Me ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwarmu idan muka zo mutuwa?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Margarita Rodríguez
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
- Lokacin karatu: Minti 5
Wata ƙwararriya kan yadda jiki ke tura sako, Jim Borjigin ta yi mamaki lokacin da ta gano cewa "babu komai" da ke faruwa cikin kwakwalwa idan muna gargarar mutuwa duk da cewa "mutuwa ta zama dole ga kowane mutum".
An gano hakan ne tsawon shekara goma da suka wuce ta hanyar "bazata".
"Muna yin gwaji ne a jikin ɓeraye da kuma duba kwakwalensu bayan yi musu tiyata" ta faɗa wa sashen BBC Mundo.
Nan take biyu daga cikinsu suka mutu.
Hakan ya ba ta damar lura da yadda kwakwalwarsu ke kasancewa bayan mutuwarsu.
"Ɗaya daga cikin ɓerayen ya fara nuna wasu alamu waɗanda ba a saba gani ba," in ji Jim.
Ganin haka ne - ya janyo ta zaƙu ta ga me zai faru a gaba.
"Don haka sai na fara yin wani bincike a ƙarshen mako, tare da tunanin cewa zan samu wani bayani. Na yi mamaki bayan gano cewa ba mu da wani ƙarin bayani kan yadda suka yi suka mutu."
Tun bayan nan, Dakta Borjigin, wadda farfesa ce a harkar kwayoyin halitta da kuma yadda jiki ke kai saƙonni a Jami'ar Michigan, ta jajirce wajen yin bincike don gano abin da ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwa lokacin da muke mutuwa.
Kuma abin da ta gano, ta ce, ya wuce tunanin abin da ta yi tsammani da farko.
Ma'anar mutuwa

Asalin hoton, Getty Images
Ta bayyana cewa a tsawon lokaci, idan mutum ya gamu da bugun zuciya, mutum na iya mutuwa.
A wannan yanayi, ana mayar da hankali kan kwakwalwa: "Ana kiran shi da bugun zuciya, sai dai ba a cewa bugun kwakwalwa.
"Abin da masana suka sani shi ne kwakwalwa na nuna kamar ba ya aiki saboda babu wata alama da za a gani: Waɗannan mutane ba su magana, ba su iya tsayawa, ba su kuma iya zama."
Ƙwaƙwalwa na buƙatar isasshiyar iska domin ta yi aiki yadda ya kamata. Idan zuciya ba ta bayar da jini ba, iska ba za ta kai ga ƙwaƙwalwa ba.
"Saboda haka dukkan alamu sun nun cewa kwakwalwa ba ta aiki, ko kuma aƙalla kwakwalwar ta daina aiki," in ji ta.
Sai dai, binciken tawagarta, ya gano wani abu daban.
Kwakwalwa na aiki cikin sauri
Wani bincike da aka yi kan ɓeraye a 2013, ya gano cewa akwai wasu abubuwa da dama da ke faruwa a kwakwalen dabbobi idan zuciyoyinsu suka daina aiki.
"Sakonni da ke zuwa cikin kwakwalwa na ƙaruwa, wanda ke sanyawa a ji kowane irin abu da zai faru," in ji ta.
Ta ce hakan ba zai yiwu ba idan dabba na raye.
A 2015, wata tawaga ta wallafa sakamakon wani bincike kan kwakwalwar ɓeraye lokacin da suke mutuwa.
"A dukkan binciken, kashi 100 na dabbobin sun nuna ƙaruwar ayyuka a kwakwalwarsu," in ji ta.
"Kwakwalwar na shiga yanayin aiki cikin sauri."
Jijiyoyin kwakwalwa

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A 2023, an wallafa sakamakon wani bincike wanda ya mayar da hankali kan mutum huɗu da suka suma kuma ke kan wata na'ura da ke taimaka musu, inda aka saka na'urori da ke duba yadda kwakwalwa ke aiki.
Waɗannan mutane huɗu sun kasance suna mutuwa ne a lokacin. Likitoci da iyalai sun amince cewa babu wani taimako da za a iya ba su, don haka suka bar su suka tafi".
Tare da amincewar ƴan'uwa, aka kashe na'urorin da ke taimaka musu wajen yin numfashi.
Daga bisani masu binciken sun gano cewa biyu daga cikin marasa lafiyan, kwakwalwarsu na aiki cikin hanzari.
An kuma gano wata jijiyar kwakwalwa - wadda ke aiki da sauri - a lokacin. Jijiyar tana cikin waɗanda ke kai sakonni da kuma tuna abubuwa.
Kwakwalwar ɗaya daga cikin marasa lafiyan ta kasance tana aiki a dukkan ɓangarori.
"Yawancin marasa lafiya da ke gamuwa da bugun zuciya har ta kai ga sun kusa mutuwa, sun ce hakan yana saka su zama mutane na gari, da kuma tausaya wa wasu," in ji Dakta Jim.
Waɗanda suka kusa mutuwa

Asalin hoton, Getty Images
Wasu mutane da suka kusa mutuwa sun ce suna ganin rayuwarsu kamar kiftawar ido ko kuma suna tuna wasu muhimman abubuwa a lokacin.
Yawanci sun ce sun ga tsananin haske wasu kuma sun ce sun fuskanci fitar wasu abubuwa daga jiki da kuma lura da yadda abin ya faru.
"Eh, hakan na iya faruwa," in ji Dakta Borjigin.
"Aƙalla kashi 20 zuwa 25 na waɗanda suka tsira daga bugun zuciya sun ruwaito ganin wani haske fari, ganin wani abu, hakan ya nuna komai na faruwa."
A lamarin biyu daga cikin marasa lafiyan da aka gano kwakwalwarsu na aiki da sauri bayan cire musu na'urorin taimakawa wajen numfashi, masu binciken sun ce wani ɓangare na kwakwalwarsu da ke karɓar bayanai ya nuna cewa mutanen da suke mutuwan sun ga wasu abubuwa.
Sabuwar fahimta

Asalin hoton, UNIVERSITY OF MICHIGAN
Dakta Borjigin ta bayyana cewa bincikenta a jikin ɗan adam ba shi da yawa kuma ana buƙatar ƙarin bincike don sanin abin da ke faruwa cikin kwakwalwa idan muka zo mutuwa.
Sai dai, bayan tsawon shekara goma na bincike a wannan ɓangare, akwai wani abu da ya fito karara: "Ina tunanin maimakon raguwar aikin kwakwalwa, tana aiki da sauri lokacin da aka fuskanci bugun zuciya."
Amma me yake faruwa a kwakwalwa idan ta fahimci ba ta samun iska?
"Muna koƙarin fahimtar haka. Don haka babu bincike mai yawa a kan haka. Babu abin da aka sani," in ji ta.
Ta yi magana kan wani yanayi da ake shiga na ba mutuwa ba, ba kuma rayuwa ba, inda ta karkare cewa: dabbobi ciki har da ɓeraye da bil'adama, na da kwayoyin halitta da za su tsaya da batun rashin iska.
"Har yanzu, ana tunanin cewa kwakwalwa shi ke jin bugun zuciya: Idan zuciya ta daina aiki, ita ma kwakwalwa tsayawa take. Ba za ta iya jure hakan ba kawai tsayawa take."
Sai dai, ta hakikance cewa, ba mu san ko hakan shi ne dalilin ba.
Ta yi imanin cewa kwakwalwa ba ta daina aiki cikin sauki. Faɗa take da wasu abubuwa.
Akwai ƙarin abin da ya kamata a gano
Dakta Borjigin ta ce abin da ta gano da tawagarta a bincikensu, kaɗan ne daga ciki kuma akwai ƙarin abin da ya kamata a gano:
"Na yi imanin cewa kwakwalwa na da abubuwan yaki da rashin isasshen iska wanda ba mu fahimta ba.
"Don haka mun san cewa mutanen da ke gamuwa da bugun zuciya, sun fuskanci haka, kuma bayanan mu sun nuna cewa hakan na faruwa ne sakamakon yawan abubuwa a kwakwalwa.
"Tambayar yanzu ita ce: me ya sa kwakwalwar wanda ke mutuwa ke tattara abubuwa a cikinsa?
"Ya kamata mu zo mu haɗu domin fahimta, bincike, da kuma gano hakan saboda za mu iya yin gwaji da wuri na gawawwaki na miliyoyin mutane, tun da ba mu fahimci ainihin mene ne mutuwa ba."











