Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za a wargaza yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza matuƙar Hamas ba ta saki Isra'ilawa ba'
- Marubuci, Paul Adams
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC diplomatic correspondent
- Lokacin karatu: Minti 3
Bayan samun jinkiri wajen sakin sauran Isra'ilawa da Hamas ta yi garkuwa da su, shugaban Amurka Donald Trump – wanda babban aboki ne ga Isra'ila – ya ce za a soke yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma idan sauran waɗanda aka yi garkuwa da su ba su koma gida ba zuwa ranar Asabar.
Ya ce yana son a saki dukkan waɗanda suka rage – ba wai a riƙa sakin ɗaya, biyu, uku ko huɗu ba.
"Ina magana a kashin kaina," in ji shi. "Isra'ila za ta iya watsi da hakan idan tana so."
Idan duka mutane ba su koma ba zuwa ranar Asabar, "za a yi duk bala'in da za a yi", in ji shugaban. Ya faɗa wa manema labarai cewa Hamas za ta gani.
Me ya sa Hamas ta sanar da jinkirta sakin sauran Isra'ila kwanaki kaɗan kafin ta saki sauran waɗanda take garkuwa da su?
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafin Telegram, ta ce tana gargaɗin Isra'ila kuma tana bai wa masu shiga tsakani lokaci domin matsa wa Isra'ila lamba ta cika sharuɗan da aka ginɗaya.
Ta ce "kofa a buɗe take" domin ci gaba da sakin sauran Isra'ilawa ranar Asabar.
Da alama dai Hamas na ba da lokaci domin a warware matsalar.
Amma mecece matsalar?
Hamas ta bayyana jerin korafe-korafe, da ya kunshi jinkirin komawar waɗanda aka ɗaiɗaita da ci gaba da buɗe musu wuta da kuma kin ba da damar shigar da wani nau'in kayan agaji.
Sauran jami'an Falasɗinawa da ba na Hamas ba sun ce Isra'ila ba ta da niyyar barin ayarin motocin agaji su shiga Gaza domin taimakawa Falasɗinawa waɗanda aka lalatawa gidaje.
A dai dai lokacin da gwamnatin Isra'ila ke tattaunawa a fili kan hanyoyin karfafa wa fararen hula ficewa daga Gaza, rashin bayar da izinin zama na wucin gadi da ake bukata, na da nasaba da fargabar da Falasdinawa ke ciki
Fargabar na ƙaruwa a yanzu, kusan kowace rana tun bayan zuwan Trump.
Maganar da ta fara kamar da wasa na son ganin Falasɗinawa sun bar Gaza yayin da za a sake gina wurin, a yanzu ya zama babban batu da shugaban Amurka ya sa a gaba, inda ya buƙaci dukkan Falasɗinawa su bar yankin don Amurka za ta karɓi iko.
Yayin da Trump ke kara kaimi kan bukatarsa, Hamas na tunanin cewa ko akwai bukatar ta shiga tattaunawar tsagaita wuta karo na biyu. Wace tattaunawa za a yi?
Idan da gaske Trump yake, Falasdinawa sun san cewa za su fada hannun Isra'ila don tabbatar da cewa Gaza ba ta da fararen hula. Hana musu matsuguni ba zai wadatar ba. Tabbas sai an haɗa da karfi.
Yanzu Trump ya faɗa cewa muddin ba a saki sauran Isra'ilawa da ake garkuwa da su ba zuwa ranar Asabar, zai gabatar da buƙatar soek yarjejeniyar tsagaita wuta a kuma yi duk bala'in da za a yi.
Sai dai ya ce yana magana ne a kashin kansa kuma Isra'ila za ta iya watsi da hakan.
Ganin akwai alamar komawa fagen yaki, Hamas a yanzu na tunanin me amfanin sakin sauran waɗanda take garkuwa da su.
Ga sauran iyalai da kuma ƴan uwan mutanen da ake ci gaba da garkuwa da su, buƙatar Trump na ƙara saka su cikin fargaba.
"Wannan sanarwa na ƙara nuna cewa Hamas na turjiya," kamar yadda Dudi Zalmanovich ya faɗa wa BBC. Har yanzu ana riƙe da ɗan uwan matarsa, Omer Shem Tov.
"Ina so Trump ya bi sannu a hankali," in ji Mista Zalmanovich.
Isra'ila ita ma tana taka tsantsan kan sanarwar da Hamas ta fitar.
Batun sakin sauran Isra'ilawa a karshen mako na ƙara saka fargaba, yayin da ake cewa abin da ya sa Hamas ta fitar da sanarwa shi ne kar a samu wasu cikin mummunan yanayi.
Ganin yadda aka watsa ta gidan talabijin na yadda mayaƙan Hamas ke riƙe da makamai da kuma yawo da rana tsaka, ga kuma gargaɗin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken kan cewa ƙungiyar ta ɗauki sabbin mayaƙa fiye da waɗanda ta rasa a yaƙi, ba dukkan ƴan Isra'ila ne ke ganin cewa za a samu batun tsagaita wuta.
Yayi wuri a bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma na daf da rugujewa – wanda tun da farko mutane da dama sun yi hasashen haka – amma bayan samun alamu masu kyau a farkon yarjejeniyar, yanzu tana ƙara nuna alamun rugujewa.