Me ya sa rigunan ƙungiyoyin gasar Premier ke da ɗan karen tsada?
Matsakaicin farashin kayan kungiyoyin gasar Firimiyar Ingila na manya ƴan kamfani ya ƙaru da kashi 50.7 cikin 100 a cikin shekaru goma da suka gabata. Ga kayan yara kuwa, adadin ƙarin ya kai kashi 46.8 cikin 100.
Ɗaruruwan magoya baya daga ƙungiyoyi daban-daban sun shaida wa BBC cewa tsadar rigunan ƙwallon ƙafa na tilasta musu sayen rigunan jabu.
Rabin ƙungiyoyin da ke cikin Premier League suna cajin fam 85 kan rigar maza. A sauran ƙungiyoyi 10 kuma, farashin yana farawa daga fam 60.
To me ya sa rigunan suke da tsada haka?

Asalin hoton, Getty Images
Yanayin farashin
Bisa ga binciken kasuwa da Dr Peter Rohlmann ya gudanar, wani masani kan kayan ƙwallon ƙafa, ya ce za a iya rarraba farashin rigar kungiyoyin Premier League mai farashin fam 85 kamar haka:
- Kayan dunki, aikin yin ɗunki da jigilar kaya: fam 8.50
- Talla, kuɗin lasisi da rarraba kayayyakin: fam 9.50
- Harajin VAT: fam 13.60
- Mai ƙera kayan – kamar Adidas ko Nike – yana karɓar fam16.25
- Mai sayarwa – yawanci shagon ƙungiyoyin – yana samun matsakaicin fam 37.45
Sakataren ma'aikatar Al'adu, kafofin watsa labarai da Wasanni, Nigel Huddleston, ya bayyana damuwarsa game da matsin lambar da ke kan magoya baya wajen ƙarin farashi da ke ta ƙaruwa a koda yaushe wajen sayen rigunan kungiyoyin da suke goyon naya..
"Riguna suna da muhimmiyar rawa wajen tarihin ƙungiya , amma hauhawar farashi na nufin cewa nan gaba magoya baya za su rasa kulla alaka mai mahimmanci da ƙungiyoyinsu, sannan za a tilasta musu shiga kasuwa domin sayen rigunan jabu."
Da aka tambaye shi ko ya dace a ɗauki mataki don rage farashin, Huddleston sai ya ce: "Duk da cewa farashi da sayarwa kasuwanci ne ke fayyace komai ta kowacce ƙungiya, ina fatan ƙungiyoyin za su yi la'akari da yin duk abin da za su yi don sayar da rigunansu na asali cikin sauƙin, musamman ga magoya baya yara."
A martani ga tambayar da BBC ta yi, mahukuntan gasar Premier sun nuna dokokinta, inda ta bayyana cewa ƙungiyoyin "suna da ƴancin sayarwa, talla da nuna rigunan da suka samar, domin sayarwa daga masana'antu da suka ɗunka su a duk farashin da suka zaɓa."
Shin mene ne tunanin kamfanoni?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kamfanoni sun ce suna yin bincike mai zurfi wajen ƙirƙirar kayan tamaula da yawan da ake bukata na kayan zuwa matakin ƙoli, kuma sauye-sauyen farashin yanayin kasuwa ne wanda ka iya jefa su cikin haɗari idan ba a yi taka tsantsa ba.
Rob Warner – tsohon mai ƙera kaya a Puma da Umbro – ya ce: "Ana samun banbanci daga alama zuwa wata alamar, da kuma daga mai ƙera kayan zuwa wani, saboda yawan fasaha da ake sakawa a cikin aikin.
"Yawancin ribar mai sayarwa ne ke samu, saboda suna dogaro ƙwarai da nasara ko ƙwazo ko ficen ƙungiya.
A lokacin da nake a Umbro… masu sayarwa kan sayi rigunan Ingila miliyan ɗaya, amma idan Ingila ta fice daga gasa tun a matakin rukuni, sai kwatsam kaga muna da tarin riguna da ba su da wani amfani ko ƙima a wajenmu. Wannan haɗari ne."
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa farashi yake kara tsada a baya-bayan nan, Warner sai ya ce: "Masu ɗinki suna da ƙwarewa da gogewa… dabarun da ake amfani da su wajen ƙera kalar kaya da yin tambarin ƙungiya da sauransu duk suna da inganci.
"Sannan idan ka ƙara la'akari da ƙarin kuɗin yarjejeniyar kayan wasa da ke tsakani ƙungiya da kamfanin kayayyakin wasanni, da kuma kuɗin da suke biya wa manyan ƙungiyoyin, sai ka gane dalilin hauhawar farashin kayayyakin."
BBC ta tuntubi dukkan kamfanoni tara da suke ƙera kaya ga ƙungiyoyin Premier League – wato Adidas da Castore da Joma da Hummel da Macron da Nike da Puma da SUDU da kuma Umbro – domin jin ra'ayoyinsu.
Yaya lamarin yake a ɓangaren kayan jabu?

Asalin hoton, Getty Images
Da yake farashi na ta ƙaruwa, akwai hujjoji da ke nuna cewa magoya baya da yawa suna ƙara komawa sayen rigunan jabu.
Border Force – hukumar da ke kula da shige da fice da kuma kwastam – ta ce a yanzu haka tana ƙwace kayayyakin jabu fiye da kowane lokaci a baya.
BBC ta samu izinin ɗaukar hoto a filin jirgin sama na East Midlands, yayin da jami'ai ke buɗe daruruwan kwaleye da akwatuna da sauran abubuwan da ake dakon kayayyaki, inda aka fitar da dozin-dozin na rigunan ƙwallon ƙafa da ake zargin na jabu ne.
Kwace irin waɗannan riguna sau da yawa yana kasancewa ne sakamakon binciken haɗin gwiwa da Ofishin Kare Haƙƙin Mallaka (IPO) da kuma Border Force suke yi.
Andy Cooke-Welling, daraktan aiwatar da doka da tattara bayanan sirri a IPO, ya ce:
"Kayayyakin jabu da ake shigowa da su Birtaniya suna jawo wa tattalin arziƙi asarar da ta kai har fam biliyan 7, kuma mun san cewa hakan na iya haddasa kimanin kusan mutum 80,000 su rasa akinsu."
Ya ƙara da cewa: "Babban ɓangare na wannan matsala na fitowa ne daga masana'antar ƙwallon ƙafa, kuma abin da za mu gani kenan a lokacin gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa shi ne ƙaruwa kayan wasanni na jabu mai yawa, wanda hakan ke nufin ƙarin riba ga masu laifi idan aka ci gaba da sayen kayan nasu na jabu."











