Tinubu ya isa jihar Benue domin ganewa idanunsa abin da ya faru

Asalin hoton, Presidency
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya isa jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya a wata ziyara da yake yi bayan wasu kashe-kashe da aka samu a wasu yankunan jihar.
Rahotonni sun ce fiye da mutum 200 aka kashe a hare-haren bayan-bayan nan da wasu masu ɗauke da makamai suka ƙaddamar.
Wannan ne karo na farko da shugaban ke ziyartar mutanen da ke fama da tashen-tashen hankula a jihar.
Masu suka na zargin shugaban da kasa kare al'ummar ƙasar, yayin da ake samun ƙaruwar rikice-rikice a wasu sannan ƙasar.
An dai sha alaƙanta rikicin da addini da ƙabilanci, to amma ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International a Najeriya ta ce rikicin jihar ba shi da alaƙa da addini.
Ta yaya ziyarar za ta yi tasiri?
Shugaba Tinubu dai ya ce zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar, da suka haɗa da sarakunan gargajiya da ƴansiyasa da jagororin addini da shugabannin al'umma da ƙungiyoyin matasa, da nufin lalubo hanyoyin magance rikicin jihar.
Barista Bulama Bukarti wanda masanin harkar tsaro ne a yankin Sahel ya ce ziyarar shugaba Tinubu zuwa Benue na da matuƙar tasiri.
"Wannan ziyara abu ne mai kyau domin hakan na nuna cewa koke-koken da al'umma ke yi sun shiga kunnensa. Kuma hakan na nufin shi shugaban ƙasar ya ɗauki al'amarin da muhimmanci." In ji Tinubu.
To sai dai barrister Bukarti ya ce tasirin ziyarar zai dogara ne kan yin abun da ya dace a lokacin ziyarar da bayan ziyarar.
"Bai kamata a tsaya daga gidan gwamnati ba. Abin da ya kamata a yi shi ne tawagar shugaban ƙasa su yi ƙafa da ƙafa zuwa wurin da al'amarin ya faru sannan kuma a ƙyale mutanen da ke cikin damuwa domin bayyana masa halin da suke ciki. Hakan ne zai sa shugaban ƙasa ya fahimci ina matsalar take.
Idan ma akwai yiwuwa to ya kamata shugaban ya kai ziyara zuwa maƙabartar da aka binne mutanen da aka kashe ko kuma ɗakin ajiyar gawa domin ganin gawarwakinsu." In ji barista Bulama Bukarti.
Hanyoyin warware rikicin Benue
Barista Bulama Bukarti ya ce matsalar Najeriya ita ce a duk lokacin da aka samu rikici irin wannan akan tsara shugaba ya kai ziyara amma kuma daga nan shi kenan ba tare da ɗaukar wani matakin da zai daƙile sake faruwar rikicin a gaba ba.
"Wani lokacin za ka abin ya zama kamar biki an zo da makaɗa da mawaka maimakon kai ziyarar ta'aziyya kuma daga nan shi kenan babu wani abun da zai biyo baya."
Masanin ya ce abin da zai biyo bayan ziyarar shi ne zai sa a gane ko za a ɗauki hanyar warware matsalar ko kuma a'a.
Barista Bulama ya kuma lissafa hanyoyin warware irin wannan rikici guda biyar.
- Daukar matakan yanzu-yanzu: Ɗaya daga cikin hanyoyin warware irin waɗannan rikice-rikice tsakanin al'umma sun haɗa da ajiye jami'an tsaro tare da ba su kayan aiki nan take.
- Matakan matsakaicin zango: A kama waɗanan ake zargi sun aikata wannan laifi a gurfanar da su sannan idan an same su da laifi a hukunta su domin zama izina ga masu son kwatanta irin wannan laifi a nan gaba.
- Matakai masu dogon zango: A tabbatar da an gano matsalar da ke janyo rikice-rikice ba tare da nuna banbanci ba wanda akasin hakan ka iya bai wa ƴan ta'adda damar kutsawa su yi amfani da damar.
- Ɗaukar matakan sulhu tsakanin al'umma: Dole ne a fito da wasu matakai wajen nuna musu cewa girmama juna dole ne sannan kowa na da ƴancin yin rayuwa a kowane sashen na Najeriya.
- Aiki tare tsakanin gwamnatoci: Shugaban ƙasa da gwamnan jihar su fito da tsari kamar hukumomi da za su rinƙa haɗa hancin tsare-tsare da za su biya buƙatun al'umma domin gujewa afkuwar irin waɗannan rikice-rikice a nan gaba.











