Yankin Sahel na Afirka ya koma fagen yakin al-Qaeda da IS

- Marubuci, Daga Mina Al-Lami
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sashen BBC Monitoring
Yankin Sahel na Yammacin Afirka ya zama wani sabon fage na yaƙi, bayan ƙungiyar IS ta bayyana cewa tana gwabza faɗa da mayaƙan al-Ƙa'ida a Mali da Burkina Faso.
IS ta bayyana haka ne a ranar 7 ga Mayu, a wani rahoton da ta buga a jaridarta ta al-Naba da ke fita mako mako.
Ta zargi ƙungiyar Jamaat Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) mai alaƙa da al-Ƙaida, kan soma faɗa da kuma haɗa rundunar dakaru domin kai wa IS hari a ƙasashen biyu.
An saba da wannan yanayin inda IS da ƙungiyoyin masu alaƙa da al-Ƙaida ke gwabza faɗa a wasu wuraren, kamar Yemen da Somalia da Syria tare da ɗaukar mayaka da kwasar albarkatu.
Maƙalar IS ta ci karo da rahotannin da aka fitar a farkon wannan shekarar da ke cewa ƙungiyoyin biyu suna kawance da juna a yankin.
Faɗan zai iya yin tasiri ga ayyukan dakarun cikin gida da na ƙasashen waje a yankin Sahel, inda dukkanin ƙungiyoyin suka matsa da kai hare-hare tun a bara.

Asalin hoton, ISLAMIC STATE PROPAGANDA
Me IS ta ce?
A rahotonta, ƙungiyar IS ta yi allawadai da hare-haren al-Ƙaida na baya-bayan nan a Mali da Burkina Faso, inda ƙungiyoyin suke da karfi.
Ta ce JNIM, bisa umurnin shugabanta Iyad Ag Ghaly da Amadou Koufa, sun girke manyan dakaru domin kai wa ƙungiyar IS hare-hare lokuta da dama a dukkanin kasashen biyu tun watan Afrilu.
IS ta ce, yunƙurin JNIM, ya zo daidai da kuma faɗan da dakarun hadin guiwa na Afirka da na Faransa ke yi da ita.
IS ta yi iƙirarin cewa, JNIM na amfani da wannan damar domin kai wa IS hare-hare a wannan lokacin.
Ta kuma ce IS ce babbar barazanar JNIM a yanzu, tun lokacin da ta amince ta tattauna da gwamnatin Mali har suka ƙulla yarjejeniyar zaman lafiya da dakarun da ke goyon bayan gwamnati da kuma masu adawa da kuma ƙabilun da ke arewacin Mali.
A baya IS ta so ta yi amfani da amincewar JNIM domin bude tattauna da hukumomin Mali a matsayin wata hanya ta gurgunta ƙungiyar mai alaka da al-Ƙaida.
Me ya sa yanzu?
Ba a san dai manufar dalilin da ya sa IS da JNIM ba su fito suna bayyana faɗan da suke gwabzawa ba har sai bayan fitar da wannan rahoton na IS, musamman a cewar IS, sun daɗe suna gwabza faɗa tun 17 ga Afrilu.
Rahoton IS, ya biyo bayan wani bayanin da ba a tabbatar ba da aka alaƙanta da JNIM kuma aka yaɗa intanet ranar 5 ga Mayu a wani shafin da ba a tantance ba. inda al-Ƙaida ta fito ta yi watsi da iƙirarin amincewa da tsagaita buɗa wuta.
Idan har bayanin ingantacce ne, zai iya bayyana dalilin da ya sa IS ta fito ta sanar da duniya.
Zargin bayanin JNIM na zuwa ne a matsayin martani daga wani saƙon murya da aka yaɗa a watan Afrilu wanda aka ce ya fito ne daga kwamandan IS a Mali Abdel Hakim al-Sahraoui. Saƙon na IS yana neman tsagaita buɗa wuta idan JNIM ta amince ta biya kuɗin jinin da ta zubar na mayaƙan IS da kuma neman a saki maƴaƙanta da aka kama.
Dukkanin ƙungiyoyin babu wanda ya tabbatar da sakwannin da aka ake zargi.

Asalin hoton, ISLAMIC STATE PROPAGANDA
Rahoton na IS ya tabbatar da abin da kafofin yaɗa labarai na cikin gida ke bayar da rahotanni akai a makwannin baya musamman kan ƙungiyoyin biyu a Mali da Burkina Faso.
Wannan ya kuma kawo ƙarshen rahotannin da kafafen yaɗa labarai ke bayarwa kan abin da jami'an tsaro ke cewa game da hadin kan IS da JNIM wanda ke kara haifar da barazana a Sahel.

Za ku so ku karanta wasu karin labaran

Adawar Al-Qaeda da IS
Rikicin IS da JNIM shi ne na baya bayan nan a cikin shekaru na yaƙi tsakanin IS da al-Ƙaida.
Dalilan suna kama da juna: IS ta zargi al-Kaida da kaucewa ka'idojin jihadi, yayin da kuma al-Ƙa'ida ta ɗauki IS a matsayin mai tsatstsauran ra'ayi da zubar da jini wanda ya saɓa dokokin shari'a da kuma "ɓata sunan mujahidun"
Domin jaddada matsayinta kan al-Ƙaida, kwanan baya IS ta saki wani dogon bidiyo inda ta zayyana jerin dalilanta na bayyana al-Ƙaida da dukkanin rassanta, hadi da JNIM a matsayin "masu ridda." Ƙungiyar ta yi amfani da bidiyon domin yin kira ga mayaƙan al-Ƙaida su sauya sheƙa zuwa IS.
Ƙorafe-Ƙorafen na IS game da fuskantar munanan hare-harenn JNIM a Mali da Burkina Faso wata tunatarwa ce kan ikirarin da ta taba yi a watan Nuwamban 2018 kan hare-haren al-Shabab a Somalia. Wannan na zuwa bayan bangarorin biyu sun gwagza faɗa tare da yi wa juna barazana.
Rikicin a yankin Sahel na baya-bayan nan ya yi daidai da rikicin IS da al-Ƙaida reshen Yemen AQAP. Ƙungiyoyin biyu sun daɗe suna gwabza faɗa tun watan Yulin 2018.
A dukkanin ƙasashen Mali da Yemen, IS ta zargi abokiyar gabarta al-Ƙaida da haɗa baki da dakarun gwamnatoci da sauran mayaƙan da ke yaƙi da IS.
IS kuma tana yaƙi da Taliban a Afghanistan. IS ta yi amfani da tattaunawar sulhu da tsakanin Taliban da amurka da kuma yunƙurin JNIM na tattaunawa da gwamnatin Mali, a matsayin wani muhimmin abu na yaƙar ƙungiyoyin tare da fatan janyo hankalin mambobinsu.
Me zai faru?
Mayaƙa sun tsawwala hare-hare a ƙasashen Sahel tun bara, wanda ya tilasta haɗin guiwar kasashe da kafa rundunonin soji domin magance barazanar.
JNIM ta kasance ɗaya daga cikin reshen al-Ƙaida mafi haɗari, da ita da al-Shabab a Somalia.
Amma IS a Sahel - wadda ta kira kanta "Yankin Afirka ta Yamma" amma aka fi kira da IS a yankin Sahara - ta kafa kanta a ƙasashe Sahel.
Ƙungiyar ta ɗauki alhakin munanan hare-hare da sojojin Mali da Nijar da Burkina Faso da dama suka mutu.
Rikici tsakanin mayaƙan biyu zai iya dagula lamurransu da ƙarfinsu tare da karkatar da hankalinsu wajen kai wa dakarunn gwamnati da na kasashen waje hari.
Rahoton IS nuna hoton zanen faɗan da ta gwabza da JNIM, tare da cewa JNIM ta fi IS yawan mayaƙa.
Sannan faɗan zai ƙara rage martabar ƙungiyoyin na janyo ra'ayin sabbin mayaƙa a yankin. Zai yi wahala su iya janyo ra'ayin wasu kungiyoyin jihadi domin haɗa kai a yaƙ gwamnati da dakarun ƙasashen waje.
Wannan zai iya zama dalilin da ya sa IS da JNIM ba su fito sun yi bayani kan faɗan da suke ba sai yanzu.
Sashen BBC Monitoringna bayar da rahotanni da sharhi a Talabijin da rediyo da intanet a sassan duniya. Za ku iya bibiyar BBC Monitoring aTwitter daFacebook.












