Zidane ko Fabregas zai maye gurbin Maresca a Chelsea, kungiya 3 ke zawarcin Dumfries

Zinedine Zidane

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zinedine Zidane
Lokacin karatu: Minti 3

Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo,mai shekara 20, yana ganin ba shi da makoma a Manchester United karkashin jagorancin Ruben Amorim kuma zai yi tunanin barin kungiyarsa ta kuruciya a watan Janairu.(Mail - subscription required), external

Manchester United da Manchester City da Liverpool da kuma Tottenham sun fara tattaunawa da dan wasan Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25 game da barinsa Bournemouth a kan fam miliyan 65 ko dayake sai ya cimma ma matsaya da Bournemouth din a watan Janairu domin su iya siyansa. (The i - subscription required), external

Manchester United ta yi ammanar cewa Semenyo zai iya karfafa bangaren hagu na kungiyar yayin da Amorim ke nuna shakku kan dan wasan Denmark Patrick Dorgu, mai shekara 21, wanda aka sayo kan fan miliyan 25 a watan Fabarairu daga Leece.(Sun), external

Bournemouth na Kallon dan wasan Tottenham da yankin Wales Brennan Johnson,mai shekara 24, a matsayin wanda zai maye gurbin Semenyo. (Teamtalk), external

Sai dai watakila, Cherries su fuskanci goggaya daga Crystal Palace, wadanda sun nuna sha'awar daukar Johnson daga Spurs. (Guardian), external

Akwai yuwuwar Barcelona zata biya fan miliyan 26 don siyan Marcus Rashford daga Manchester United inda dan wasan Ingila mai shekara 28 ya sauya salon wasansa a matsayin dan wasan aro a Sifaniya.(Mundo Deportivo - in Spanish, external)

Dan wasan Sassuolo, Armand Lauriente mai shekara 27 na gab da barin kungiyar a watan Janairu inda ake hasashen zai koma Sunderland. (Sunderland Echo), external

Real Madrid ta bayyana a matsayin kungiyar da dan wasan Al-Hilal da Portugal Ruben Neves, mai shekara 28 yake son ya koma da tamaula. (Fichajes - in Spanish), external

AC Milan na son dan wasan Brazil Thiago Silva, mai shekara 41, ya koma kungiyar a lokacin hunturu bayan ya soke kwantaraginsa da Fluminense. (ESPN), external

Kyaftin din Brighton Lewis Dunk,mai shekara 34, ya kara tsawaita kwantiraginsa da shekara guda inda zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2027.(Sky Sports, external)

Har yanzu Manchester United da Newcastle da Aston Villa na zawarcin dan wasan Inter Milan da Netherlands Denzel Dumfries, mai shekara 29. (Teamtalk), external

Barcelona ta kusa kula yarjejeniya da dan wasan old Norwich Ajay Tavares mai shekara 15 , wanda ya buga wa tawagar Ingila yan kasa da shekaru 17 (Sun), external

Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane da kocin Strasbourg Liam Rosenior da kuma kocin Como Cesc Fabregas na cikin wadanda Chelsea ke son ta dauka idan kocin kungiyar Enzo Maresca ya yanke shawarar barin Stamford Bridge. (Caught Offside, external)