Ƴan tawaye sun kashe sojojin wanzar da zaman lafiya 13 Jamhuriyar Congo

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Ian Aikman
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 4
An kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya guda 13 a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo sanadiyyar tashin hankalin da ake fama da shi a ƙasar.
Rundunar sojin Afirka ta Kudu wadda dakarunta ke cikin masu ƙoƙarin wanzar da zaman lafiyar a Congo ta ce an kashe sojojinta guda 9 a lokacin da ake fafutikar hana mayaƙan ƴan tawaye na ƙungiyar M23 daga dannawa zuwa birnin Goma da ke gabashin ƙasar ta Congo.
Haka nan daga cikin waɗanda aka kashen akwai sojojin Malawi guda uku da kuma na Uruguay guda ɗaya.
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce ya yi magana da shugabannin ƙasashen na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo da kuma na Rwanda yayin da ake ci gaba da kira da kawo ƙarshen rikicin.
Yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta janye duk wasu ma'aikatanta waɗanda zamansu bai zama tilas a Goma ba – birnin da ke da yawan al'umma da suka haura miliyan ɗaya, inda faɗa ke ƙara tsananta.
Wani taron Majalisar Dinkin Duniya da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin, yanzu an dawo da shi zuwa Lahadi saboda ƙazancewar rikicin.
Ƙungiyar M23 ta yi kira ga dakarun Congo da ke a birnin Goma da su miƙa wuya domin guje wa zubar da jini.
Duk wannan na zuwa ne bayan mayaƙan M23 sun hallaka wani gwamnan soja na ƙasar ta Congo a lokacin da ya kai ziyara fagen daga a ranar Alhamis.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A farkon wannan wata na Janairu, mayaƙan sun karɓe iko da garuruwan Minova da Masisi da ke gabashin ƙasar ta Congo.
A jiya Asabar lokacin tattaunawarsa ta waya da shugabannin Congo da kuma na Rwanda, Macron ya yi kira gare su da su kawo ƙarshen yaƙin.
Kamfanin dillancin labaru na AFP ya ambato shugabar harkokin waje ta Tarayyar Turai, Kaja Kallas na buƙatar ƙungiyar M23 ta dakatar da matsawar da take yi zuwa Goma, sannan kuma ta yi tir da goyon bayan da Rwanda ke bai wa ƙungiyar.
Yaƙi ya ƙazance tsakanin ƙungiyar M23 da dakarun Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo tun farkon kamawar wannan shekara, inda ƙungiyar ta yi nasarar kame iko da wurare da dama, fiye da kowane lokaci a baya.
Rikicin na baya-bayan nan ya riga ya tarwatsa sama da mutum 400,000 cikin wanna shekarar kawai, kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Shugabannin al'umma a yankin sun ce sama an kashe sama da mutum 200 a wuraren da ƙungiyar ta kame, yayin da ɗaruruwan mutane ke karɓar magani a asibitocin birnin Goma.
A baya-bayan nan ƙasashe da dama, kamar Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Amurka sun buƙaci mutanensu su fice daga birnin na Goma.

Asalin hoton, Reuters
Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta yi gargaɗin cewa farar hula na shiga cikin ƙarin haɗari yayin da sojojin na Congo ke artabu da mayaƙan M23, kuma ta zargi dukkanin ɓangarorin biyu da aikata manyan laifukan take hakkin bil'adama a kan fararen hula.
Tun daga shekarar 2021 ne ƙungiyar ƴan tawaye ta M23 ta ƙwace iko da yankuna da dama masu arziƙin ma'adanai, lamarin da ya yi sanadiyyar tarwatsa dubban ɗaruruwan al'umma.
Gwamnatin Congo da Majalisar Dinkin Duniya duk sun zargi Rwanda da mara wa ƴan tawayen baya, sai dai gwamnatin Rwanda ba ta gaskata ko kuma musanta zargin ba.
Rwanda ta taɓa zargin Dimokuraɗiyyar Congo da yin aiki tare da mutanen da ake zargi da kisan kiyashin da aka yi wa ƴan ƙabilar Tutsi na da masu sassaucin ra'ayi na Hutu a Rwanda a shekarar 1994.
Ƙungiyar M23 ta samo asali ne daga wata ƙungiyar ƴan tawaye da aka kafa a 2012 domin kare ƴan ƙabilar Tutsi da ke a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, wadda ta yi zargin ana zalunta da hantarar al'ummarta.
Sai dai masu sukar Rwanda sun zarge ta da yin amfani da ƙungiyar M23 domin kwasar ma'adanan ƙasa kamar zinare, da ke danƙare a yankin na gabashin Congo.










