Me ya sa ake kiraye-kirayen korar ƴan Najeriya a Ghana?

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan Najeriya da ke Ghana na kokawa kan kiraye-kirayen da al'ummar ƙasar ke yi na a kore su. Kuma ana faragabar wannan lamarin zai iya haifar da taƙaddamar diflomasiyya tsakanin manyan ƙasashen biyu da ke Yammacin Afirka.
Yeƙuwar 'Nigerians must go' - wato Dole ƴan Najeriya su tafi - ya samo asali ne bayan wani da ake kira Chukwudi Ihenetu ya yi iƙirarin cewa shi ne 'sarkin ƴan ƙabilar Igbo a Ghana.
Su dai al'ummar Ibo sun samo asali ne daga kudu maso gabashin Najeriya.
Tun a shekara ta 2013 ne Ihenetu ya yi bidiyon nasa, sai bidiyon ya sake tasowa inda ake ta yaɗa shi a shafukan sada zumunta na ƙasar ta Ghana.
A cikin bidiyon, Ihenetu ya bayyana cewa ya mallaki fili mai girmar eka 50 a Ghana, inda yake shirin gina mazaunin ƴan ƙabilar ta Ibo, wanda ya ce zai ƙunshi kasuwa da otal da fadar sarki da ɗakin taro da zai ɗauki mutum 2,000 da kuma tituna waɗanda za a sanya wa sunayen shugabannin al'umma Ibo.
Bayan Allah-wadai da bidiyon ya haifar, Ihenetu ya gana da ministan harkokin waje na Ghana, Sam Ablakwa a cikin watan Yuli, inda ya nemi afuwa.
Ablakwa ya ce muna sa ran "dukkanin ƴan'uwanmu ƴan Afirka baƙi za su bi dokokinmu da al'adunmu tare da guje wa duk wasu abubuwa ko kalamai da suka saɓa wa doka ko kuma na rarraba kawuna".
A bidiyoyin da aka riƙa yaɗawa a ƙarshe-ƙarshen watan da ya gabata, an ga ƴan ƙasar ta Ghana na zanga-zanga ɗauke da alluna masu rubutun da ke cewa "yaranmu na ɓacewa saboda ibo", "Ƴan Najeriya na sace mutane suna amfani da su domin yin tsafi: da kuma "Lafiyarmu na cikin hatsari saboda yawaitar karuwanci".
A cikin ɗaya daga cikin bidiyoyin an ga watan mata na ce: "Dole ne ƴan Najeriya su tafi saboda ba zai yiwu kuna a ƙasar wasu ba amma kuna yin yanda kuka so. Dole ƴan Najeriya su tafi."
"Har ma sarkin Ibo suke da shi a Ghana. Sun ƙwace mana ƙasarmu. Nan da wani lokaci za mu ci galaba a kansu mu sake karɓe ƙasarmu," in ji wani mai zanga-zangar.
'An tsane mu ne kawai'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sai dai ƴan Najeriya da ke zama a Ghana sun koka kan yadda ake cin zarafi da kuma hantarar su, musamman ma daga masu bayar da hayar gidaje.
Sun bayar da misalin yadda ake tsuga wa ƴan Najeriya kuɗin haya, sannan kuma ake ware su ana gindaya musu wasu sharuɗɗa na kasuwanci, waɗanda suka shafi kasuwancin ƴan Najeriya kawai.
Wani ɗan kasuwa ɗan Najeriya ya ce kiraye-kirayen korar su daga ƙasar wani yunƙuri ne kawai na wasu ƴan Ghana waɗanda ba sa farin ciki da ci gaba da ƴan Najeriya a ƙasar ke samu a harkar kasuwanci, inda suke son su fusata ƴan Najeriya har ƴan Najeriyar su mayar da martani, ta yadda hakan zai haifar da rikicin diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu.
"Yawancin ƴan Najeriya sun fuskanci ƙiyayya. Idan ka je neman hayar gida ko shago, ana ɗaukar cewa kana da mugun kuɗi saboda kai ɗan Najeriya ne, ko da kuwa kai ma faɗi tashin rayuwa kake yi," in ji shi.
"Idan ɗan Ghana zai biya dala 95 na haya, kai za a iya buƙatar ka biya nunki biyar na hakan ko ma fiye, idan kuma ka gaza sai a kore ka."
Fargabar hari
Kiraye-kirayen sun sake tayar da tarihin takun-saƙa da ke tsakanin Ghana da Najeriya da kuma fargabar kai hari.
A shekarun da suka gabata, saɓanin fahimta ta kasuwanci ta sanya ƴan kasuwar Ghana sun rufe kantunan ƴan Najeriya da ke ƙasar bayan sun zargi ƴan Najeriya da karya dokokin da suka haramta musu sayar da kaya kai-tsaye ga al'umma.
A shekarun 1980, Najeriya ta kori mutane sama da miliyan ɗaya waɗanda suka haɗa da ƴan Ghana da wasu daga ƙasashe masu maƙwaftaka a lokacin da ta fuskanci matsin tattalin arziƙi, inda ƙasar ta ɗora wa ƴan ƙasashen waje laifin yawaitar rashin ayyukan yi da aikata laifuka.
Sai dai a farkon wannan wata shugaban Ghana ya bayyana cewa ba za a lamunci nuna ƙiyayya ba a ƙasar.
"Najeriya da Ghana ƴan'uwan juna ne wadanda ke da dogon tarihi kuma ba za mu bari wani abu ya shiga tsakaninmu ba," in ji shi.
"Sake yaɗa tsohon bidiyo da wani ɗan Najeriya mazaunin Ghana ya yi tun sama da shekara 10 da ta gabata ya ɗaga hankula, to amma abin farin cikin shi ne an shawo kan lamarin," kamar yadda John Mahama ya ambata.











