'Rayuwarmu na cike da tsoro' – masu noma a kusa da Boko Haram

A farmer at a Boko Haram frontline

Asalin hoton, Ayo Bello/BBC

    • Marubuci, Ijeoma Ndukwe
    • Aiko rahoto daga, Rahoto daga jihar Borno
  • Lokacin karatu: Minti 5

Yayin da mata ke bai wa lambunansu ruwa, suna tumɓuke ciyayi a wata kusurwar karkara da ke arewa maso gabashin Najeriya, jami'an tsaro masu kayan sarki na tsaye ƙiƙam suna gadinsu a kusa riƙe da zungura-zungura bindigogi.

Su ne jami'an tsare dazuka – wani sashen jami'an tsaro na musamman da gwamnati ta kafa don kare manoma daga 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi kamar Boko Haram da Iswap, waɗanda na iya kawo farmaki a gonaki cikin kowanne lokaci.

"Akwai fargaba – rayuwarmu na cike da tsoro," kamar yadda Aisha Isa 'yar shekara 50 ta faɗa wa BBC lokacin da take kula da amfanin gonarta.

Saboda rayukan mutanen gidansu na cikin hatsari idan suka ci gaba da zama a mahaifarsu, ala dole suka yi gudun hijira shekara 11 da ta wuce.

Da sanyin safiya, motar fikof na kwaso su, ita da sauran wasu takwarorinta daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno zuwa ƙauyen Dalwa.

Tafiya ce mai nisan ƙasa da awa ɗaya.

Yanzu tana zaune ne a wani matsugunnin wucin gadi kuma noman wake da masara, shi ne kawai hanyar da ta rage mata don ciyar da 'ya'yanta, kamar yadda ta ce.

"Za mu yi kasada mu zo ko jami'an tsaron daji ba su zo ba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A nan sojoji sun shata wata doguwar iyaka, zagaye da wani fayyataccen gwalalo, a ciki ne mutane suke iya shuka amfanin gonakinsu. Matuƙar suka tari aradu da ka, suka tsallaka iyakar, barazanar gamuwa da Boko Haram ta daɗa girma.

"Muna jin labarai na yadda ake sace mutane," cewar Mustapha Musa, ɗan shekara 42.

"Wasu an kashe su. Abin da ya sa nake jin tsoro kenan kuma ba na son na zo idan kariyar jami'an tsaro."

Magidancin kuma mahaifin 'ya'ya 10 ya ce ya bar ƙauyensu, Konduga ne, shekara 13 sannan ba zai iya komawa can ba har sai gwamnati ta tabbatar da tsaro mai ɗorewa.

A cikin shekara 15 tun bayan fara rikicin 'yan ta-da-ƙayar-baya a arewa maso gabas, an kashe dubban mutane, sannan an tursasa wa miliyoyi tserewa gidajensu.

Yawan mutanen da aka kashe a hare-haren da aka kai wa manoma bana ya ninka biyu tun daga shekara ta 2024 a cewar binciken wata ƙungiya mai bibiyar wuraren da ke fama da rikice-rikice (Acled).

Duk da haka, gwamnan jihar Borno yana hanzarta aikin sake mayar da mutanen da rikici ya raba da gidajensu daga sansanonin 'yan gudun hijira – a wani ɓangare na shirin daidaita al'amura, da kuma tunkarar katsewar da aka samu a harkokin samar da abinci.

Agro ranger

Asalin hoton, Ayo Bello/BBC

Bayanan hoto, Gwamnatin Najeriya ta ce tana da niyyar faɗaɗa rundunar jami'an tsaron daji

Mutane kusan miliyan huɗu ne ke fuskantar yunwa a faɗin yankunan da ke fama da rikici na arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗi. Sai dai wasu hukumomin ba da agaji sun ce shirin mayar da mutane garuruwansu yana gaggawa.

Wata ƙungiya da ake kira, International Crisis Group, mai aiki don warware miyagun rikice-rikice ta ce manufar, na sanya mutanen da rikici ya raba da gidajensu a hatsari - ta nunar cewa 'yan ta-da-ƙayar-baya na tatsar manoma a yankunan da suke iko da su ta hanyar tara kuɗi don ayyukan tsaurin ra'ayi.

Abba Mustapha Muhammed wanda aka sace tare da sauran manoma tara kuma har yanzu yana cike da firgici da daɗewa bayan faruwar mummunan lamarin, shi ganau ne ba jiyau ba na abubuwan da kan faru idan waɗanda aka sace ba su biya kuɗin fansa ba.

"Akwai mutumin da aka kashe saboda ya kasa biyan kuɗin fansa. Danginsa ba su iya kai kuɗin a kan lokacin da aka ba su ba," cewar Abba Muhammed. "An kashe shi sannan aka jefar da shi. Kuma suka nemi dangin mamacin su je su ɗauki gawa."

Group of women going to the farms

Asalin hoton, Ayo Bello/BBC

Tsarewar da aka yi masa a cikin ruƙuƙin daji tsawon kwana uku lamari ne "mai cike da baƙar wahala", in ji shi. "Ɗan ƙanƙanin abincin da akasari suke bai wa mutum ba ya kashe yunwa, kuma yana sa gudawa. Sannan babu tsaftataccen ruwan sha."

Mahaifin 'ya'ya ukun ya faɗa wa BBC cewa yana jin tsoro sosai ya koma noma ɗan abin da zai ci saboda "'yan ta-da-ƙayar-baya har yanzu suna nan a laɓe. A jiyan nan ma, sun sace fiye da mutum goma".

Duk da labarai irin waɗannan, Mohammed Hassan Agalama, kwamandan rundunar jami'an tsaron daji a Borno, ya dage a kan cewa jami'an tsaron sun hana 'yan ta-da-ƙayar-baya ƙaddamar da miyagun hare-hare.

"Ba mu ga ƙarin 'yan ta'adda suna zuwa kawo wa manoma hari ba saboda sun san cewa muna nan a kusa duk lokacin damuna," cewar Kwamanda Agalama, da ke aikin ƙarƙashin hukumar tsaron farar hula ta Najeriya (NSCDC).

James Bulus, wani mai magana da yawun hukumar, ya ƙara faɗa wa BBC cewa gwamnati na samun nasara a yaƙin da take yi da 'yan ta-da-ƙayar-baya: "Noman nan kawai zai nuna muku cewa al'amura sun koma daidai, kuma manoma na yin harkokinsu kamar yadda suka saba a gonaki."

Sai dai ya amsa cewa ba shakka ma'aikata ba za su iya wadata ba.

Jami'an tsaron dazuka, wani ɗan ƙaramin shiri ne kuma ba masalaha ta dogon lokaci ba ce ga taɓarɓarewar tsaro a faɗin yankin.

"Ba za mu iya kasancewa a ko'ina ba. Mu ba aljanu ba ne. Zai yiwu ne a ce jami'an tsaron daji 600, su kasance a duk gonakin Borno? Ba zai yiwu ba."

A haka ne, gwamnatin tarayya Najeriya ta ce tana da shiriin faɗaɗa shirin jami'an tsaron dazuka.

Babban mai sharhi kan harkokin Afirka a ƙungiyar Acled, Ladd Serwat ya ce bana an ga ƙaruwar hare-haren da 'yan ta-da-ƙayar-baya ke kai wa fararen hula a gonakin jihar Borno.

Bugu da ƙari, a rabin farkon wannan shekara ta 2025, kashe-kashen Boko Haram da Iswap da aka ba da rahoto sun kai yawan da ba a gani ba cikin shekara biyar.