Tottenham ta lashe kofin Europa

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham Hotspurs ta lashe kofin zakaru na Europa na kakar wa sata 2024-25 bayan doke Manchester United da ci ɗaya mai ban haushi.
Tun a minti na 42 ne Spurs ta zura wa United kwallo ɗaya ta ƙafar Brennan Johnson, kafin a je hutun rabin lokaci, kuma ƙwallon ce ta maƙale har aka tashi wasa.
Spurst a samu wannan nasara ce bayan kwashe shekara 17 ba tare da lashe kowane irin kofi ba.
Wannan nasara ta bai wa Tottenham gurbin zuwa gasar zakarun nahiyar Turai ta ta Uefa Champions League duk da rashin ƙwazo a Premier.
Sai dai a ɓangare ɗaya ita kuwa United ta ƙare wannan kaka babu komai kasancewar ba ta taka rawar a zo a gani ba a gasar Premier, lamarin da ya sa yanzu ta ke a matsayi na 16 a kan tebur.
Duk da cewa wasan wanda aka buga a filin San Mamés Barria da ke Sifaniya bai ƙayatar ba, amma ba ƙaramin abin alfahari ba ne ga Spurs.

Asalin hoton, Getty Images
A tattaunawarsa da TNT Sports bayan kammala wasan, ɗan wasan Tottenham Son Heung-min ya ce "Wannan ne mafarkin da na daɗe ina yi. Yau ya zama gaskiya. Na fi kowa farin ciki a faɗin duniya.
"Tsawon mako ɗaya da ya wuce kullum sai na yi mafarkin wannan wasa, yau abin da nake nema ya samu, zan iya yin bacci yanzu hankali kwance."











