Yadda aka kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Ɗan-Isuhu a Zamfara

Lokacin karatu: Minti 3

Fitaccen ɗanbindigar nan da ya yi fice wajen garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, wanda ya addabi yankunan jihar Zamfara da wasu yankunan jihar Katsina, wato Kachalla Isuhu Yellow, wanda aka fi sani da Ɗan-Isuhu ya cimma sa'i.

Lamarin ya auku ne da yammacin Alhamis, bayan daɗewa da ya yi yana wasan-ɓuya da jami'an tsaro da kuma wasu daga cikin takwarorinsa shugabannin ƙungiyoyin ƴanbindiga a arewacin Najeriya da suke nemansa ruwa a jallo.

Rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar ɗanbindigar a wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Yazid Abubakar ya fitar.

Haka nan ma ɗanjarida mai bincike kan harkokin ƴanbindiga, Munir Fura-Girke ya tabbatar da kashe ɗanbindigar.

Sanarwar ƴansanda ta ce jam'ian tsaro ne suka samu labarin cewa an ga ƴanbindiga da dama ɗauke da muggan makamai sun nufi garin Keta, inda ya ce jami'an tsaron haɗin gwiwa na ƴansanda da askarawan Zamfara da ƴan sa-kai da mafarauta suka kai ɗauki, inda suka fafata da gungun ƴanbindigar na tsawon lokaci.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kashe ɗansanda ɗaya, da askarawan tsaron jihar guda huɗu da ƴan sa kai guda biyu, sannan mafarauta biyu sun jikkata a lokacin artabun.

"Amma duk da haka jami'an haɗin gwiwar sun samu nasarar kashe ƴanbindiga da dama, ciki har da fitaccen ɗanbindiga Ɗan Isuhu Mudale, wanda ya daɗe yana addabar yankin Tsafe," kamar yadda sanarwar ta nuna.

Yadda aka kashe shi

Da yake yi wa BBC ƙarin haske kan yadda aka samu nasarar kashe ɗanbindigar, ɗanjarida Munir Fura-Girke ya ce dama akwai rashin jituwa tsakanin Ɗan-Isuhu da wasu gungun ƴan fashin daji da dama, musamman da ɓangaren Dogo Giɗe.

Fura-Girke ya ƙara da cewa Ɗan-Isuhu ƙani ne ga Ado Aleiro, "kuma sun daɗe suna takun-saƙa da rikice-rikice a tsakaninsu."

Ya ce shi ma Ɗan-Isuhun ya kashe wani babban ɗanbidiga da ake kira Baƙin Sifindi da abokinsa, "bayan ya musu kwanton ɓauna a tsakanin dajin Munhaye da Ɗanjibga, ya buɗe musu wuta ya kashe su."

Wane ne Ɗan-Isuhu

Ɗan-Isuhu ya fi yin fice ne wajen harkokinsa a yankunan Tsafe da Ɗansadau da ke jihar Zamfara.

A game da fitattun hare-haren da ya kitsa kuwa, Munir Fura-Girke ya ce sanannen ɗanbindiga ne da sunansa ke amo a tsakanin mutanen yankunan Zamfara da Katsina.

"Yana cikin manyan ƴanbindiga da ke kai miyagun hare-hare musamman a tsakanin ƙananan hukumomin Tsafe da Gusau a jihar Zamfara. Sannan galibin yankunan kudancin Katsina irin su ƙananan hukumomin Faskari da Funtua da Malumfashi da Bakori da wani yanki na Danja duk shi ne yake da iko da su. Duk hare-haren da ake yi a yankunan, ko dai shi ya kitsa su, ko shi ya kai da kansa tare da yaransa."

Fura-Girke ya ce Ɗan-Isuhu ya shahara wajen kai wa jami'an tsaro hare-hare, "ya kashe da dama musamman a hanyar Gusau zuwa Funtua, da garkuwa da mutane da safarar makamai a tsakanin ƴanbindiga."

"Abin da ya fara fito da shi, shi ne harin ƴanbindiga a jirgin ƙasa na Abuja zuwa Kaduna. Yana cikin waɗanda suka kai harin a ranar 28 ga watan Maris a 2022. Galibin waɗanda aka yi garkuwa da su a jirgin shi ne ya ajiye su, ya riƙa azabtar da su, har lokacin da suka biya kuɗin fansa."

Fura-Girke ya ce Ɗan-Isuhu ne ya yi garkuwa da wasu ƴanmata yaran wani Alhaji Abu Furfuri "suka yi wata takwas, sannan a ƙarshe ya karɓi kusan miliyan 70 kuɗin fansa a 2022.

A ƙarshe Fura-Girke ya ce kashe ɗanbindigar zai taimaka wajen kawo sauƙi ga mutanen yankunan da yake da iko da su.