Hanyoyi tara da za su taimaka muku rage kashe kuɗi sakamakon tashin farashin kayayyaki

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da cewa farashin kayayyaki ya hauhawa da kashi 17.71 zuwa watan Mayun wannan shekarar.

Hakan ya sa rayuwa ta ƙara tsada, kuma 'yan kasar na ci gaba da fama da mawuyacin hali.

Wannan yanayi ya sa jama'a da dama na ta tunanin yadda za su yi da batun sayen kayayyakin abinci ganin cewa babu kuɗi a hannunsu.

Duk da cewa wasu jama'a sun soma matse bakin aljihu inda suke sayen abin da suke buƙata, amma duk da haka suna so su ga sun rage canji a aljihunsu idan suka shiga kasuwa sayen kayayyakin abinci.

BBC ta tattauna da wata ƙwararriya kan harkokin kuɗi Oluwatosin Olaseinde, wadda ta ƙirƙiro shirin tsimin kuɗi na Money Africa da Ladda tok.

Wasu daga cikin masu yaɗa bayanai a shafukan intanet sun shaida wa BBC yadda za a rage kashe kuɗi ganin yadda tattalin arziki ke tafiya a halin yanzu.

A sayi abin da kawai ake buƙata

Yanzu ba lokaci ba ne na kashe kuɗi domin sayen kayayyakin alfarma, wato abubuwan da ba dole ba ne amfani da su. A sayi abubuwan kawai da ake buƙata.

Babu ɓarna

A samu kofi da za a riƙa auna abincin da ake buƙata idan ana shirin dafa abinci. Kada a ɓarnata komai, a dafa abincin da za a iya cinyewa kawai.

A sake duba jadawalin abinci

Ya kamata a sake duba jadawalin abinci domin a duba abin da za a sauya, amma duk da ana son rage kashe kuɗi akwai buƙatar a ci abinci mai gina jiki.

Misali, idan mutum yana so miyarsa ta ji nama da kifi, mutum zai iya rage su domin amfani da wani abinci nau'in protein kamar ƙwai ko wake.

A sayi kaya tare da mutane

A riƙa haɗa hannu da sauran iyalai ana sayen kayayyaki da yawa musamman busassun abinci da ba su buƙatar kashe kuɗi idan za a ajiye su.

A tantance kayan da ke ciki dakin dafa abinci

Rosie ta ce akwai buƙatar mutum ya duba ɗakin dafa abincinsa da kyau kafin ya tafi kasuwa. Ya kamata a yi haka saboda kada mutum ya je ya sayi abin da dama yana da shi.

A je shago mai rangwamen kayayyaki

A je shagon da suke sayar da kayayyaki masu rahusa kuma za a iya tafiya wuraren da ake sayar da kaya kan sari.

A yi amfani da firiza ko firji da kyau

Saka abinci a cikin firiza zai taimaka wurin ajiye shi.

Za a iya ajiye kayayyaki kamar madara da man shanu da kayan marmari da yaji da kayan lambu da sauran kayayyakin da ake buƙata.

A san yadda za a ajiye kayan abinci

Babu buƙatar a kashe kuɗi da yawa a kowane lokaci kan kayan abincin da za a iya saya da yawa a ajiye.

Akwai yadda mutum zai iya ajiye shinkafa da fulawa da wake da sauran kayayyakin abinci ta yadda ba za su lalace da wuri ba.

Amfani da masu sarin kayayyaki

Domin rage kashe kuɗi, ya kamata mutum ya riƙa shawara da masu sarin kayayyaki domin su sayar.

Za su iya taimakon mutum su saya masa kayayyaki a duk lokacin da su ma za su sayi kaya ko kuma mutum ya je gonar da ake noma kayan abinci domin ya saya a can.