Liverpool da Man Utd na son Bouaddi, Chelsea ta sha gaba a kan Karetsas

Hoton Ayyoub Bouaddi na tafa hannu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Liverpool da Manchester United na daga cikin manyan kungiyoyin da ke gogayyar sayen matashin dan wasan Lille da Faransa Ayyoub Bouaddi mai shekara 18. (CaughtOffside)

West Ham ta bayyana sha'awarta ta sayen dan wasan gaba na Wolves da Norway Jorgen Strand Lasen mai shekara 25 a watan Janairu. (Athletic)

Idan har raunin da dan wasan gaba na Liverpool dan Sweden Alexander Isak mai shekara 26, ya yi tsanani, watakila kungiyar ta nemi wanda za ta maye gurbinsa - inda kila ta karkata ga dan wasan gaba na gefe na Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25. (Telegraph)

Aston Villa ta bi sahun kungiyoyin da ke son sayen dan bayan Wolves da Norway David Moller Wolfe, mai shekara 23, a watan Janairu. (Football Insider)

West Ham da AC Milan sun yi nisa a tattaunawa a kan dan wasan gaba na Jamus Niclas Fullkrug mai shekara 32. (Sky Sports)

Chelsea na neman doke abokan hamayyarta na Turai wajen saye matashin danwasan tsakiya na Genk da Girka Konstantinos Karetsas mai shekara 18 (Teamtalk)

A halin da ake ciki kuma dan bayan Faransa Axel Disasi, mai shekara 27, zai bar Chelsea a watan Janairu inda kungiyoyi da yawa ke jira su ga yadda makomarsa za ta kasance. (Fabrizio Romano)

Har yanzu Tottenham ta ji wata magana ba daga Fiorentina, duk da rade-radin da aka rinka yadawa a Italiya cewa Fabio Paratici zai karbi kwantirgin shekara biyar don zama darektan wasanni na kungiyar ta Serie A. (Mail)