'Ya ce idan na yi yunƙurin tserewa zai kashe ni' - Matar da aka yi wa fyaɗe a DRC

Asalin hoton, Göktay Koraltan / BBC
- Marubuci, Orla Guerin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Goma
- Lokacin karatu: Minti 8
Gargaɗi: Wannan rubutun na ɗauke da bayanai masu tsayar da hankali ciki har da bayanin yanda fyade yake.
"Ya gaya min cewa idan na yi yunƙurin tserewa zai kashe ni."
Pascaline, mai shekara 22, kenan take bayanin irin maganganun da mutumin da ya yi mata fyade a gidan yarin Goma, birni mafi girma a gabashin Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo, a cikin daren ranar 27 ga watan Janairu, yake faɗa mata.
he largest city in eastern Democratic Republic of Congo, in the early hours of 27 January.
"Ya tilasta sadu da ni, na ƙwammace na bari ya yi a kan na rasa rayuwata," Pascaline ta sheda wa BBC.
Shi ne mutum na biyu da ya yi mata fyaɗe a gidan yarin Munzenze. Na farko an yi mata ne da azabtarwa da har sai da ta suma.
Ta ce waɗanda suka yi mata fyaɗen sun hauro ne daga ɓangaren maza na gidan yarin inda bango ne kawai ya raba su", ta ce.
"Mun ji hayaniya lokacin da suke haurowa ta kan wani tankin ruwa. Suna da yawa sosai abin ya tsorata mu. Waɗanda tsautsayi ya faɗa wa an yi musu fyaɗe. Waɗanda kuma suka yi sa'a sun samu sun fita ba tare da an ko taɓa su ba."
Ana hatsayinta a cikin gidan yarin, da kuma cikin birnin, yayin da 'yantawayen M23 ke durfafo Goma, bayan da suka yi gagarumar nasarar kunno kai yankin.
Yawancin masu tsaron gidan yarin da kuma hukumomin birnin tuni sun tsere. Ana iya jin ihu da hayaniya a wajen gidan yarin.
Bayan 'yan sa'o'i sai wuta ta tashi a cikin gidan yarin kuma bisa ga dukkan alamu fursunoni maza ne suka cinna ta, yayin da suke ƙoƙarin tserwa.
Zuwa wayewar gari fursunoni maza 4,000 sun tsere. Mata kuwa 'yan kaɗan ne suka iya guduwa. Jumullar fursunoni mata 132 da kuma yara aƙalla 25 suka mutu a sanadiyyar wutar, kamar yadda wasu kafofi biyu suka bayyana.
Wani jami'in Majalisar Ɗinkin Duniya ya sheda wa BBC cewa aƙalla mata 153 ne suka ƙone a wutar.
Bayan wata ɗaya Pascaline ta dawo wannan gidan yari inda ta ga yadda wuta ta lalata ginin inda hasumiyar tsaron gidan ke tsaya kyam amma ba kowa a cikinta.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tana son bayyana wa duniya abin da ya faru da ita da ma sauran fursunonin mata da suka mutu, ƙarara ba tare da an sakaya suna ko hotonta ba.
Ta ratsa ta tsakiyar babban ɗakin kurkukun matan, inda take kallon yadda wuta ta yi wa wajen - ga bango ya ƙo, ga tukwane da tarin tufafi duk a warwatse. Bisa ga dukkanin alamu abin ya tsorata ta, ta ma kasa magana, sai dai kanta kawai take girgizawa.
"Zuwa wani lokaci ban ma san me yake faruwa ba kuma," ta ce. "Bayan da na ga waɗanda suka mutu ne daga nan hankalina ya dawo na natsu - zan iya cewa Allah ne kawai Ya cece ni."
Pascaline, da ke sayar da albasa ta samu kanta a wannan kurkuku ne bayan da wanda take yi wa aiki ya zarge da sata.
Ita ma Nadine, mai shekara 22, ta komo gidan yarin a karon farko. Ta kasa mantawa da munanan abubuwan da ta gani a lokacin.
"Idan ina bacci da daddare, sai na riƙa ganin duk abubuwan da suka faru. Ina ganin waɗanda suka mutu. Ina ganin duk tarin mutanen da na gani sun mutu har zuwa lokacin da na tsira. Maimakon su buɗe mana ƙofa, sai suka bari mu mutu a nan kawai kamar dabbobi."

Ita ma Nadine ta ce maza biyu ne suka yi mata fyaɗe.
"Sun zo ne da giya," ta gaya wa BBC. "Suna son bugar da mutane. Sun ka,ma ni ne da ƙarfin tsiya. Sun ɗauki dukkanin matana da ke nan."
BBC ba ta iya tantance mata nawa aka yi wa fyaɗe ba a wannan dare, daga cikin jumullar mata 167, da kafofi suka bayyana ana tsare da su a gidan yarin.
Nadine na cike da fushi a kan hukumomi saboda ɗaure ta da aka yi tun da farko a kan bashin da ake binta, ta ce, sannan kuma aka ƙi barinta ta fita.
"Ba na jin za a taɓa yin adalci a Kongo," ta ce. "Na yi Allah-wadarai da yadda gwamnati ke tafiyar da abubuwa a nan."
Gwamnatin Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo, wadda ke can nisan sama da kilomita 1,500 (Mil1,000 ) can a babban birnin ƙasar Kinshasa - ba ta da sauran iko a birnin Goma. 'Yantawaye ne ki riƙe da iko a birin kuma suna ci gaba da nausawa gabashin.
Daga irin kayayyakin da wuta ta ƙona a gidan yarin ana iya ganin wasu kayayyaki kamar na yara.
An ba wa fursunoni mata damar zama da ɗa ko 'ya ɗaya daga cikin 'ya'yansu a gidan yarin.
Yara biyu ne kwai suka tsira daga gobarar daga cikin su 28, in ji wata kafa.
Tun kafin lamarin, a wannan rana an saki fursunoni yara, waɗanda ake tsare da su a wani ɓangare ne gidan.

Ba hayaƙi da wutar ba ne suka kashe masu rauni kawai, in ji wata matar fursuna mai shekara 38, wadda ba ta so a bayyana ta. Za mu kira ta da suna Florence.
Ta ce, "yara sun fara mutuwa" lokacin da aka fara harba hayaƙi mai sa hawaye a ɓangaren mata na gidan yarin.
"'Yansanda da sojoji sun kewaye gidan, waɗanda suka riƙa harbi da jefa hayaƙi mai sa hawaye cikin gidan maimakon su kashe wutar,'' in ji Florence.
"Lokacin da aka fara harba mana hayaƙin mai sa hawaye, sai wutar ta tsananta. Idanuwanmu na ta hawaye suka zama kamar barkono aka sa mana. Kusan ba ma ta yadda za ka iya numfashi," in ji ta.
Zargin wutar da kuma fyaden na tattare da ruɗani, inda kowane ɓangare ke zargin juna da laifi.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam sun ce 'yantawayen M23 da sojojin gwamnati dukkansu na amfani da fyaɗe a matsayin wani makamin yaƙi a rikicin na Jamhuriyar Dumukuraɗiyyar Kongo.
Sai dai kuma a kan wannan Florence ta ce fursunoni ne 'yan uwansu suka aikata fyaɗen
"Kana iya ganin cewa fursunoni ne. Wasu sun zo ne ko takalmi babu a ƙafarsu lokacin da suka hauro kan ɗakin fursunoni mata, suna ta kiran sunan waɗanda suka sani. Kuma babu cikin waɗanda suka kawo harin da yake sanye da kayan-sarki ko kuma yake ɗauke da makami.
Florence ta ce ta fara jin ƙaran harsashi tun daga ƙarfe 11 na dare har bayan nan, kuma 'yansanda na kashe fursunonin da ke tserewa a waje.
"Idan fursuna ya fita sai su harbe shi. Lokacin da ake ta ruwan harsashin, na durƙusa ina roƙon Ubangiji Ya cece mu daga wannan mawuyacin hali da muke ciki."
Wasu daga cikin fursunonin da suka hauro ɓangaren mata suna neman inda za su tsira ne, in ji ta.
Sun wuce daga cikin bangwayen da ke kallon waje - inda waje ne da ba a saba ajiye 'yansanda ba. To amma nan da nan sai wuta ta tashi a wajen ganga-ganga.
Florence ta fara ganin wutar da misalin ƙarfe 4 na asuba. Daga nan kuma sai abin ya tsananta tana taimaka wa mutane daga wannan zuwa waccan.
"Mutane na mutuwa a gaban idanunmu. Ba zan iya ƙirga su ba. Mun yi ta ƙoƙarin farfaɗo da su ta hanyar ba su ruwa. Wasu matan hayaƙi ne da rashin iskar da za su shaƙa ya sa suka mutu. Wasu kuma bugun zuciya ne ya kashe su," in ji Florence a tattaunawarta da BBC.
Ita ma ta ɗora alhaki a kan hukumomin Kongo a kan mutuwar da dama.
"Ya kamata a ce hukuma ta buɗe ƙofofin gidan yarin lokacin da wutar ta tashi ko kuma su zo su kashe ta."
BBC ta tuntuɓi hukumomin ƙasar da ke Kinshasa kan abin da za su ce game da abin da wasu da suka tsira a lamarin suka faɗa mana amma har zuwa yanzu ba wata amsa daga hukuma.
Florence ta ce a ƙarshe dai an buɗe ƙofar gidan yarin ɓangaren mata da misakin ƙarfe 11 na safe amma ba ta san wanda ya buɗe ba - ita da wasu 18 da suka tsira suka fito, kuma ba wani taimako da aka ba su.
"Hatta 'yansanda da muka gani a hanya ba su tambayi labarin fursunonin ba, ko su tambaya su ji ko wani ya ji rauni ko ma dai ya muke," in ji ta.
A wannan lokacin mayaƙan 'yantawayen tuni sun shiga wasu sassan birnin , tun bayan da suka fara danno kai da mislain ƙarfe 8 na safe. Birnin Goma ya faɗa hannunsu.
Kusan ba abin da ya dame su game da matan suna kurkuku ko suna waje.

Asalin hoton, Göktay Koraltan / BBC
Mun haɗu da wata matar da ta tsira, Sifa, mai shekara 25, kwance a wani tanti a asibitin Goma, wadda wata ƙawarta ta cece ta daga wutar.
sai a ɓangaren jikinta na hagu take iya kwanciya saboda ko'ina jikinta ciwo yake mata sosai.
An nannaɗe hannunta na dama kusn gaba ɗaya da bandeji, kuma ko'ina a hannunta da fuskarta ƙuna ce. hatta bayanta ma da ƙuna. Idan ma'aikatan jinya za su sauya mata bandeji sai sun ba ta maganin rage raɗaɗi.
To amma jiwonta ya wuce na jiki domin 'ayrta mai shekara biyu, Esther ta rasu a kurkukun.
"Ina goye da Esther, lokacin da za mu gudu mu tsira, sai na ji wani abu ya faɗo mat. Bam ne ko mene ne ban sani ba. Nan take ta mutu," Sifa ta gaya wa BBC.
To ta yaya Sifa, mai sayar da gyaɗa ta samu kanta a kurkukun da ke maƙare da mutane da 'yarta?
An zarge ta ne da hannu a fashi da makami, abin da ta musanta. Ta ce an tura ta kurkuku ne ba tare da an same ta da laifi ba. 'Yan ƙasar sun sheda wa BBC cewa wannan abu ne da aka saba gani a ƙasar.
Ba lalle ba ne a san ainahin abin da ya faru a gidan yarin Munzenze. Bisa ga dukkan alamu, masu riƙe da iko ba su da niyyar hanzarta gano abin da ya faru. Walau gwamnatin da ke Kinshasa ko kuma 'yantawayen da ke riƙe da iko a Goma.












