Roma ta gaza cimma matsaya kan Zirkzee, Barcelona na harin Torres

Asalin hoton, Reuters
Manchester United da Roma sun gaza cimma matsaya kan farashin ɗan wasa Joshua Zirkzee mai shakeru 24, inda Man United ke son siyar da shi kan fam miliyan 35, da jan ƙafa wajen amincewa da bayar da shi a masatyin aro. (Corriere dello Sport - in Italian)
Barcelona ta ƙagu ta tswaita kwantaragin ɗan wasanta Hansi Flick zuwa 2028, duk da cewar manajan ƙungiyar mai shekaru 60, ya ce zai sanya hannu ne na sabon kwantaragin zuwa 2027, a watan Mayun da ya gabata na bana. (Bild - in German)
Barcelona na duba yiwuwar ɗaukar ɗan wasan Aston Villa mai shekaru 28 Pau Torres da ɗan wasan Borussia Dortmund Nico Schlotterbeck, yayin da suke ci gaba da neman ɗan wasan baya. (ESPN)
Babban burin Chelsea shi ne samun ɗan wasan tsakiya, inda ta ke harin ƴan wasa Kobbie Mainoo, mai shekaru 20, na Manchester United da Adam Wharton, mai shekaru 21, na Crystal Palace. (Telegraph - subscription required)
Crystal Palace na neman ɗan wasan gefe, a kakar siyen ƴan wasa, bayan raunin da Daniel Munoz ya samu, da zai yi jinya ta tswaon wani ɗan lokaci. (Sky Sports)
anan sa rai ɗaya daga cikin ɗn wasan baya da Palace ke son ɗukowa daga Bayern Munich Sacha Boey mai shekaru 25, zai bar ƙungiyar a ƙarshen wata mai zuwa. (Standard)
Oliver Glasnerna Palace ya ce ɗan wasan Marc Guehi, mai shekaru 25, zai tsawaita zamansa a ƙungiyar zuwa ƙarshen kakar wasanni. (Standard)
AC Milan na tataunwa da ɗan wasan gaban Jamus Niclas Fullkrug, mai shekaru 32, daga West Ham, bayan da suka nemi a siyar musu da shi ko a basu aronsa. (Bild - in German)
Ole Gunnar Solskjaer ya shawarci Manchester United tda su ɗauko Erling Haaland, da Jude Bellingham, da Declan Rice, a lokacin da yake manaja a Old trafford, amma mai makon haka sai suka siyo Donny van de Beek, da Jadon Sancho, da Cristiano Ronaldo. (Mail - subscription required)
Da alama babu tabbaci ko Leeds United za ta kashe fam miliyan 25 wajen ɗauko ɗan wasan AC MilanSantiago Gimenez mai shekaru 24, sai dai ta na duba yiwuwar ɗauko wani sabon ɗan wasan gaba a watan Janairu a matsayin aro na gajeren lokaci. (Football Insider)
Nick Woltemade ya kasance ɗan wasan da Bayern Munich ke harin ɗauka a kakar wsannin, gabanin ya koma Newcastle United daga Stuttgart, a wata hira ya ce "Ya yi farin ciki da lamarin ya kasance a hakan".(Sport Bild, via Sky Sports Germany)
Dan wasan Newcastle United mai shekaru20, Alfie Harrison, na jan hankalin wasu ƙungiyoyi biyu da ke buga gasar Champoins. (Sky Sports)











