Netanyahu na neman ƙarin farin jini daga yaƙin Iran - Ko Isra'ilawa za su yarda da shi?

    • Marubuci, Wyre Davies
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Jerusalem
  • Lokacin karatu: Minti 5

A watan Maris a lokacin da ya yi watsi da shirin zaman lafiya da ake ganin alfanunsa, firaministan Isra'ila ya ɗauki matakin da wasu masu sharhi ke ganin ya ɗebo ruwan dafa kansa ne a siyasa.

Yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a Gaza, wadda wakilin musamman na Donald Trump Steve Witkoff ya jagoranta, tun ma kafin a rantsar da shugaban na Amurka a wa'adin mulkinsa na biyu ta kai ga sakin gomman 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su, inda aka yi musayarsu da ɗaruruwan fursunonin Falasɗinawa.

A mataki na gaba an tsara sakin ƙarin 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su da kuma janyewar sojojin Isra'ila a hankali - a hankali daga Gaza, kafin a ƙarshe a yi yarjejeniyar dakatar da yaƙin gaba ɗaya.

Ganin cewa bisa ga dukkan alamu dukkanin ɓangarorin biyu - Isra'ila da Falasɗinu sun gaji da rikicin, suna duba yuwuwar kawo ƙarshen yaƙin wanda ake ganin shi ne mafi haddasa asara a tarihin rikicin nasu.

To amma Benjamin Netanyahu ba ya son a kawo ƙarshen yaƙin.

Yayin da ya bayar da umarnin ci gaba da kai hari a faɗin Gaza, firaministan ya ayyana cewa za a ci gaba da yaƙin har sai ya murƙushe Hamas gaba ɗayanta.

Komawar ragowar Yahudawan da Hamas ta yi garkuwa da su ba shi ne babban abin da ke gaban firaministan ba.

Banda ma kuma maganar fararen hula da ake jikkatawa da kashewa da kuma jefa su cikin mawuyacin hali a hare-haren na Isra'ila.

Yawancin 'yan Isra'ila musamman iyalan waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su, sun harzuƙa.

Sun zargi Netanyahu da fifita makomarsa ta siyasa fiye da rayuwa da makomar 'yan uwansu da kuma amfanin ƙasar.

Farin jinin firaministan ya yi ƙasa sosai a wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka yi, sannan yana faman haɗa kan gwamnatin da ta rarrabu sakamakon ministoci masu tsattsauran ra'ayin riƙau da kuma jam'iyyun addinan gargajiya.

Yanzu bayan wata uku, Netanyahu yana alfahari da gagarumar nasarar da yake gani ya samu ta soji a kan babbar maƙiyarshi Iran.

A yanzu dai yana tunanin shirya zaɓen wuri da kuma sake tsayawa takara a matsayin firaminista.

A wani taron manema labarai da ya kira a farkon makon nan, Netanyahu mai shekara 75 wanda tuni shi ne firaministan Isra'ila mafi dadewa a kan mulki, ya ce har yanzu yana da abubuwan da yake so ya kammala, kuma zai nemi yin hakan matuƙar al'ummar Isra'ila na son ya yi, a cewarsa.

Gaba a makon, yana ganin nasarar da yake gani ta lalata shirin nukiliya na Iran a matsayin wata dama da ba zai taɓa bari ta kufce mishi ba, Netanyahu ya nuna cewa zai iya kuɓutar da 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su da kuma murƙushe Hamas, wanda bayan wannan ne zai yi wata babbar yarjejeniya a yankin na Gabas ta Tsakiya.

To amma kiran zaɓen wuri zai iya zamar masa wata babbar kasada, kamar yadda ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta baya-bayan nan ta nuna, domin farin jininsa ya ragu saɓanin abin da yake fata, daga rikicin kwana 12 da Iran.

Yarda

A tsarin siyasar da yake a rarrabe inda haɗaka take da muhimmancin gaske sosai a majalisar dokokin Isra'ila mai kujera 120, jam'iyyar Netanyahu, Likud za ta rasa kujeru da dama da hakan zai sa ta rasa samun rinjaye, kuma hakan zai sa ta nemi yin haɗaka da ƙananan jam'iyyu masu ra'ayin riƙau kamar yadda wata ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a da jaridar Ma'ariv ta gudanar ta nuna.

Haka kuma sakamakon wannan ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa kashi 59 cikin ɗari na 'yan Isra'ila suna son ganin an kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza domin a yi musayar waɗanda Hamas take riƙe da su.

Kusan rabin waɗanda aka tambaya a ƙuri'ar - kashi 49 cikin ɗari su ma suna ganin dalili ɗaya kawai da ya sa Netanyahu ke yaƙin shi ne domin siyasarsa.

A cewar Farfesa Tamar Hermann, ta cibiyar nazarin dimukuraɗiyya ta Isra'ila, kiran zaɓen wuri babbar kasada ce ga Netanyahu fiye ma da yaƙin Iran, saboda a yankin Gabas ta Tsakiya ba za ka san inda kake ba a wata shida na gaba.

Shari'ar cin hanci da rashawa

A mako mai zuwa firaministan zai bayar da bahasi a babbar shari'ar da ake yi masa ta zargin cin hanci da rashawa da kuma zamba.

Kotu ta yi watsi da yunƙurinsa na neman jinkirta shari'ar saboda abin da ya kira ayyuka masu yawa da ke gabansa da kuma halin da ƙasar ke ciki - wato yaƙi da Iran a makon da ya gabata.

Netanyahu da magoya bayansa sun kafe tare da nuna cewa shari'ar wata kutungwilar siyasa ce kawai ake yi masa, to amma a ƙasar da ke fama da rarrabuwar kai masu hamayya da shi su ma sun dage lalle sai ya fuskanci shari'a.

Ganin halin matsin da Netanyahu yake ciki a kan wannan shari'a ya sa Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ke ɗaukar firaministan a matsayin wani gwarzo, yana ganin ya kamata a soke wannan shari'a ko kuma aƙalla a yafe masa.

To amma kuma fa idan ba a manta ba, waɗannan kalamai ne da ke fitowa daga bakin Trump wanda a 'yan kwanakin da suka gabata yake sukar Netanyahun a kan yadda yarjejeniyar dakatar da yaƙin Iran ke neman sukurkucewa tun ma kafin a fara ta.

Haka kuma da yawa daga cikin al'ummar Isra'ila na ganin ƙoƙarin da Trump ke yi na neman shigar wa Netanyahu wannan batu na shari'a abu ne da bai dace ba wanda kuma ba zai taimake shi ba.

Jagoran 'yan hamayya Yair Lapid ya ce bai kamata Trump ya tsoma baki a harkar shari'ar ƙasa mai zaman kanta ba.

A fagen siyasar duniya kuwa, 'yan Isra'ila da dama na zargin Netanyahu da cewa ya cutar da Isra'ila a tsakanin ƙasashen duniya da kuma damar tattalin arziƙinta, ta hanyar ci gaba da yaƙi a Gaza ba tare da buƙatar hakan ba, duk da cewa da yawa daga cikin janar-janar ɗinsa na soja sun ce rundunar sojin Isra'ila ta cimma nasara sosai a Gaza.

Kada kuma a manta da cewa fa har yanzu akwai sammacin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta bayar a kan firaministan da tsohon ministansa na tsaro Yoav Gallant, a kan zargin aikata laifukan yaƙi a Gaza, inda aka kashe mutane sama da 55,000 a yaƙi da Hamas.

Sai dai gwamnatin Isra'ila tare da Netanyahu da kuma Gallant duka sun yi watsi da zargin.

A ƙarshe, kamar yadda yawancin masu sharhi suka ce, zai yi wuya a iya kiran sabon zaɓe a Isra'ila, yayin da ake ci gaba da yaƙi a Gaza, kuma 'yan Isra'ila ke ci gaba da zama tsare a hannun Hamas.

To amma daman tun da daɗewa da dama daga cikin masu sukar lamirin Netanyahu da ma abokan hamayyarsa suka kawar da lissafinsa, ba sa ganin zai yi nasara, kuma ba sa ma tunanin wata dabarar da zai iya yi a nan gaba.