Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe mutane a rikicin kabilanci a Numan ta Adamawa
Bayanai na kara fitowa kan wani rikici mai nasaba da kabilanci da aka samu a yankin Numan na jihar Adamawa a jiya Litinin.
Mutane a kalla 20 ne hukumomin suka tabbatar sun mutu a cikin rikicin tsakanin kabilun Bacama da Fulani a kauyuka daban-daban na yankin.
Tuni dai wata tawagar gwamnati karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar ta ziyarci yankin.
Ga dai karin bayanin Imam Aminu Yakub, limamin masallacin Juma'a na daya da ke garin Numan ya yi wa Haruna Shehu Tangaza.
Latsa alamar lasifikar da ke kasa don jin bayanin:
To sai dai kwamishinan watsa labaran jihar Ahmed Sajo ya shaida wa Harunan cewa a hukumance mutane kimanin 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu.
Latsa alamar lasifikar da ke kasa don jin bayanin:
Rikicin kabilanci dai a baya-bayan yana dan faruwa a wasu sassan kasar.
Ko a watan Yunin shekarar nan ma an kashe mutane tare da lalata kadarori da dama a hare-haren da aka kai matsugunan Fulani a karamar hukumar Sardauna da ke jihar Taraba makwabciyar Adamwan.
Rundunar sojin Najeriyar ta bayyana kashe-kashen da aka yi wa Fulanin a wancan lokaci a matsayin kisan-kare-dangi.