Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Shin rikicin siyasa na ƙara ta’azzara matsalar tsaro ne a Zamfara?
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta daɗe tana fama da matsalar ƴan fashin daji masu kashewa da satar mutane domin kuɗin fansa.
Sai dai kuma wasu na ganin rikicin siyasar Zamfara ya yi tasiri wajen ta’azzara matsalar tsaron tare da kawo cikas ga ƙoƙarin samun nasarar kawar da ita, bayan ganin yadda gwamnan jihar Dauda Lawan Dare da kuma tsohon gwamnan jihar kuma ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle sun fito suna suka da caccakar junansu.
Da farko, Gwamna Dauda ne ya buƙaci Matawalle ya yi murabus a muƙaminsa na minista har sai ya wanke kansa, yana mai zarginsa da taimaka wa ƴan bindiga ta hanyar gayyatarsu gidan gwamnatin jihar da kuma biyansu kuɗin fansa daga lalitar gwamnati.
Sai dai a martaninsa, Matawalle ya musanta zargin tare da cewa shi kaɗai ne ya rantse da Al'Kur’ani cewa ba shi da alaƙa da ƴanbindiga.
Sannan ministan ya ƙalubalanci wanda ya gaje shi ya fito ya rantse da Al'Kura’ni mai tsarki cewa ba shi da hannu a matsalar tsaron Zamfara.
Shi ma ɓangaren Sanata Abdul’aziz Yari na jam’iyyar APC ya fitar da sanarwa ta martani da gwamna Dauda na jam’iyyar PDP game da kalamansa kan Matawalle.
Cikin sanarwar, Abdul'aziz Yari, ya gargaɗi Gwamna Dauda cewa ya daina ɗora laifin matsalar tsaro kan Bello Matawalle, ya mayar da hankali ga aikinsa.
Sai dai a nata martanin, jam'iyyar PDP a Zamfara ta ce Bello Matawalle ya kamata Sanata Yari ya ba wa wannan shawarar.
Ɓangarorin biyu sun daɗe suna sukar juna kan lamurran da suka shafi jihar Zamfara tun bayan zaɓen 2023 da Dauda Lawan Dare na jam’iyyar PDP ya kayar da Bello na jam’iyyar APC.
Masana na ganin wata al’ada ce a Najeriya duk gwamnan da ya hau idan ya gaji matsala zai dinga dora matsalar ne ga wanda ya gada. “Domin shi kansa Bello Matawalle lokacin da yana gwamna ya zargi wanda ya gada Abdul’aziz Yari,”
“Yanzu kuma ga shi yana sa’insa da wanda ya gaje shi Gwamna Dauda – don haka ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya,” in ji Barista Audu Bulama Bukarti mai sharhi kan lamurran yau da kullum kuma masanin sha’anin tsaro a Najeriya.
“Duk ƙarfin mutum idan har aka fito da ƙwaƙwaran hujjoji kan manyan zarge-zargen taimakawa ƴanta’adda da za su gamsar da masu hankali, dole gwamnati ta ƙaddamar da bincike”
“Idan ya kasance ana jifar juna da irin waɗannan maganganu kuma babu wata hujja akansu, babbar matsala ce ga ƙoƙarin samun nasara kan matsalar,” in ji masanin.
Ya ce babban abin takaici ne irin sa’insar shugabannin siyasa a Zamfara domin harkar tsaro ba harkar siyasa ba ce
Ya ƙara da cewa da gwamnan jihar mai ci da kuma ƙaramin ministan tsaro babu wanda Allah ya ɗora wa alhakin matsalar tsaron Zamfara kamar su biyu.
“Alhakin tafiyar da gwamnatin jiha na kan gwamna yayin da kuma ƙaramin ministan tsaro, wakili ne na jihar Zamfra a tarayya. Amma kuma sai ga shi an ga sun koma suna caccakar juna.”
“Rashin tsaro matsala ce da ta shafi kowa – ta shafi PDP ta shafi APC da dukkanin ƙabilu da addinai.”
“Don haka abin takaici ne yadda ake siyasantar da matsalar tsaron maimakon su hada kansu su yaki matsalar,” a cewar Barista Bukarti.
Masu sharhi dai na cewa ƴanbindiga ne yanzu ke cin gajiyar wannan saɓani na shugabannin siyasar ta Zamfara domin idan sun ci gaba da sukar juna, ƴanbindigar sun san cewa ba a shirya samun nasara akansu ba.
“Magana ce ta salwantar rayuka da dukiyoyin al’umma da ake kashewa ba ji ba gani da kuma yadda ake cin zarafi da keta haƙƙin mata da yara ƙanana. Wannan kuma ya fi ƙarfin siyasa kuma ya fi ƙarfin duk abin da za a yi amfani da shi a raba kan mutane, a cewar Rabiu Sani mai sharhi kan siyasar Zamfara.
Mece ce Illar rikicin siyasar?
Kasancewar ma’aikatar tsaro ita take da iko da sojoji da ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro, rashin samun haɗin kai da gwamnatin jiha da take da iko da ƴan sa-kai wata babbar illa ce ga ƙoƙarin shawo kan matsalar tsaron.
Wata babbar illar kuma ita ce yadda ƴan siyasar za su iya yi wa juna zagon ƙasa la’akari da irin jifar juna da suke yi kan matsalar tsaron.
Barista Bulama Bukarti ya ce, ba abin mamaki ba ne wani ɗan siyasa ya dinga cin dudduniyar abokin hamayyarsa idan har ya ga ya fara ɗaukar matakan da za su kai ga samun nasara kan matsalar tsaron,”
“Ƴansiyasar za su fi mayar da hankali kan kare kansu da ƴan’uwansu maimakon mayar da hankali kan matsalar tsaron,”
“Idan ba an tara karfi waje guda ba yana da wahala a iya samun nasara kan matsalar tsaron,” in ji shi.
Hanyoyi biyu na magance matsalar
Zafin adawa da caccakar juna babu wata riba da za ta haifar, illa ƙara ta’azzara matsalar.
Su kansu ƴan fashin daji suna haɗa kansu a ta’asar da suke yi, wani lokaci har haɗaka suke yi a lokacin da za su kai hari.
Barista Bulama Bukarti ya ce lokaci ne da ya kamata ɓangarorin siyasar na Zamfara su yi karatun ta-natsu su kalli al’ummarsu su haɗa kai su yaƙi matsalar tsaron da ta gurgunta kusan komi na ci gaban rayuwa a Zamfara.
Ya ce ya kamata su jingine duk wani bambanci na siyasa su hada kai su samar wa jiharsu tsaro.
“Suna iya yin siyasa idan an zo ɓangaren siyasa, amma babbar illa ce suna siyasantar da rayukan al’umma,” a cewarsa.
Haɗin kai
Dole ne sai an haɗa kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatin jiha
A watannin baya gwamna Dauda da wanda ya gada ƙaramin ministan tsaro Bello Matawalle sun taɓa yin tayin za su iya haɗa kansu domin sa jihar gaba.
Amma kuma ga alama a yanzu yadda suke suka da zargin juna yana da wahala a ce sun kama hanyar cika wannan alƙawalin.
“Dukkanin ƴan’taddan nan maƙiyar APC da PDP da duk wanni ɓangare na al’umma domin kowa ba su ragawa, don haka kuskure ne a ce shugabannin jihar sun gaza kada haɗa kansu.”
“Haɗin kan ƴansiyasa zai ƙara ƙarfafa haɗin kan jami’an tsaro na tarayya da na jiha,” in ji Bukarti.
Kafa gidauniya
Matsalar tsaron Zamfara ta yi sanadiyar salwantar dubban rayuka tare da raba mutane da dama da gidajensu.
Masana na ganin lokaci ne da ya kamata a ce shugabannin siyasar jihar sun haɗa kai tare da bayar da tallafi ga gidauniya ta tsaro domin tallafawa jami’an tsaro da kuma mutanen da rikicin ya shafa.