Yadda sojojin haya daga Romania suka kasa kai labari a yaƙin DR Congo

Sojojin haya daga Romania

Asalin hoton, EPA

    • Marubuci, Ian Wafula
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa security correspondent, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sojojin haya na Romania su kimanin 300 sun tsinci kansu a wani mumunan yanayi bayan an kai su DR Congo domin taya ɓangaren sojojin gwamnati yaƙi a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Mika kai da suka yi bayan harin da ƴan tawaye suka kai a gabashin birnin Goma ya kuma wargaza fatan waɗanda suka nemi aikin na samun maƙudan kuɗaɗe.

BBC ta ga takardun kwangiloli da ke nuna cewa ana biyan waɗannan sojojin da aka ɗauka aiki kusan dala 5,000 (£4,000) a wata, yayin da asalin dakarun sojojin ƙasa na yau da kullun ke samun kusan dala 100, ko kuma a wasu lokutan ma su yi ta tiƙa aiki ba tare da an biya su ba.

An dai kwaso waɗannan sojojinj hayar na Romania ne domin taimaka wa sojojin ƙasar wajen yaƙar ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, waɗanda suka ce suna fafutukar kare haƙƙin tsirarun ƴan ƙabilar Tutsi ne da ke DR Congo.

A lokacin da aka fara kai farmakin a birnin Goma a daren Lahadi, an tilasta wa ƴan ƙasar ta Romania neman mafaka a sansanin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Constantin Timofti, wanda aka bayyana a matsayin shugaban tawagar sojojin hayar, ya shaidawa tashar TVR ta Romania ranar Litinin, cewa, ''ƴan tawayen M23 sun samu goyon bayan sojoji da kayan aikin soja na zamani daga ƙasar Rwanda, kuma sun yi nasarar kai wa wuraren da mu ke a birnin Goma. ''

"Rundunar sojin ta ƙasar ta tsere daga fagen daga kuma hakan ya tilasta mana janyewa."

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Romania, Andrei Țărnea, ya shaida wa BBC cewa, tattaunawa mai cike da sarkakiya ta biyo baya, inda ƙungiyar M23 ta miƙa mayaƙan Romanian - waɗanda ya bayyana a matsayin ma'aikata masu zaman kansu na gwamnatin DR Congo da ke aikin horar da sojoji - zuwa Rwanda.

Birnin Goma ya kasance a daidai kan iyakar ƙasar da Rwanda - kuma ƴan jarida sun ɗauki hoton sojojin hayar yayin da suke tsallakawa, suna miƙa wuya.

Kafin su tsallaka, wani bidiyo da aka naɗa da wayar hannu ya nuna kwamandan M23 Willy Ngoma yana caccakar ɗaya daga cikin ƴan ƙasar Romania cikin harshen Faransanci, yana gaya masa ya zauna a ƙasa, ya harde kafafunsa ya kuma dora hannayensa a kai.

Ya tambaye shi game da horon da ya samu na soji -inda ya amsa da cewa dakarun faransa ne suka horar da shi.

"Sun ɗauke ku aiki kan albashin dalar Amurka 8,000 kowanne wata, kuna cin abinci mai kyau," Ngoma ya yi ihu, yana mai nuni da bambamcin da ke tsakanin wancan da albashin sojan gwamnatin Congo.

"Muna faɗa ne don makomarmu. Kar ku zo nan don neman yawon shaƙatawa," in ji shi.

,,

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojojin hayar suna aiki ne tare da sojojin Congo - kamar yadda aka gani a farkon watan Janairu a yankin arewa maso yammacin Goma
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba a dai tabbatar da inda Ngoma ya ga inda ake biyan dala 8,000 ba, amma takardun kwangilar aiki da wani tsohon sojan haya ɗan kasar Romania ya nuna wa BBC a watan Oktoba ya yi bayani dalla dalla cewa kuɗin da ake biyan manyan ma'aikata ya fara ne daga dala 5,000 a kowane wata yayin aiki da kuma $3,000 a lokacin hutu.

Yarjejeniyar ba ta zayyana wani takamamane lokacin wa'adin aiki ba, tare da shirin cewa ƴan kwangilar za su yi hutun wata ɗaya bayan sun shafe watanni uku a bakin daga.

Na gana da tsohon sojan haya a Bucharest babban birnin Romania, inda na je na binciki Asociatia RALF, wadda wata tawagar ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya suka ce wani kamfani ne na Romania na "tsoffin ƴan Romania da suka taɓa aiki tare da rundunar sojojin ƙasashen waje ta Faransa''.

Horațiu Potra, ɗan ƙasar Romania ne ke jagorantar ta, wanda ya bayyana kansa a matsayin mai horar da dakarun soja.

A watan Yuni, a lokacin da nake Goma, na ga da irin waɗannan sojojin haya a shingayen binciken ababen hawa kuma an baza su a cikin birni, suna aiki tare da sojojin ƙasar.

A cikin shekaru ukun da suka gabata, wasu sun bayar da rahoton ganin yadda suke tuka sojojin Congo cikin motocin sojoji.

..

Asalin hoton, Horațiu Potra

Bayanan hoto, Horațiu Potra ya taka muhimmiyar rawa a aikin horas da sojojin DR Congo

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ba ta amsa buƙatar da BBC ta yi mata ba, kan ko an gudanar da binciken kan waɗannan sojojin haya kafin a ɗauke su aiki, ko kuma idan akwai kamshin gaskiya kan batun rashin daidaiton albashi tsakanin ƴan kwangilar masu zaman kansu da sojojin Congo ba.

Iyalan Vasile Badea, ɗaya daga cikin ƴan ƙasar Romania biyu da aka kashe a watan Fabrairun da ya gabata, lokacin da mayakan M23 suka yi wa ayarin sojojin kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa Sake, wani gari da ke kusa da Goma, sun shaida wa BBC cewa shi ɗan sanda ne.

Badea, mai shekaru 46 ya ɗauki dogon hutu daga rundunar kuma ya fara aiki a DR Congo saboda tayin da aka yi masa na albashi mai tsoka.

Ɗan sandan ya fuskanci ƙalubalen bioyan kuɗin wani gida da ya samu kuma ya na buƙatar ƙarin kuɗi.

..

Asalin hoton, Vasile Badea family

Bayanan hoto, Vasile Badea ya ɗauki hutu daga rundunar ƴan sanda lokacin da aka kashe shi a DR Congo a bara

Amma wani sojan DR Congo da na gana da shi a watan Yuni ya nuna rashin jin daɗinsa game da dabarun rundunar sojin ƙasar.

"Ba a yi adalci ba, idan ana maganar faɗa, mu ne ake fara turawa fagen daga," Sojan da ya buƙaci a sakaya sunansa ya sahidawa BBC.

"Su (sojojin hayar) suna zuwa ne kawai a matsayin tallafi."

Ya tabbatar da cewa ana biyansa kusan dala 100 duk wata amma yawanci ana jinkiri ko kuma ba ma a biya shi gaba ɗaya.

Na yi mu'amala da shi na ƙarshe mako guda da ya gabata inda ya tabbatar da cewa yana nan a Kibati kusa da Goma, inda sojoji ke da sansani.

"Abubuwa sun yi muni sosai," in ji shi a cikin wani saƙo da ya aiko.

Tun daga lokacin ban sami damar magana da shi ba - kuma tun daga lokacin mayakan M23 suka mamaye sansanin Kibati tare da kashe sojoji da dama, ciki har da kwamandansa.

DR Congo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Congo na karɓar albashin kimanin dala 100 kowanne wata - kuma wani sojan da aka ɗauka ya shaida wa BBC cewa wani lokaci su kan fuskanci jinkiri ko ma a ƙi biyansu baki ɗaya.

Masu sa ido kan al'amuran yau da kullun sun ce karɓe Goma da aka yi dagfa hannun sojoji cikin sauri na nuni da wargajewar dabarun tsaro na DR Congo, inda a dakarun sojin ƙasar wanda hakan ya taimakawa M23.

Richard Moncrief, daraktan ayyukan ƙungiyar International Crisis Group mai kula da yankin Great Lakes, ya yi nuni da cewa, gami da sojojin hayar, sojojin ƙasar Congo suna aiki tare da dakarun ƙungiyar Southern African Development Community (Sadc), da mayakan sa kai da aka fi sani da Wazalendo, da kuma sojoji daga Burundi. .

"Yana haifar da yanayi inda ba zai yiwu a shirya ayyukan soja a tsanake, saboda ba a fayyace ta inda ake samun umarni ba ," kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Ina tsammanin yana da mahimmanci a yi aiki don samun haɗin kai sosai a ayyukan sojin da ake gudanarwa a Arewacin Kivu, ana iya ɗaukar matakin rage yawan ƙungiyoyi masu dauke da makamai."

Ga tsohon sojan hayar, makomar abokan aikinsa na Romania ba ta zo da mamaki ba.

"Rashin tsari yana haifar da gazawa," kamar yadda ya shaida wa BBC.