Arsenal ta sake komawa mataki na ɗaya a teburin Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta samu makin da take bukata a Everton ta koma kan teburin Premier League, bayan tashi daga wasan Premier League a filin wasa Hill Dickinson ranar Asabar.
Tun da yammaci Manchester City ta hau kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila, sakamakon doke West Ham a Etihad.
Arsenal ta yi nasarar cin Everton 1-0 a wasan mako na 17 ta hannun Viktor Gyokores a minti na 27 da take leda a bugun fenariti.
Arsenal ta samu damar kara ƙwallaye a ragar Everton da suka koma zagaye na biyu, inda Leandro Trossard da kuma Martin Zubimendi suka buga ƙwallo ya je ya doki turke kowanne.
Da wannan sakamakon Arsenal ta koma matakin farko a teburin Premier League da tazarar maki biyu tsakani da City da tazarar shida tsakani da Aston Villa, wadda za ta karɓi bakuncin Manchester United ranar Lahadi.
An sabunta labarin bayan kammala wasannin ranar Asabar.
Za a fara wasannin mako na 17 a gasar Premier ta kasar Ingila a ranar Asabar, inda za a yi karawa bakwai.
Arsenal ce a saman teburi, amma idan ta yi kasassaba za ta iya tsintar kanta a ta biyu kasancewar maki biyu ne kawai ya raba ta da Manchester City wadda take taka rawar gani a baya-bayan nan.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kawo yanzu an buga wasa 160 da cin ƙwallo 457, kuma Erling Haaland na Manchester City shi ne kan gaba mai 17 a raga, bayan kammala wasannin mako 16.
Wannan shi ne karon farko da za a buga Premier League ba tare da wasu ƴan ƙwallon Afirka da aka gayyata tawagoginsu domin buga gasar cin kofin Afirka da za a yi a Morocco daga 21 ga watan Disamba.
Manchester City za ta kara ne da kungiyar West Ham United da ke fama da matsaloli, kuma take a cikin ukun karshen teburi ya zuwa yanzu.
Wannan na zuwa ne kafin ƙungiyar Arsenal da Mikel Arteta ke jan ragama, wadda ke fama da yawan raunin 'yan wasa, ta je gidan Everton daga baya a ranar ta Asabar.
Ƙungiyar da Pep Guardiola ke horarwa tana ta biyun teburi da tazarar maki biyu tsakani da Arsenal ta ɗaya - kenan za ta koma ta ɗaya na wucin gadi da yake City ce za ta fara wasa da wuri, yayin da Gunners kuma za ta buga nata wasan da dare.
Manchester City na kan ganiya, inda ta sha kashi sau ɗaya kacal a filin Etihad a wasannin 11 a baya-bayan nan, sannan tana kan jerin wasa shida a jere ba tare da rashin nasara ba a dukkan fafatawa.
Duk da raunin manyan 'yan wasanta irin su Rodri da John Stones, da kuma rashin Omar Marmoush da Rayan Ait-Nouri saboda za su wakilci ƙasashensu a gasar cin kofin Afirka ta Afcon, amma sauran ƴan wasan da take da su masu ƙwarewa da hazaka, ya sa ana ganin za ta iya doke West Ham cikin ruwan sanyi, wadda ke can kasan teburin mai fuskantar barazabar faɗuwa daga gasar, kuma ba ta yi nasara ba a wasa biyar a baya-bayan nan.
Haka kuma, City ba ta sha kashi ba a wasa 19 a gasar Premier League da ta fafata da West Ham tun bayan rashin nasarar da ta yi 2-1 a gida a watan Satumban shekarar 2015.
Wasan da suka buga a Premier League a bara:
Premier League ranar Asabar 4 ga watan Janairu 2025
- Man City 4 - 1 West Ham
Premier League ranar Asabar 31 ga watan Agustan 2024
- West Ham 1 - 3 Man City
Wasannin mako na 17 a Premier da za a buga

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Asabar 20 ga watan Disamba
- Newcastle da Chelsea
- Wolves da Brentford
- Bournemouth da Burnley
- Brighton da Sunderland
- Man City da West Ham
- Tottenham da Liverpool
- Everton da Arsenal
Ranar Lahadi 21 ga watan Disamba
- Leeds da Crystal Palace
- Aston Villa da Man Utd
Ranar Litinin 22 ga watan Disamba
- Fulham da Nottm Forest
Arsenal na fama da masu tsaron bayanta da ke jinya

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal za ta je yankin Merseyside a yammacin ranar Asabar domin fafatawa da Everton, wadda take komawa kan ganiya a wasannin da take bugawa, inda ta yi nasara a karawa huɗu cikin shida a baya-bayan nan.
Ƙungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama ba ta cikin kwanciyar hankali saboda ƴan wasanta da ke jinya.
A ƴan makonnin nan Arsenal ta ci wasa uku kacal cikin shida a lig a baya-bayan nan.
Idan har ta yi rashin nasara a filin Hill Dickinson ka iya bai wa ƙungiyar Pep Guardiola damar ɗarewa kan teburin babbar gasar tamaula ta Ingila a lokacin da ake tunkarar bikin kirsimeti da na sabuwar shekara.
Arsenal na fama da ƴan wasa da yawa da ke jinya saboda rauni, inda Kai Havertz da Gabriel Magalhaes da Cristhian Mosquera da Max Dowman da Ben White da Martin Zubimendi dukkansu ba su halarci atisaye ba a ranar Talata.
Ƴan wasan Sunderland shida sun ta fi buga Afcon
Sunderland, wadda za ta je fafatawa da Brighton & Hove Albion, ita ce ƙungiyar da ta fi fuskantar matsala, inda ƴan wasanta shida za su buga wa tawagoginsu gasar cin kofin Afirka da za a fara a Morocco daga ranar 21 ga watan Disamba.
Sunderland na ci gaba da bayar da mamaki a wannan kakar inda take matsayi na takwas a teburin Premier League duk da a bana ta dawo cikin gasar, yayin da Brighton ke bayanta da maki uku, tana matsayi na goma.
Manchester United, wadda ta yi canjaras 4-4 da Bournemouth a wani wasa mai cike da abubuwan ban mamaki ranar Litinin, za ta fuskanci babban ƙalubale lokacin da za ta ziyarci Aston Villa ranar Lahadi.
Aston Villa, wadda ke matsayi na uku a kan teburi, wadda ke kan kololuwar ganiya, tana da tazarar maki uku tsakaninta da Arsenal ta ɗaya.
Sai dai ƙungiyar Manchester United ƙarƙashin Ruben Amorim ba za ta samu Bryan Mbeumo da Noussair Mazraoui da Amad Diallo ba, kasancewar za su wakilci ƙasashensu a gasar AFCON.
Santo na fatan Fullkrug zai koma kan ganiya

Asalin hoton, Getty Images
Kocin West Ham, Nuno Espírito Santo, ya ƙi yin tsokaci kan makomar Niclas Füllkrug, a daidai lokacin da ake ta yada rahotannin yiwuwar sauyin sheƙa a watan Janairu da zarar an buɗe kasuwar cinikin ƴan ƙwallo.
Ɗan wasan Jamus, wanda rauni ya dame shi a lokuta da dama, ana alaƙanta shi da komawa AC Milan, bai buga wasa uku ba a baya-bayan nan a Premier League a West Ham. Sai dai yanzu ya koma atisaye gabanin karawa da za su yi da Manchester City ranar Asabar.
Füllkrug bai ci ƙwallo ko ɗaya ba a wasa tara da ya buga a kakar bana, kuma ƙwallo uku kacal ya zura a raga a wasa 29 tun bayan komawarsa daga Borussia Dortmund a bazarar shekarar 2024, kan kuɗin da ake cewa ya kai fam miliyan 27.
West Ham, wadda ke fuskantar barazanar faɗuwa daga gasar Premier League, saboda zamanta a kasa-kasan teburin gasar, ba za ta samu cikakkun ƴan ƙwallonta ba, sakamakon da Aaron Wan-Bissaka da El Hadji Malick Diouf za su wakilci Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da Senegal a gasar cin kofin Afirka.
Keith Andrews ba zai rena Wolverhampton ba
Kocin Brentford, Keith Andrews, ya gargadi ƴan wasansa da kada su ɗauki karawa da Wolverhampton za ta zo musu cikin sauƙi ko su raina ƙungiyar.
Brentford, wadda ake kira The Bees, za ta je filin Molineux, inda Andrews ya shafe shekara tara yana taka leda a rayuwarsa ta ɗan wasa — ciki har da kakar wasa guda tare da abokin hamayyarsa na yanzu, wato kociya Rob Edwards, wanda har yanzu yake neman nasararsa ta farko tun bayan maye gurbin Vitor Pereira a Wolves.
Sai dai Andrews na ganin Wolverhampton Wanderers suna nuna samun ci gaba a ƴan makonnin nan, kuma ya ce dole ne Brentford ta taka wasa mafi kyau, domin ta murmure daga rashin nasarar da ta sha a hannun Manchester City a wasan Carabao Cup a tsakiyar mako.
Andrews ya fara harkar kwallon kafarsa ne a Wolves, inda ya zama mafi ƙarancin shekaru da ya taɓa zama kyaftin a ƙungiyar cikin sama da shekara 10. Daga baya ya koma Hull City a shekarar 2005.
Brentford na sa ran auna koshin lafiyar Jordan Henderson da Igor Thiago, dukkansu ba su yi karawar Carabao Cup ba da Manchester City a tsakiyar mako sakamakon raunuka da suke jinya, yayin da Josh Dasilva har yanzu bai murmure ba.
Leeds ba ta da sabbin ƴan ƙwallon da ke jinya
Daniel Farke ya ce bai ga wani dalili da zai hana Dominic Calvert-Lewin shiga cikin shirye-shiryen kocin Ingila, Thomas Tuchel zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi ba a baɗi.
Calvert-Lewin ya dawo kan ganiya da koshin lafiya tun bayan komawarsa Leeds United kafin fara kakar bana, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a Everton, wanda ya yi kaka biyu yana jinya.
Kawo yanzu ya zura ƙwallo biyar a wasa 14 da ya buga a gasar Premier League a kakar nan, ciki har da huɗu a karawa huɗu a baya-bayan nan, yana taimaka wa ƙungiyar da Farke ke jan ragama, wadda ke fafutukar gujewa faɗuwa daga gasar.
Farke, wanda Leeds za ta karɓi baƙuncin Crystal Palace a filin Elland Road ranar Asabar, ya ce: "Ya taba yin hakan a baya. Ya buga wa Ingila wasanni da dama kuma yana da tarihin zura ƙwallaye a raga.
Babu wani sabon ɗan wasa da ya ji rauni, amma dai Farke zai rasa Sean Longstaff ba da Daniel James da kuma Lukas Nmecha da ke jinya.
Manyan ƴan wasan Forest na warkewa daga jinya
Kociya, Sean Dyche ya ce manyan ƴan wasan Nottingham Forest na murmurewa daga jinya.
Kungiyar ta yi fama da yawan yan wasa da suka daɗe suna jinya kamar Ola Aina
da kuma Chris Wood.
To sai dai mai tsaron raga, Matz Sels da kuma Nico Dominguez, za su iya buga mata wasan Premier League da za ta buga ranar Litinin.
Wasan da aka buga tsakanin Fulham da Forest a bara:
Premier League ranar Asabar 15 ga watan Fabrairu 2025
- Fulham 2 - 1 Nottingham Forest
Premier League ranar Asabar 28 ga watan Satumbar 2024
- Nottm Forest 0 - 1 Fulham
Forest tana ta 16 a kasan teburin Premier League, ita kuwa Fulham tana ta 14.
Ƴan wasa na goyon bayan koci, Parker - Anthony

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Burnley, Jaidon Anthony ya ce kocin Burnley, Scott Parker, na da cikakken goyon bayan 'yan wasan ƙungiyar, kuma lokaci ya yi da za su koma cin wasannin da suke bugawa.
Ƙungiyar da take matsayi na biyun ƙarshe a teburin gasar, za ta fafata da tsohuwar ƙungiyar Anthony, wato Bournemouth, a ranar Asabar.
Sai dai Bunrnley na fatan kawo karshen wasa bakwai da ta yi rashin nasara a jere a gasar Premier League, rabon da ta ci wasa tun bayan nasara 3-2 a gidan Wolverhampton a cikin watan Oktoba.
Masu tsaron bayanta, Lucas Pires da Kyle Walker za su koma buga wasanni, waɗanda ba su a karawar da suka sha kashi 3-2 a gida a hannun Fulham a makon da ya gabata, sakamakon dakatarwa.
Sai dai Burnley za ta yi rashin Axel Tuanzebe da Hannibal Mejbri da Lyle Foster, kasancewar suna wakiltar ƙasashensu a gasar cin kofin nahiyar Afirka, AFCON a Morocco.
Haka kuma, Connor Roberts da Zeki Amdouni da Bashir Humphreys da Jordan Beyer har yanzu suna jinya.











