Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda aka hallaka ƙasurgumin ɗanbindiga Isuhu Buzu a Zamfara
A Najeriya, kungiyar hadakar askarawa da sibiliyan JTF ta jihar Zamfara sun sami nasarar halaka wani kasurgumin dan bindiga, mai suna Kacalla Isuhu Buzu a garin Kaya na yankin karamar hukumar Maradun.
Wannan lamari ya auku ne yayin da mutanen garin Kuncin Kalgo ke kukan 'yan bindiga sun sara masu harajin kudi, naira miliyan ashirin da sayen babura uku, bayan wani hari da 'yan bindigan suka kai masu irin na hushi kaza kare kan dami, inda suka kashe mutum biyu.
Hakan dai ya biyo wani farmaki ne da sojoji suka kai wa 'yan bindiga a garin na Kuncin Kalgo.
Wani mazaunin garin Kuncin Kalgo na yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce yanzu haka suna zaune cikin gagarumin tashin hankali da barazana ta rayuwa:
''Domin kuwa 'yan bindiga sun sa mumu harajin naira miliyan 20, sun kuma ce sai mun saya musu babura uku. ba su fada mana takamaimai ranar ba, kawai dai sun ce mu tabbatar mun hada wannan kudi in ba mu kawo su ba za su zo su yi kan-mai-uwa-da-wabi.''
Mutumin ya bayyana abin da ya ce ya janyo musu wannan lamari : ''Ko a ranar Asabar da jami'an tsaro suka kai musu farmaki suka kore su daga cikin gari zuwa daji, suka anshe baburansu suka tafi da su.
''Bayan da safe jami'an tsaro sun kai musu farmaki da yamma suka dawo mumu da martani suka fashe haushi kanmu, inda suka kashe mana mutum biyu, suka yi ta ruwan wuta cikin gari kowa ya boye.''
Ganin cewa al'ummar wannan yanki na zaune da 'yan bindigan lafiya, mai maganar ya ce dole ce ta sa su wannan zaman lafiya domin ba yadda za su yi.
''Dalilin da suke zaune da mu, mu ba yanda za mu yi da su, ai su ke yanda suka ga dama. Su ke mulkinmu, ba mu ke mulkinsu ba.
''Kuma a cikin garin da suke zaune da mu, da makamansu da kaki da bindigoginsu da albarusansu da suke ta yawo, wallahi in magana ka yi cikin mutane ma, wani yana iya daukar bulala ya maka.
''Sannan babu abin da ba sa mamu. Abinci in suka ga dama za su ci ba su biya. Mace ma in suka gani suna iya amfani da ita ba wanda zai iya ce musu komi. Ai wannan ba zaman lafiya ba ne ba, saboda sun fi karfinmu ne ba yanda za mu yi.
Ya kara kokawa da cewa: ''Mun yi kira ga gwamnati a taimaka mana da jami'an tsaro a cikin garin nan. Matukar jami'an tsaron nan ba cikin gari suka zo suka zauna ba, lalle-lalle, in dai za su kawo farmaki ne su koma, to mu za su bar mumu bala'i baya.''
Sai dai Mustafa Jafaru Kaura, babban mai ba gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan harkokin yada labarai, ya ce gwamnatin jihar ta farga da irin matsalolin tsaron da ke addabar mutanen garin na Kunchin Kalgo da ma sauran wasu garuruwa da ke yankin kuma nan ba da jimawa ba za ta fitar da wani mataki, wanda zai yi wa tufkar hanci:
''Amma dai tabbas gwamnatin nan na samun gagarumar nasara kan 'yan bindiga inda ko a jiya-jiyan nan an samu nasarar kashe wani kasurgumin danfashi wanda ake kira Kacalla Isuhu Buzu wanda ya dade yana addabar mutanen yankin karamar hukumar Maradun.''
Ya ce an samu nasarar kashe danbindigan ne sakamakon bayanan sirri da Askarawan jihar suka samu inda suka yi masa kwanton-bauna.
''Don tabbatar da an kashe shi sai da aka fito da kanshi aka shigo cikin gari don jama'a su tabbatar da cewa an samu nasarar kashe shi, kuma aka yi ta murna saboda an samu sauki kwarai da gaske.''
Mai ba gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan harkokin yada labarai, ya kara da cewa gwamnatin jihar ba za ta saurara ba, game da bin duk wani mataki da ya dace, har sai ta kakkabe 'yan bindigan da ke addabar jama'ar jihar.