Na fi Onana tafka kura-kurai a kakar bana - Amorim

Asalin hoton, Getty Images
Kocin ƙungiyar Manchester United, Ruben Amorim ya ce ya fi golan ƙungiyar Andre Onana da sauran ƴanwasansa tafka kura-kurai a kakar bana.
Ana dai nuna wa Onana yatsa ne bisa kuskuren da ya yi har aka zura ƙwallaye biyu a ragar Man United a wasan da suka fafata na gasar cin kofin Europa da ƙungiyar Lyon ta Faransa, inda aka tashi 2-2.
Wannan kuskuren ya zo ne kwana biyu bayan tsohon ɗanwasan ƙungiyar, Nemanja Matic ya bayyana Onana a matsayin ɗaya daga cikin masu tsaron raga da suka fi rashin nagarta da ƙungiyar ta taɓa yi a tarihinta.
Daga kakar bara zuwa ta bana, Onana ya yi manyan kura-kurai guda takwas da suka yi sanadiyar jefa ƙwalla a ragar Manchester United, wanda shi ne kura-kurai mafi yawan da wani gola ya tafka a gasar Premier ta Ingila.
Amma da kocin ƙungiyar yake ba shi kariya, Amorin wanda ya karɓa ragamar horas da ƙungiyar a watan Nuwamban da ya wuce, ya ce, "idan kuka yi nazarin yadda kakar ke tafiya, na fi ƴanwasan tafka kura-kurai, musamman daga watan nan zuwa watan da ya wuce.
"Babu abin da zan ce game da Onana a wannan lokacin, abin da ya fi dacewa shi ne a shiru a cigaba da sa ido, sannan idan lokaci ya yi, zan zaɓi ƴanwasa 11 da suka fi dacewa ne su fara wasa. Amma lallai na yarda da ƙwarewar Andre Onana," in ji shi.
Za a fafata zagaye na biyu na wasan ne a filin Old Trafford a ranar Alhamis mai zuwa.
Yanzu dai Manchester United ce take ta 13 a teburin Premier, kuma hanya ɗaya tilo da ta rage mata domin samun gurbin shiga gasar zakarun turai ita ce lashe kofin Europa.











