Me ya sa wasu ƴan Ghana ke fafatawa a rikicin ƴan tawayen Burkina Faso?

Sojojin Burkina Faso

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojojin Burkina Faso na faɗa da masu iƙirarin jihadi waɗanda suka karɓe iko da yankuna da dama na ƙasar
    • Marubuci, Ed Butler
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Tamale, Ghana
  • Lokacin karatu: Minti 6

Wasu ƴan Ghana uku sun faɗa wa BBC cewa suna cikin waɗanda ke faɗa tsakanin masu iƙirarin jihadi da kuma sojoji a Burkina Faso, inda suka kwatanta cewa ana gwabza ƙazamin faɗa da kuma artabu da juna.

"Muna tare da gawarwaki a kodayaushe. A wasu artabu, na ga gawarwakin mutane 40, 50 har 100 ma," kamar yadda ɗaya daga cikin mutanen ya shaida wa BBC.

Dukkansu uku, waɗanda suka haura shekara 30 zuwa 40, sun ce sun gwabza faɗa a Burkina Faso sau da dama tun 2018. Sun tsallaka iyakar da ke tsakanin ƙasashen biyu mai tsawon kilomita 550, ba tare da jami'an tsaro sun gane su ba.

Sun musanta cewa suna faɗa ne don addini ko kuma masu iƙirarin jihadi na horar da su, inda suka ce sun je yin faɗa ne domin kare al'ummomin fararen hula waɗanda suke da alaƙa ta iyali da kuma ƙabila.

"Sojojin Burkina Faso sun kashe babban yayana da matarsa da kuma yaransa. Abin ya yi min ciwo matuka. Sojoji sun kutsa cikin gidajensu. Sun kashe dukkansu, iyali gaba-ɗaya da ya ƙunshi mutum 29," in ji ɗaya daga cikin mutanen.

Sai dai wani daga cikinsu ya ce addini yana ƙarfafa masa gwiwa, inda ya ce: "idan ka mutu kana faɗa tsakanin masu iƙirarin jihadi, to Al-jannah za ka tafi, kana kan hanya madaidaiciya.

Kan mutanen ya rabu a lokacin da aka tambaye su cewa ko sun taɓa shiga a kai wa fararen hula hari.

Ɗaya ya musanta yin haka, amma guda kuma ya amsa cewa ya yi.

"Wasu mutane sun taimaka wa sojoji wajen far mana, shi ya sa mu ma za mu kashe su," in ji shi.

"Ka san... Ba na jin daɗin faɗa a haka. Yawan mutane da muka kashe, mutanen da sojoji suka kashe, abin yana da muni. Amma faɗan nan ya shiga cikin jininmu," a cewarsa.

Duka mutanen sun buƙaci a sakaya asalinsu.

BBC ta kasa tabbatar da iƙirarinsu, amma sun nuna mana hotunan makamai, tare da kwatanta mana wuraren da aka gwabza faɗa a baya-bayan nan da bayyana sunayen kwamandojin masu iƙirarin jihadi a Burkina Faso.

BBC ta tattauna da mutanen a wasu kasuwannin sayar da dabbobi a arewacin Ghana, inda aka yi zargin masu iƙirarin jihadi na ɗaukar sabbin mayaƙa.

Mata masu gudun hijira.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mutane sun kasance suna yin tafiye-tafiye tsakanin Ghana da Burkina Faso
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Yunin 2022, wata ƙungiya mai zaman kanta mallakin Faransa (Promediation) ta ce bincikenta ya nuna cewa masu iƙirarin jihadi sun ɗauki sabbin matasa tsakanin 200 zuwa 300 daga Ghana.

Sannan a wani rahoto da cibiyar hulɗar ƙasashe ta ƙasar Netherlands ta fitar a watan Yulin bara, ya ce mayaƙan ba su samu wata gagarumar nasara ba wajen ɗaukar sabbin mutane a Ghana.

Sai dai, mutanen sun faɗi mabambantan abubuwa, inda suka faɗa wa BBC duk da cewa ba a tabbatar ba cewa mutane daga sassan Ghana da kuma kabilu daban-daban na shiga ƙungiyoyin mayaka a Burkina Faso.

"Wasu na yin faɗa don jihadi. Wasu na yi don kasuwanci," ɗaya daga cikin mutanen ya faɗa.

Suna samun dabbobi da dama cikin waɗanda masu ikirarin jihadi ke sacewa bayan korar mutane daga ƙauyuka.

"Idan muka far wa gari, muna ɗaukar dabbobi: wani lokaci kamar 50, wasu lokuta kumja 100," in ji ɗaya daga cikin mutanen.

Ana zargin cewa ana kai dabbobin zuwa arewacin Ghana, sannan a sayar cikin kasuwanni.

BBC ta samu tabbacin safarar dabbobin ta kan iyaka daga wajen masu harkar dillancin dabbobi.

An yi imanin cewa sayar da dabbobin na cikin kuɗaɗen shiga da ƙungiyoyi irin Jama'atul Nasrul-Islam wal -Muslimin (JNIM) ke samu, wanda ke alaƙa da al-Qaeda da suka fi kai hare-hare a Burkina Faso. Tana kuma kai hare-hare a Nijar da Mali.

A bara Majalisar Ɗinkin Duniya ta kwatanta yankin yammacin Afrika a matsayin cibiyar ta'ddanci na duniya.

Ƙungiyoyin agaji sun ce a tsawon shekaru goma da suka wuce, yaƙi ya ɗaiɗaita wasu mutum miliyan biyu a Burkina Faso da kisan dubun-dubata.

Ninpoa Nasuri na ɗaya daga cikin dubban mutane da suka tsere zuwa Ghana don kauce wa rikici.

Ta faɗa wa BBC cewa a gabanta aka kashe mijinta a 2024 yayin wani samame da mayaƙan JNIM suka kai ƙauyensu da ke gabashin Burkina Faso.

"Sun cafke mutanen, kuma suka lakaɗa musu duka har suyka mutu. Mijina manomi ne. Ba shi da alaƙa da sojojin gwamnati ko rikicin," ta shaida wa BBC.

Sauran mutanen da aka ɗaiɗaita sun kwatanta irin wannan cin zarafi da sojojin Burkina Faso suka yi musu.

Saafiya Karim in a colourful outfit
Bayanan hoto, Saafiya Karim ta tsere zuwa Ghana bayan samame da aka kai wa ƙauyensu

"Mutanen da suke kashewa sun kai shekara 80 zuwa 90. Mutanen nan ba za su iya riƙe bindiga ba, ba za su iya faɗa da kowa ba. Sun kashe su ba tare da wani dalili ba," in ji Saafiya Karim.

Zuwa yanzu dai ayyukan masu ta da ƙayar baya bai wani tasiri kan Ghana ba, duk da cewa an kai wasu hare-hare ne a ƙasashe da ke makwabtaka da ita a Togo da Ivory Coast.

A wata sanarwa da aka aika wa wani ɗan jaridar Ghana Mohammed Eliasu Tanko, wani mutum da ke ayyana kansa da wakilin ƙungiyar JNIM - ya ce ba su da niyyar kai hari a Ghana.

"Ba a bai wa mayaƙan JNIM damar kai hari Ghana ba. Wannan sahihiyar sanarwa ce. JNIM ba ta son shiga yaƙi da Ghana," kamar yadda mutumin da aka fi sani da Ansari ya faɗa a cikin sanarwar, wadda BBC ta gani.

Sai dai ƙaruwar rikici tsakanin al'ummu a wani ɓangare na Ghana ya janyo fargabar cewa masu iƙirarin jihadin na ƙoƙarin amfani da rikicin domin cimma buƙatunsu.

Garin Bawku ya shafe gomman shekaru yana fama da rikice-rikice tsakanin ƙabilu da dama waɗanda ke ƙoƙarin mallakar sarautar yankin. Ana tunanin cewa sama da mutum 100 ne aka kashe a rikicin tun bayan ɓarkewar faɗa a watan Oktoban 2024.

"Kowane yammaci, Bawku na cike da harbe-harben bindiga da kuma musayar wuta. Mutane na amfani da bindigogin AK47 da M16 da kuma harsasai da dama," kamar yadda wani mazaunin yankin ya faɗa wa BBC.

Mata zaune a karkashin wani itace a sansanin ƴan gudun hijira a garin Bawku na Ghana.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu gudun hijira daga Burkina Faso sun zo garin Bawku domin neman mafaka

An zargi wasu mutane da sayar wa dukkan ɓangarorin makamai.

"Mun gano cewa suna sayar da makaman da suka ƙwace daga wajen sojojin Burkina Faso. Suna yin haka ne ta hanyar amfani da motocin dakon kaya da ke zuwa Nijar da komawa ɗauke da albasa. Suna ɓoye makaman cikin waɗannan motoci," Tanko ya shaida wa BBC.

"Wani jami'in leƙen asiri ya tabbatar min da cewa wannan sabuwar hanya ce ta shigar da makamai. Kuma jami'an tsaron Ghana ba su da kayan aiki da za su gano waɗannan motoci idan suna wucewa, abin ya saka Ghana cikin barazana," in ji shi.

Ministan tsaron Ghana Edward Omane Boamah bai yi martani ga buƙatar ji daga garesa da BBC ta yi.

Shugaba John Mahama, wanda ya sha rantsuwar kama aiki a watan Janairu bayan samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa a watan Disamban, ya kai ziyara garin Bawku a watan da ya gabata a wani ƙoƙari na ɗabbaka zaman lafiya tsakanin ƙungiyoyin da ke gaba da juna. Duk da haka, an ruwaito ci gaba da samun artabu tsakaninsu.

Mai magana da yawun jam'iyyar da ke mulki a Ghana Sammy Gyamfi ya shaida wa BBC cewa kawo karshen rikicin Bawku shi ne abin da gwamnati ta fi bai wa fifiko.

"Rikicin ya fara yaɗuwa kuma idan ba a ɗauki mataki ba, akwai alamun cewa masu iƙirarin jihadi daga wani yanki za su iya amfani da damar don cimma manufarsu," in ji shi.

Mutanen guda uku da BBC ta tattauna da su - sun ce mai yiwuwa rikicin ya yaɗu.

"Wannan abin zai iya zuwa ko'ina, ko kuma kowace ƙasa. A baya babu rikici a Togo amma yanzu ana kai hare-hare a can. Idan za su iya zuwa Togo, za su iya isa Ghana. Waɗannan mutane suna da karfi, suna da iko sosai," ɗaya daga cikinsu ya faɗa.

Sai dai ɗaya daga cikin mutanen ya bayyana cewa ta da ƙayar baya a Burkina Faso ba ta alaƙa da ƙoƙarin yin jihadi.

"Suna kashe mutane kawai, tare da sace dabbobinsu. Abin da ke faruwa ba jihadi bane don haka ba na son shi," in ji shi.