Zaɓi mai tsauri da masu shiga tsakani ke da shi a rikicin Sudan

Asalin hoton, AFP
Yayin da Khartoum na Sudan ya sauya daga birni mai cike da kwanciyar hankali zuwa wani filin daga, Saudiyya da Amurka sun gayyaci ɓangarorin da ba sa ga maciji da juna zuwa Jeddah.
Za su je ne domin tattaunawa kan yadda za a tsagaita wuta.
Sai dai ƙwararru irinsu Alex de Waal na cewa, wannan mataki na wucin-gadi ne kawai, domin cimma buƙatar gaggawa.
Masu shiga tsakani na cikin tsaka mai wuya: duk shawarar da suka yanke kan tsari da jadawalin tattaunawar gaggawa ita ce za ta tabbatar da hanyar da za a bi wajen samar da zaman lafiya a Sudan.
Don tsagaita rugugin bindigogi, jami'an diflomasiyyar Amurka da na Saudiyya za su yi magana da wakilai gudu uku-uku na janar-janar ɗin da ke yaƙi da juna a Sudan yayin tattaunawar ta birnin Jeddah.
Manufar tattaunawar, ita ce a cimma tsagaita wuta don ayyukan jin ƙai. Wata dabara da hanyoyin da za a riƙa bibiya don kai kayan agaji. Babu ɓangaren da ke son fara tattaunawa don cimma yarjejeniya kan yadda shugabancin ƙasar zai kasance.
Jam'iyyun fararen hula da kwamitocin unguwanni masu nuna turjiya, waɗanda zanga-zangarsu ta lumana ta yi awon gaba da mulkin tsohon shugaban kama-karya, Omar al-Bashir shekara hudu da suka gabata, za su kasance 'yan kallo a tattaunawar.
Ba abu ne mai sauƙi ba, a iya shawo kan ɓangarorin manyan sojojin su amince da kowacce irin yarjejeniyar tsagaita wuta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Babban hafsan sojojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, zai dage kan cewa shi ne yake wakiltar halastacciyar gwamnati. Zai ayyana Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda aka fi sani da ''Hemedti'', a matsayin ɗan tawaye.
Amma Hemedti, wanda shi ne mataimakinsa kafin fara tafka wannan rikici, zai buƙaci a bai wa kowanne ɓangare matsayi iri ɗaya.
Zai so kowa ya dakata a inda yake, wato dai mayaƙansa na rundunar RSF su ci gaba da iko da mafi yawan sassan birnin Khartoum. Janar Burhan zai bukaci kowa ya koma matsayinsa na baya kafin a fara gwabza yaƙi.
Samun wani sassauci na nufin sasantawa mai tsauri da janar-janar ɗin biyu.
Masu shiga tsakani na bukatar samun yarda da tabbacinsu, cewa idan suka yi sassauci yanzu, to hakan ba zai jefa su cikin kasada da hatsari ba.
Wani hanzari ba gudu ba kuma, shi ne ɓangarorin da ke faɗa da junan za su buƙaci taka wata muhimmiyar rawa a tattaunawar kafa shugabanci da kuma manufar da za ta dace da muradansu.
Wani abu da Burhan da Hemedti - da ma maƙwabtan ƙasar Larabawa - suka amince cewa ba sa so, shi ne gwamnatin dimokraɗiyya, wadda ake ta jujjuyawa tun kafin ɓarkewar faɗan.
Sojojin su biyu, su ne suka riƙa tafiyar da mulkin ƙasar tun shekara ta 2019, bayan hamɓaras da al-Bashir, inda suka ƙi amincewa su miƙa iko hannun fararen hula.

Asalin hoton, AFP
Wani ɓangare na yarjejeniyar shi ne yin afuwa kan laifukan yaƙi.
Tattaunawar da manyan janar-janar ɗin suka mamaye mai yiwuwa ne ta kawo ƙarshe da wata yarjejeniyar zaman lafiya, wadda za ta ba da damar raba ganima abin da kuma zai sake mayar da hannun agogon baya game da yiwuwar kafa gwamnatin dimokraɗiyya tsawon ƙarin shekaru.
Amma idan ba a dakatar da yaƙin ba, Sudan na fuskantar barazanar rugujewa a matsayinta na ƙasa.
Abdalla Hamdok - Firaminista gwamnatin hadaka ta soji da fararen hula da janar-janar ɗin suka hamɓaras a 2021 - ya ce barazanar da sabon yaƙin ke da ita ta fi girman abin da aka gani a Syria da Yemen.
Yana ma iya ƙarawa da cewa, girman rikicin sai ya zarce na Darfur.
Tura ƙarin dakaru fagen daga
Akwai mummunan hasashe game da yadda yaƙe-yaƙen basasar Sudan ke wakana.
A kwanakin farko, kwamandojin soji - janar-janar na soji da shugabanni 'yan tawaye - sukan cimma ƙuduri cikin fushi su yi wa abokin gabarsu bugun da ba zai iya tashi ba.
Rikici yakan rincaɓe yayin da kowanne ɓangare ke kai hare-harensa, abu ne mai sauƙi a iya gane wane ne ke wannan ɓangare ko wancan - da kuma wane ne yake matsayin ɗan ba-ruwanmu.

Asalin hoton, AFP
Mun shaida hakan lokacin da yaƙin basasa na 1983 a Sudan, mun kuma sake ganin haka shekara 20 bayan nan a Darfur, da kuma rikice-rikicen tsaunukan Abyei da Heglig da kuma Nuba kusa da iyakar arewa zuwa kudanci lokacin da Sudan ta Kudu ta ɓalle a 2011.
Faɗace-faɗacen farko a yaƙin basasar Sudan ta Kudu na 2013 su ma da irin haka suka faro.
A ranar 15 ga watan Afrilu, lokacin da faɗa ya kaure tsakanin sojoji da rundunar RSF, kowanne ɓangare ya lashi takobin rusa ɗaya ɓangaren.
Sun mayar da hankali wajen buɗe wuta kan wurare masu muhimmanci na abokan faɗansu a babban birnin ƙasar, ba tare da la'akari da ɗumbin ɓarnar da za su haddasa wa birnin da mazaunansa ba.
Tarihin rikice-rikicen baya ya nuna cewa idan ba a gaggauta daƙile wannan yaƙi ba, to zai ci gaba da ƙazancewa.
Kowanne ɓangare na tura ƙarin dakarun fagen daga, a ƙoƙarin ganin ya ja ra'ayin ƙungiyoyin yankuna masu makamai waɗanda zuwa yanzu ba su shiga yaƙin ba, tare da neman taimakon abokan ƙawance na ƙasashen waje masu goyon baya.
Yanzu muna cikin wannan zango.
Yanayin rikice-rikicen da aka saba gani a Sudan, na nuna cewa abokan gabar ba za su iya ɗorewa tsawon lokaci ba, Makamai da kuɗaɗe da sauran hidimomi za su fara yanke musu, abin da zai sanya su shiga yarjejeniyoyi da wasu ɓangarori, don samun ƙari.
Daga na za a fara ganin ɓarakar da ke cikin kowanne ƙawancen abokan yaƙi. Sauran ƙungiyoyi masu makamaki su ma za su shigo fagen faɗan.
Al'ummomin yankuna za su ɗauki makamai don kare kansu. Su ma 'yan ƙasashen waje za a zargo su ciki. Tuni waɗannan al'amura sun fara faruwa. Lamarin ya fi ƙamari a Darfur, mahaifar Hemedti, wadda tuni ta sake kamawa da wuta.
Har yanzu, ba mu ga fararen hula cikin wani tsararren al'amari ana kai musu hari saboda ƙabilarsu ba.
Amma akwai babban hatsarin faruwar hakan, kuma da zarar mayaƙan kowanne ɓangare sun tafka gagarumar aika-aika, gaba za ta ƙara ruruwa.
Abu na gaba shi ne rikici ya faɗaɗa zuwa sassan ƙasar, abin da zai riƙa iza rigingimu tsakanin garuruwa da al'ummomi a lokacin da yake bazuwa.
Ƙungiyoyi masu makamai za su rarrabu sannan su tattaru, za a ga faɗa a kan iko da wurare masu maiƙo kamar tituna da filayen jiragen sama da mahaƙar zinare da cibiyoyin raba kayan agaji.
A Darfur, bayan ƙazamin yaƙi da kisan kiyashin 2003 zuwa 2004, sai yankin ya auka cikin yanayi irin na zaman kara-zube.
Shugaban jami'an kwantar da zaman lafiya na haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya da Tarayyar Afirka ya bayyana lamarin da "wani yaƙi da kowa yake yaƙar kowa".
Wannan ne yanayin fage mai cike da rashin doka da Hemedti ya girma ya gawurta, ta hanyar amfani da kuɗi da tarzoma wajen gina tungar ikonsa.
Akwai yanayi mai yawa wanda ɗaukacin Sudan ta zo tana kamanceceniya da Darfur.
'Juya-baya a lokacin da ake da bukata'
Masu shiga tsakani na Amurka da Saudiyya na kokarin ganin ba su ɗau ɓangare ba.
Ba kamar sauran ƙasahen Larabawa ba - inda Masar ke goyon bayan Burhan, sannan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na goyon bayan Hemedti - Sudiyya ba ta da gwani.
Amurka na barazanar sanya takunkumi. Ba lallai ne hakan ya yi wani tasiri ga janar-janar ɗin ba - Sudan na fama da takunkuman Amurka tun cikin 1989, kuma harkokin kasuwancin sojoji na ci gaba da garawa duk da haka.

Asalin hoton, Getty Images
Matsin lamba da zai yi tasiri na nufin haɗin-kan ƙasashen duniya. Kowa - ciki har da China da Rasha - su amince cewa wannan yaƙi babban bala'i ne.
Jami'ai a Majalisar Dinkin Duniya sun ɗora alhaki kan mambobin ƙasashen Afirka, su shigar da batun a gaban kwamitin tsaro na MDD.
Kawo yanzu, ba su ce komai a kan wannan batu ba.
Tarayyar Afirka ta gudanar da taro ta hanyar kwamitin tsaro da zaman lafiya kwana guda da fara rikicin, inda suka buƙaci a tsagaita wuta, amma ba ta cikin masu shiga tsakanin na Jeddah wato Amurka da Saudiyya.
A yanzu, kowacce rana da ke fitowa ta koma ga Ubangijinta na sake zama barazana da fargaba ga makomar yaƙin.
Daƙile wannan rikici abu ne mai wahalar gaske.
Saboda turjiyar da kowanne ɓangare ke nunawa na ganin ya yi tasiri ko nasara a wannan yaƙi.
Amma wani abu da ba za a iya kaucewa ba shi ne, wannan gumurzu ana yin sa ne domin birnin Khartoum.
An shiga yanayi na tsaka mai wuya ganin bukatar agajin gaggawa a kowanne ɓangare na kasar da ƙaruwar yunwa.
Fararen hula sun maƙale a ƙasashen da suka nemi mafaka, sannan waɗanda ke ƙasar na fama da katsewar lantarki da ruwan sha da hanyoyin sadarwa, ga kuma ƙarancin abinci.
Kuma suna cikin tsananin buƙatar kuɗi.

Asalin hoton, Reuters
'Yan Sudan na ganin ƙasashen duniya sun yi watsi da su a daidai lokacin da suke cikin wahala, da taimakon ɗaiɗaikunsu ne fararen-hula ke samun kafar shiga da kayan agaji.
Akwai barazana cewa yunwa za ta kasance makamin yaƙi, sannan batun agaji zai kasance abin da jagororin yaƙin za su ci karensu babu babbaka da shi.
Ƙungiyoyin ba da agaji za su buƙaci amfani da hanyar bayan fage wajen isa ga fararen-hula.
Babu maslaha kan daƙile ta'azzarar rikicin. Al'amura na iya rincaɓewa nan gaba kaɗan.
Kuma da alama duk shawarar da aka yanke a tattaunawar neman tsagaita wuta - wa ake wakilta, bisa wanne sharaɗi kuma a kan wacce manufa - waɗannan duka na iya sauya makomar ƙasar tsawon shekaru masu zuwa.
Alex de Waal shi ne shugaban gidauniyar zaman lafiya ta duniya a kwalejin nazarin shari'a da harkokin diflomasiyya ta Fletcher da ke jami'ar Tufts ta Amurka.











