Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Netanyahu ya yaba wa Trump kan shirinsa na kwashe Falasɗinawa daga Gaza
- Marubuci, Ian Aikman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Marubuci, Maia Davies
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
Firaiministan Isra'ila ya ce yana kokarin ganin shirin shugaban Amurka Donald Trump na kwashe al'ummar Gaza tare da sake tsugunar da su ya tabatta.
Benjamin Netanyahu ya ce yana aiki tare da Amurka wajan samar da '' tsari daya'' ga yankin Falasdinu bayan ganawar da suka yi da sakataren harkokin wajan Amurka Marco Rubio a birnin Kudus a ranar Lahadi.
Tattaunawar dai na zuwa ne bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar ganin cewa Gaza ta koma karkashin kulawar Amurka tare da kwashe Falasdinawa miliyan biyu da ke wurin zuwa kasashe makwabta.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargadin cewa tilasta wa farar hula ficewa daga yankin da aka mamaye abu ne da ya saɓa wa dokokin kasa da kasa kuma '' tamkar kawar da wata kabilace daga doron kasa''.
Babban jami'in diflomasiyyar na Amurka ya ce shirin na Trump watakila ya ''girgiza'' wasu tare da bada ''mamaki'' amma ya nuna ''jarumtaka'' wajan bayar da shawara wata hanyar da za a bi saboda ''rashin tasiri shawarwarin baya ba''
Netanyahu ya ce shi da Rubio sun tattauna kan yadda za a aiwatar da manufar Trump, inda ya kara da cewa Amurka da Isra'ila suna da matsaya daya kan Gaza.
Shugaban na Isra'ila ya yi gargadin cewa Israila za ta kai farmakin da ba a taba ganin irinsa ba idan Hamas ba ta saki dukkanin Isra'ilawa da ta yi garkuwa da su ba.
Rubio ya ce , kungiyar Hamas ba za ta iya ci gaba da zama rundunar soji ko ta gwamnati ba, kuma muddin ta tsaya a matsayin rundunar da za ta iya gudanar da mulki, ko kuma rundunar da za ta iya yin barazana ta hanyar amfani da tarzoma, to zaman lafiya zai gagara.
Sojojin Isra'ila sun kaddamar da wani shirin rusa kungiyar Hamas domin maida martani ga wani harin da ba a taba ganin irinsa bayan harin da mayakanta suka kai a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda aka kashe mutane kusan 1,200 tare da yin garkuwa da 251.
Fadan dai ya yi kaca- kaca da Gaza, inda aka kashe mutane fiye da 48,200 a yakin da aka shafe watanni 16 ana gwabzawa, a cewar ma'aikatar lafiya ta Hamas.
Galibin al'ummar Gaza sun rika sauya matsuguni a lokuta da dama, an lalata kusan kashi saba'in cikin dari na gine -ginen yankin kuma tsarin kiwon lafiyar yankin da ruwan sha da kula muhali duk sun gamu da cikas. Haka kuma ana fuskantar karancin abinci da man fetur da magunguna da kuma matsuguni.
Shugabannin Falasdinawa da na Larabawa sun yi watsi da shirin Trump na mamaye Gaza, inda Hukumar Falasdinu da Hamas suka jaddada cewa, filin Falasdinawa ba na sayarwa ba ne.
Sabanin kokarin da Amurka ta yi na samar da zaman lafiya a yankin, babban jami'in diflomasiyyar na Amurka bai gana da wasu shugabannin Falasdinawa ba domin tattauna makomar Gaza.
A yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa a jiya Lahadi, Rubio da Netanyahu sun bayyana wuraren da suka cimma matsaya, da suka hada da muradin kawar da ikon mulkin Hamas a yankin, da hana Iran mallakar makamin nukiliya, da sa ido kan abubuwan da ke faruwa a Syria bayan kifar da mulkin Assad.
Rubio ya zargi Iran da hannu "a duk wani aiki na tashin hankali, a duk wani aiki da zai kawo tarnaki, ga duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali" a yankin.
Netanyahu ya kuma yi alawadai da abin da ya kira " yunkurin tozarta Israila " na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC), wadda ya ce "ta yi wa Israila karya.
Ya gode wa gwamnatin Amurka bisa sanya takunkumi kan kotun ta ICC, wadda a bara ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministan tsaronsa bisa zargin aikata laifukan yaki a Gaza - wanda Isra'ila ta musanta - da kuma wani babban kwamandan Hamas.
Rubio ya ziyarci Isra'ila a rangadinsa na farko a yankin Gabas ta Tsakiya a matsayin sakataren harkokin wajen Amurka.
Har ila yau, zai gana da jami'an Rasha a Saudiyya a cikin kwanaki masu zuwa don tattaunawa kan yakin Ukraine - taron da ba a gayyaci Ukraine da wasu kasashen Turai ba.
Ziyarar tasa ta zo ne bayan jigilar wasu manyan bama-bamai da aka kera a Amurka zuwa Isra'ila a cikin dare.