Ko Amorim na iya farfaɗo da Manchester United a kakarsa ta biyu?

Ruben Amorim

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kocin Manchester United Ruben Amorim
    • Marubuci, Abdulrazzaq Kumo
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Manchester United ta kwashe fiye da shekara 10 ba ta taka rawar a zo a gani, idan aka kwatanta da yadda ta saba a baya, musamman lokacin da Sir Alex Ferguson yake horas da ƴanwasan ƙungiyar.

Tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya a 2013 United ke neman kocin da ya dace da ita inda suka gwada irin su Jose Mourinho da Erik Ten Haag da David Moyes da Ralph Rangnick da sauran su, amma kowanensu ya gaza dawo da Manchester United kan ganiyarta duk da cewa wasu daga cikinsu sun lashe kofuna.

A watan Nuwamban 2024 ne Manchester United ta ɗauki Ruben Amorim a matsayin sabon mai horaswa domin maye gurbin Erik Ten Haag wanda ya shafe fiye da shekara biyu yana horar da ƙungiyar inda ya lashe kofin ƙalubale na FA a 2024.

Ruben Amorim ya koma Manchester United ne daga Sporting Lisbon inda a lokacin yake taka rawar gani a Portugal - ya lashe kufuna biyar cikin shekara huɗu, kuma salon wasansa ya riƙa ɗaukar hankalin masoya ƙwallon ƙafa.

Sai dai, tun bayan zuwan shi Manchester United wadda dama tana cikin garari, lamura suka fara taɓarɓarewa wa Amorim inda ya kafa wasu munanan tarihi.

United ta kammala kakar wasan 2024/2025 a matsayin ta 15 a teburin Premier League inda Amorim ya yi rashin nasara a wasanni 14, ya yi canjaras shida da nasara bakwai – Hakan ya sa Amorim ne ke da kaso mafi ƙaranci a yawan makin da kowane kocin United ke samu a ƙarshen kaka tun bayan Alex Ferguson.

A gasar Europa League, United ta yi ƙoƙarin zuwa wasan ƙarshe amma Amorim ya gaza doke Tottenham a wasan – ba ta samu gurbin zuwa Champions league ba - lamarin da ya ƙara tayar da hankalin magoya bayan Manchester United.

Baya ga abubuwan da ke faruwa cikin filin wasa, Amorim ya samu saɓani da wasu ƴan wasan ƙungiyar da suka haɗa da Rashford da Garnacho inda ya zargi ƴan wasan da rashin jajircewa a lokacin atisaye, kuma ya daina amfani da su a wasa.

Daga baya ƴan wasan suka bayyana aniyarsu ta barin ƙungiyar inda wasu magoya bayan suka yi fushi da hakan, wasu kuma suka goyi bayan matakin.

Bayan kakarsa ta farko a Manchester United, akasarin magoya bayan ƙungiyar ba su da ƙwarin gwiwa saboda gaza taka rawar a zo a gani, amma duk da haka ƙungiyar ta ce tana goyon bayan Amorim kuma za ta ba shi goyon bayan da yake buƙata.

'Da alama wannan sabuwar Manchester United ce'

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Zuwa yanzu, Manchester United ta sayi ƴan wasa biyu da suka haɗa da Matheus Cunha daga Wolverhampton Wonderers da Bryan Mbeumo daga Brentford.

Duk da cewa ƙungiyar ta ce tana cikin matsalar rashin kuɗi, ta kashe fiye da fam miliyan 130 kan ƴan wasan biyu kuma tana zawarcin Benjamin Sesko.

Rahotanni sun kuma ce United na neman sabon mai tsaron raga da ɗan wasan tsakiya.

Duk da haka, United ta lashe gasar wasannin share fage na wasu ƙungiyoyin Premier League da aka gudanar a nahiyar Asiya inda sabbin ƴanwasan biyu Cunha da Mbeumo suka fara taka wa ƙungiyar leda.

Mai sharhi kan wasanni Simon Stone ya ce Manchester United ɗin da ta lashe wannan gasar sabuwa ce.

"Da alama wannan Manchester United ɗin sabuwa ce. Ƴan wasan sun fara fahimtar salon wasan Amorim," in ji Simon.

Ya ƙara da cewa: "Wasannin share fage da United ta buga nasara ce gare su, kuma ƴan wasan na cikin farin ciki sannan tana da haɗin kan da kowace ƙungiya ke buƙata idan har tana so ta cimma nasara".

Simon Stone ya ce haɗin Cunha da Amad Diallo ya ƙara wa gaban Man United ƙarfi.

Sai dai a ra'ayinsa, a maimakon United ta kashe kuɗi ta kawo ɗan wasan gaban da Amorim ke so, gwara ta sayi ɗan wasan tsakiya mai ƙarfi.

Wasan Arsenal na farko a gasar Premier League inda za ta karɓi baƙuncin Arsenal zai iya nuna wa mutane ko kakar Amorim ta biyu za ta yi kyau ko kuma wasannin share fage na United tashin gishirin andir ne.