An kashe gwamnan jihar Darfur ta Yamma a Sudan

Asalin hoton, AFP
Hukumomi a Sudan, sun ce dakarun kungiyar kar-ta-kwana na RSF da ke yaki da rundunar sojin kasar sun kashe gwamnan yammacin yankin Darfur.
Daman kafin kisan nasa, Khamis Abbakar, ya zargi mayakan na RSF da kuma kungiyoyin 'yan bindigar da ke kawance da su da aikata kisan kiyashi a kan 'yan kabilarsa.
Gwamnan ya yi gargadin cewa hare-haren da ake kaiwa sun bazu zuwa birnin inda ya nemi daukin kasashen duniya.
A cikin daren da ya gabata ne mayakan na Rapid Support Forces, RSF, da ke fafata yaki da sojin kasar ta Sudan, hadaka da wasu kungiyoyin mayakan sa-kai jami’an Sudan su ka ce sun hallaka gwamnan na Yammacin Darfur a babban birnin yankin,El Geneina.
Daman ‘yan sa’o’i kafin ya gamu da ajalin nasa a wata hira da aka yi da shi ta talabijin gwamnan ya zargi mayakan na RSF da abokansu da laifin kai hare-hare kan kabilarsa ta Masalit.
Lamarin da ya sa har ya nemi kasashe da hukumomin duniya su shiga tsakani kan ta’asar da ya ce ana yi wa jama’arsa.
Yanzu rikici ya barke a biranen Nyala da Zalingei.
Masu raji sun ce sama da mutum dubu daya aka kashe tun bayan da rikicin ya barke a tsakiyar watan Afirilu a birnin El Geneina, wato babban birnin jihar ta West Darfur din.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A daya bangaren rikicin kuma sama da mutum dubu biyu ne fadan da ake yi tsakanin dakarun kungiyar ta RSF da sojan Sudan ya raba da muhallinsu.
Kuma da dama daga cikin wadanda suka tseren sun fice daga kasar.
Ranar Laraba majalisar dinkin duniya rikicin na Sudan ya raba mutum sama da miliyan biyu da muhallinsu , kuma hare-haren da ke fadada zuwa Darfur ka iya zama laifuka na cin zarafin bil’Adama.
Darfur yanki ne da aka tafka yaki na kisan kiyashi a farkon shekarun 2000, a lokacin da kabilu 'yan Afirka suka yi tawaye suna zargin gwamnatin Sudan da Larabawa suka mamaye da nuna musu wariya.
An zargi gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Omar al-Bashir da ramuwa ta hanyar bayar da makamai ga kungiyar mayaka ta wasu kabilun Larabawa, makiyaya da ake kira Janjaweed, inda mayakan suka rika harar fararen hula.
Rikicin ya tarwatsa miliyoyin mutane a yankin inda aka yi kiyasin mayakan na Janjaweed sun kashe mutum kusan dubu 300.
Daga baya mayakan na Janjaweed suka rikide da sahalewar gwamnatin Sudan zuwa kungiyar RSF a 2017, inda ta zama wani reshe na jami'an tsaro na kasar.
A wata sanarwa da kungiyar ta RSF ta fitar ta ce fadan na El-Geneina na kabilanci ne, tana mai zargin tsohuwar gwamnatin kasar da rura wutarsa.
Ta ce tana fafutukar ganin an kai wa birnin kayan agaji.











