren kan Kiristoci ba a wannan lokacin a Najeriya.

A wani lokacin IS na cewa ta kai harin ne sabodata tana zargin Kiristocin da haɗa kai da sojoji a yaƙi da su.