Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda kisan mata a Adamawa ke jan hankali a Najeriya
Ƙungiyar kare haƙƙin bil'Adama ta Amnesty Internaltional ta buƙaci a gudanar da bincike na gaskiya, domin hakkake abin da ya auku, dangane da zargin kisan mutum tara da raunata wasu da dama da aka yi, yayin da wasu mata suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a garin Lamurde na jihar Adamawa, ta Najeriya, ranar Litinin da ta gabata.
Wannan kira ya biyo bayan zargin da ake ta yi ne, cewa sojoji ne suka buɗe wuta kan matan da ke zanga-zangar lumanar, amma kuma hukumomin sojan na musanta zargi.
Yanzu dai, baya ga alhini da zaman makoki da ake yi, an shiga ja-in-ja, dangane da wanda ake zargin ya yi harbin bindiga da ya kashe matan, kuma ya raunata wasu da dama, yayin da suke gudanar da zanga-zangar.
A tattaunawarsa da BBC daraktan ƙungiyar ta kare hakkin bil'Adaman ta Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi ya ce tun daga lokacin da abin ya faru suke bin diddigi: ''Tun daga ranar Litinin da wannan abu ya faru, muna bin didddigin wannan lamari.
''Mun tura mutane wurin, sun yi magana da mutane da dama, dangi da suka rasa 'yan'uwansu, abin da suka tabbatar mana gabaɗayansu ba tare da saɓani ba, shi ne cewa wani soja ne ya buɗe wuta ya yi sanadiyyar wannan asarar rayuka da aka yi,'' in ji shi.
Dangane da yadda suka tabbatar da yadda lamarin ya faru, darektan ya yi wa BBC ƙarin bayani da ce: '' To muna da tsari na bincike. Kuma a irin tsarin da muke bincike ba ma dogara da sheda guda ɗaya. Mukan kai ga sheda 15 zuwa 2, kuma ba wai kawai ta mutane ba, muna magana da jami'an tsaro ma waɗanda suke waɗannan yankuna da kuma shugabannin al'umma da na addini duka.
''Sannan muna da hotuna da bidiyo da suke tabbatar mana da cewa an buɗe wuta a wannan wuri.''
Ya ce abin da suke so a yi shi ne a yi bincike na gaskiya a tabbatar da wanda ya aikata ta'asar.
''Mu abin da muke so a yi shi ne a yi bincike na gaskiya na adalci a tabbatar cewa an yi bincike wanda yake ya dace da ƙa'idojin duniya na yin bincike na gaskiya, domin idan ba a yi bincike ba, to duk wata magana da za a yi ko kuma jayayya a kan wa ya yi ko kuma bai yi ba, duka wnnan ba zai yi tasiri ba, sai an yi bincike na gaskiya.''
Su ma al'ummar da mutanen nasu suka rasa rayukansu a lokacin zanga-zangar suna so a gudanar da cikakken bincike.
A cewar Barista Danbaba Kpawemi Rigange, mai bayar da shawara ta fuskar shari'a ga al'ummar garin: '' Sojojin da ake zarginsu da aikin da suka yin nan na harbin matan nan da ba sa riƙe da makami, muna son a sauke su daga muƙaminsu kuma a yi musu bincike a yi musu shari'a bisa ga laifin da suka aikata.''
Ya ƙara da cewa, '' Kuma iyalin da aka yi musu rashin nan a biya musu diyya kuma waɗanda sun ji rauni a ɗauki matakin jinyarsu.''
Game da yawan waɗanda suka rasu, Barista Rigange, ya ce, da farko mutum tara ne suka rasu daga baya kuma wata yarinya mai shekara 13 ita ma ta rasu ranar Laraba hakan ya kawo yawan waɗanda suka mutu zuwa goma.
Sannan kuma ya ce akwai mutum 16 da aka jikkata waɗanda suke asibitin ƙwararru na Yola, sannan kuma kawi wasu 13 zuwa sama da suma suke jinya Numan.
Wakilin al'ummar ya ce abin da ya janyo lamarin shi ne, matan ne suke zanga-zanga kan tashin hankalin da ke faruwa a yankinsu, inda suke kira ga gwamnati domin ta ɗauki mataki a kan lamarin shi ne aka kai musu harin.
Ya ce ba wanda suke zargi da kai harin sai sojoji na Yola, domin a cewarsa suna da shedu a kan hakan, da kayan da suka samu da kuma hotuna na abin da ya faru.
Sai dai kuma a wani sako da rundunar sojan Najeriya ta wallafa a shafinta na X, ta musanta zargin da ake yi, cewa soja ne ya yi harbin da ya halaka masu zanga-zangar. Kuma sakon ya danganta aukuwar lamarin ga 'yan bindiga.