Ƴan tawayen M23 sun sake kame birni na biyu mafi girma a DR Congo

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Emery Makumeno
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Kinshasa
- Lokacin karatu: Minti 2
Ƙungiyar ƴan tawayen DR Congo ta M23 sun kutsa birnin Bukavu birnin mafi girma a gabashin jamhuriyar, inda suka ƙwace ofishin gwamnan lardin.
Mutane sun yi jeru a kan tituna suna tafawa da jinjina wa mayaƙan a lokacin da suke kutsawa cikin birnin ba tare da fuskantar wata tirjiya ba.
Bukavu shi ne birni na biyu mafi girma a yankin da ƴan tawayen suka karɓe bayan Goma mai cike da albarkatun ƙasa.
Gwamnatin Congo ta faɗi cewa kame birnin sannan ta umarci mazauna birnin da su zauna a gidajensu "domin gujewa ka da mayaƙan su hare su."
Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙasashen turai sun gargadii cewa farmakin na baya-bayan wanda ya tilasta wa dubban mutane barin gidajensu ka iya haddasa mummunan yaƙi a yankin.
Wata mazauniyar birnin na Bukavu wanda ba ta son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa mafi yawancin mutanen har yanzu na tsoron barin gidajensu.
"Tun jiya ƙananan yara da matasa suka ɗauki makamai. Suna ta harbe-harbe irin na kan-mai-uwa-dawabi, da kuma sace-sace, in ji ta.
A ranar Juma'a ne mayaƙan suka kame filin jirgin saman birnin na Bukavu da ke da tazarar kilomita 30 arewa da birnin - daga nan kuma sai suka nufi birnin wanda shi ne babban birnin lardin Kudancin Kivu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Gwamnan lardin, Jean-Jacques Pursu Sadiki ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa har safiyar Lahadi mayaƙan na cikin Bukavu, inda ya ƙara da cewa sojojin na Congo sun janye domin gujewa taho-mu-gama.
Shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce an sace kayan abinci daga rumbunan ajiyar abinci da ke da tan kusan 7,000 na kayan abincin.
Kama birnin na biyu mafi girma dai na nuni da irin yadda ƴan tawayen na M23 ke ƙara faɗaɗa hare-hare da suka fara ƙaddamarwa tun a 2021, kuma ana yi wa al'amarin kallon cin fuska ga shugaba Felix Tshisekedi.
Mai magana da yawun gwamnatin Dr Congo, Patrick Muyaya ya ce Rwanda na keta haddin jamhuriyar ta DR Congo, ƙasa mai cin gashin kanta ta hanyar ƙara faɗaɗa kutse da cin zarafin al'umma.
Gwamnatin ta DR Congo dai ta zargi Rwanda da kitsa rikicin a yankin da manufar cin gajiyar albarkatun ƙasar wani abun da Rwanda ta musanta.
Shugaba Tshisekedi yana son takwaransa na Rwanda Paul Kagame ya fuskanci takunkumai dangane da abin da ke faruwa a ƙasar.
Sai dai shugaba Kagame ya yi watsi da barazanar kuma ya sha nanata cewa muradin Rwanda shi ne tsaron kanta.
Mayaƙan na M23 da suka haɗa da ƴan ƙabilar Hutu da ake zargi da hannu a kisan kiyashi a Rwanda a 1994 lokacin da aka kashe mutum 800,000 mafi yawanci ƴan ƙabilar Tusi a cikin kwanani 100.










