'Yanwasa na rubibin taka wa Man United leda - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief football news reporter
- Lokacin karatu: Minti 1
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya dage kan cewa ungiyar tasa na nan da farin jininta ga 'yanwasa duk da matsayi na 14 da take yanzu a teburin Premier League.
Ɗan ƙasar Portugal ɗin da ya fara horar da Man United a watan Nuwamba ya ce "ya san" abin da ya ke game da tawagar tasa a kakar wasa mai zuwa.
United na neman ɗanwasan Brazil mai taka wa Wolves leda, Matheus Cunha, da kuma alaƙanta ta da ake yi da ɗanwasna Ipswicht Town Liam Delap, wanda yake da farashin fan miliyan 30 a kwantaraginsa.
United na buƙatar ta lashe kofin zakarun Turai na Europa League kafin ta samu gurbi Champions League a kaka mai zuwa.
Sai dai mai horarwas ba shi da wata tantama cewa farin jinin kulob na nan duk da hakan.
"Manchester United ce fa," a cewarsa. "Kowane ɗanwasa na hanƙoron taka wa Man United leda.
"Idan kuka duba kulob ɗinmu a yanzu, kamar akwai matsaloli, ciki har da sauya koci da aka yi. "Amma duk da haka muna da masaniyar abin da ya kamata, kuma abu ne mai sauƙi a ganar da ɗanwasa.
"Magana ce ta ƙarshen kaka kuma komai zai iya sauyawa. Amma dai muna so mu fara komai da wuri kuma mun san yadda za mu yi hakan."











