Arsenal za ta ƙara wa Saka albashi, ƙila Maresca ya maye gurbin Guardiola a City

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United ta zage damtse wajen siyan dan wasan gaban Bournemouth da Ghana Antoine Semenyo a watan Janairu kuma tana ganin rashin tabbas game da makomar Pep Guardiola a Manchester City zai iya kara musu damar siyan dan wasan mai shekaru 25.(Telegraph )
Dan wasan tawagar kasar Portugal Ruben Neves, mai shekara 28, ya ki amincewa da sabon kwantiragi a kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya kuma yana son ya koma Turai kuma ana ganin hankalinsa na Manchester United .(Times )
Manchester United za ta sayar da Kobbie Mainoo, mai shekara 20 ne kawai a kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu idan ta samu tayi na musamman kuma kungiyar ta ki ba da aron dan wasan tsakiya na Ingila .(Sky Sports),
Kocin Chelsea Enzo Maresca, mai shekara 45, yana kan gaba a cikin wadanda Manchester City ke tunanin za su dauka idan kocin kungiyar Pep Guardiola dan kasar Sifaniya, mai shekara 54, ya bar kungiyar a bazara mai zuwa.(Athletic ),
Saint-Etienne ta ki amincewa da tayin farko na Yuro miliyan 8 daga Chelsea kan Djylian N'Guessan, mai shekara 17, amma za ta iya sayar da dan wasan na Faransa kan Yuro miliyan 12.5 (L'Equipe)
Hazikin dan wasan AZ Alkmaar dan kasar Holland Kees Smit, mai shekara 19, yana daya daga cikin 'yan wasan tsakiya hudu da Newcastle ke zawarci, yayin da dan wasan bayan Toulouse na Faransa Dayann Methalie, mai shekara 19, shi ma ake tunanin yana cikin jerin wadanda suke son su dauka. (Mail), external
Dan wasan tsakiya na Manchester United da Portugal Bruno Fernandes, mai shekara 31, ya saka wata bukata a kwantiraginsa da ta ba kungiyoyin da ba sa gasar Firimiya damar siyan shi kan fan miliyan 56.6.(Mail ),
Atletico Madrid na son daukar dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, wanda Manchester United ta bada shi aro ga Barcelona .(Fichajes),
Abu ne mai wuya Bayern Munich ta yi amfani da damar maida kwantaragin Nicolas Jackson daga aro zuwa na dindindin a bazara, (Bild - in German)
Bukayo Saka, mai shekara 24, zai zama dan wasa na farko a tarihin Arsenal da zai karbi albashin fam dubu 300,000 a kowane mako, inda kungiyar na dab da sanar da sabuwar yarjejeniya da dan wasan na Ingila wadda za ta kai har 2031. (Teamtalk)
Dan wasan West Ham Luis Guilherme na son ya ci gaba da taka leda a kungiyar duk da cewa rahotani sun nuna cewa dan wasan kasar Brazil mai shekara 19 zai bar kungiyar a watan Janairu . (Sky Sports), external
Kungiyar Morecambe ta National league tana son ta tsawaita aron dan wasan bayan Arsenal Maldini Kacurri, mai shekara 20, dan kasar Albania wanda ke ɗaukan hankalin kungiyoyin da suka fita kudi (Sun), external














