Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nigeria: 'Yan bindiga sun harbe mutum 11 a Plateau
Wasu 'yan bindiga sun harbe mutum 11 kusa da Rim da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiya a Najeriya.
Wasu mazauna kauyen ya shaida wa BBC cewa mutanen suna dawowa ne daga kasuwar kauyen Makera lokacin da lamarin ya auku a ranar Talata da yamma.
Shaidun sun ce an yi wa mutanen kwanton bauna ne a lokacin da motarsu ke dawowa daga kasuwar kauyen.
Wasu mazauna yankin sun ce an ga maharan a cikin Kayan sarki irin na soja, to amma hukumomin na cewa bincike ne kawai zai tabbatar da hakikannin wadanda suka kai harin.
Kakakin rundunar 'yansanda a jihar ta Filato, DSP Mathias Ter Tyopev, ya shaide wa BBC cewa basu so su yi riga Malam masallaci ba domin tuni aka fara bincike.
Ya ce an kai wadanda suka jikkata asibiti.
Har yanzu dai babu wanda ya ta dauki alhakin kai harin.
Sai dai kuma hare-haren kabilanci da aka dade ba a samu ba a jihar sun fara dawowa Filato a baya-bayan nan.
Ko a watan jiya mutane fine da 30 suka rasa rayukansu a karamar hukumar Bassa lokacin da aka kai hare-hare a kauyukansu.
Bayan hare-haren sun fara dawowa ne gwamnatin Najeriya ta tura jiragen yaki yankin domin tallafa wa sojin kasa da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya a yankin.
A baya dai an sha fama da rikice-rikice a jihar ta Filato, al'amarin da ya yi sanadin rasa dumbin rayuka tare da raba mutane da dama da muhallansu.