Yadda matsalar ƙwaya ke tilasta wa Ghana tsaurara matakan tsaron iyakokinta

GHANIAN PRESIDENT

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin Ghana ta kara tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin ƙasarta, domin magance kwararar kwayoyin nan masu matukar hadari na tramol cikin kasar.

Hakan dai ya biyo bayan wani rahoto na musamman na binciken kwakwaf da BBC ta yi ne mai suna BBC Africa Eye, wanda ya bankado yadda ake safarar kwayar ta tramol daga kasar Indiya zuwa kasashen Afirka ta yamma, wadanda suka hada da Gahana da Najeriya.

Al'amarin da ya haifar da gagarumar matsala a bangaren kiwon lafiyar jama'a.

Ministan lafiya na kasar ta Ghana, Kwabena Mintah Akandoh ne ya bayar da sanarwar wannan mataki da gwamnatin kasar ta dauka, cewa an kafa wata rundunar hadin gwiwa, wadda ta kunshi hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar, da hukumar dakile yaduwar kwayoyi masu bugarwa, da hukumar kwastam, da hukumar tara kudaden shiga, wadda ta tsaurara matakan tsaro a hanyoyin shiga kasar, domin magance shigar kayan da ba a amince da su ba.

Bayanai sun ce, wannan mataki har ya fara haifar da kyakkyawan sakamako, wajen dakile shigar da tarin kwayar tramol da makamantanta cikin kasar.

Hukumomin Ghanar sun kuma karkanta cewa, sun kara matsa kaimi wajen sa ido, da daukar matakan hukunta duk wanda aka kama da aikata miyagun laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi.

Wasu ƴan majalisar dokokin kasar su ma sun bayyana takaici, game da illar da miyagun kwayoyin ke yi ga matasa a mazabunsu.

Ita ma ƙungiyar masu harhada magunguna ta kasar Ghanar ta yi Allah wadai da irin yadda ake ta samun yaduwar magunguna masu cutarwa, ta kuma yi kira da a hanzarta gudanar da bincike, game da zarge-zargen da aka yi wa kamfanonin harhada magunguna da aka ambata sunayensu a rahoton nan na bincike kwakwaf na BBC Africa Eye, wanda ya bibiyi wannan batu a baya. A kuma hukunta duk wani kamfani da aka samu da laifi.

Sakamakon tsaurara matakan tsaro game da safarar tramol da aka yi a kan iyakokin Najeriya, sai kasar Ghana ta zama wata sabuwar hanyar safarar kwayar, duk da matakan da kasar ta tanada a baya.