'Muna so a cike giɓi wajen sayen magungunan cuta mai karya garkuwar jiki'

Asalin hoton, Kettering General Hospital
Gamayyar Ƙungiyoyin Masu Cuta mai Karya Garkuwar Jiki a Najeriya (NEPWHAN), ta nanata buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen samar da kuɗaɗe a cikin gida don cike giɓin da aka samu bayan Amurka ta dakatar da ba da tallafin magungunan kashe kaifin cutar a ƙasashe kamar Nijeriya.
NEPWHAN ta ce janye tallafin, wanda yanzu Amurka ta dawo da wani ɓangarensa, manuniya ce cewa ƙasashe kamar Najeriya su ɗaura ɗamarar nemar wa kansu mafita, da nufin kuɓutarwa da tsare lafiyar al'ummarsu.
Abdulƙadir Ibrahim, shi ne babban jami'i na ƙasa a gamayyar ya shaida wa BBC cewa, duk sun san gwamnati na iya bakin kokarinta, amma ita kadai ba zata iya ba.
Ya ce,"Dole ne a janyo kowa da kowa domin ayi wannan tafiyar baki Daya."
"Duk da an yi alkawarin za a bayar da wani bangare na kasafin kudi domin a cike gibin da aka samu, kuma ba wai abin cuta mai karya garkuwa jiki kadai ya hsafa ba, har da tarin tibi da ma maleriya."In ji shi.
Abdulƙadir Ibrahim,ya ce" Muna bukatar sauran al'umma ma su shigo musamman manya-manyan kamfanoni irinsu Gidauniyar Dangote da T.Y Danjuma, da dai sauran al'ummomi, kuma wannan kira ne da muke yi saboda mutane na wahala."
Ya ce,"Muna fatan jama'a za su saurare mu domin bama son masu dauke da wannan lalura su rasa ransu saboda rashin magani."
Babban jami'i na ƙasa a gamayyar kungiyar ta NEPWHAN, ya ce "A da ana bawa masu wannan cuta magani na wata shida to amma saboda abubuwan da suka faru na janye tallafin da Amurka ta yi, yanzu a wasu wurare ana bayar da na wata biyu kai wani wajenma na wata guda ake bayarwa."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce," Babbar matsalar ma a yanzu it ace na rashin kayan gwajin da ke amfani da su domin a gano mutanen da ke dauke da wannan cuta, wannan shi ne abin da muka fi bukatar gwamnati da kuma al'umma su shigo don a tabbatar da duk ya kamata ya san matsayinsa game da wannan cuta ya sani."
"Idan har ba a yi kokari an samar da kayan gwajin ba to akwai yiwuwar cutar nan zata ci gaba da yaduwa a cikin al'umma wanda mu bama bukatar hakan." In ji shi.
Abdulƙadir Ibrahim,ya ce"A da akwai kayan gwaji amma yanzu akwai karancinsu, sannan kuma muna bukatar tallafi saboda yanzu akwai mutum miliyan Daya da dubu dari shida dake shan magani a yanzu a Najeriya, don haka muna bukatar tallafi."
Babban jami'i na gamayyar kungiyar ta NEPWHAN,ya ce a gaskiya yanzu an samu raguwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya, to amma rashin tallafin da za a cike gibin magungunan zai sanya a koma gidan jiya don cutar zata dawo ta ci gaba da yaduwa.










